Sunday, June 9, 2013



KUNGIYAR IZALA CE TA DAWO DA RUHIN ADDINI A ZUKATAN AL'UMMAR NAJERIYA (1)

Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa'Iqamatus Sunnah, kungiya ce da aka kafata domin kawar da dukkan bi'di'o'in da aka jinginawa addinin Musulunci tare da tabbatar da cikakkiyar koyarwa Addinin Musulunci a bisa tsarin koyarwar Al-Qur'ani da Hadisan Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam Ingatattu, da kuma fahimtar magabata na kwarai. Kungiyar Izala kungiya ce da ta kunshi hazikan Malamai wadan da suka karantu suka san Addinin Musulunci kamar Yadda Manzon Allah Ya zo da shi.

Kusan wannan kungiya mai albarka ta kafu ne karkashin Jagorancin marigayi Shiekh Abubakar Mahmoud Gumi (Rahimahullah). Sheikh Gumi yayi ta fadi tashin ganin an koyar da al'umma addinin Musulunci na hakika ba wai a Najeriya kadai a kusan daukacin kasashen yammacin Afurka. Cikin ikon Allah tare da taimakonsa ne Shiekh Gumi da'awarsa tayi nasara sosai, ya bayar da fatawoyin da suka fitar da al'ummar Musulmi daga duhun Jahilci da saita su akan hanya mikakkiya ta kitabu da Sunnah.

Sanin kowa ne cewar kafin bayyanar Izala, al'ummar Musulmi musamman na Arewacin Najeriya sun tasirantu da ayyukan addini da suka saba da hakikanin koyarwar Al'qur'ani da Hadisai Ingatattu. Wannan ce ta sanya dole kungiyar ta samu tirjiya daga mutanan da suka jima suna aikata Bidi'ah wanda suke zaton Addini suke yi. A karon farko anki yadda a fahimci hakikanin abinda IZALA ta zo da shi da gangan da ganganci, dan wadan da suka fahimci hakikanin abinda Izala ta zo da shi sun san cewa idan har al'ummar Musulmi suka fahimci koyarwar addini ta hakika karkashin Izala to la shakka kashinsu ya bushe kuma kasuwarsu ta kare, wannan ce ta sanya suka kasa zaune suka kasa tsaye wajen kira ga magoya bayansu kada su kuskura su saurari Malaman Izala, rahotanni sun nuna cewa wasu malaman sukan fadawa Mabiyansu cewa duk inda kaga Dan Izala yana wa'azi gwargwadon gudunka da shi gwargwadon ladan da zaka samu! Allahu akbar.

A gari irin kano wanda yake ciki da manyan Shehunnan dariqun sufaye kungiyar Izala ta fuskanci tirjiya mai girman gaske. A wasu lokuta ankai ruwa rana sosai tsakanin Malaman Izala masu wa'azi da al'ummar unguwanni da suke ganin babu dalilin da zai sanya a kyale su suyi wa'azi. Domin a lokacin anyi ta gayawa mutane karairayin cewa 'Yan Izala wasu mutane ne masu Gemu da dagaggen wando da suke Zagin Iyayan Manzon Allah (Wal'Iyazubillah). Wannan ta sanya Malaman Izala suka sha bakar wahala kafin samun damar fara yin wa'azi a cikin unguwannin Birnin Kano da kewaye.

Kasancewar KANO gari mafi yawan jama'a a fadin Arewa, kuma al'umma masu matukar kaunar duk wani abu da ya shafi addini, ya sanya Kano ta zama wani muhimman filin daga ga kungiyar Izala. Unguwanni irinsu Fagge Masallacin Triumph da irinsu Burged da jami'ar Bayero suna daga cikin guraran farko da suka fara cin gajiyar koyarwar Izala a jihar Kano. Amma unguwannain cikin birni an samu tirjiya mai girman gaske, takai jallin da an daddaki wasu Ustazai an sassari wasu da adduna an farfasa musu lasifikoki kai abin har ya kai da kona tare da yin kashi a cikin Masallaci a cikin birnin Kano. Masallacin 'Yan Rariya dake filin Mushe a Karamar Hukumar Gwale yana daga cikin masallatan Izala na farko farko a cikin birnin Kano, an shafe lokaci mai tsawo ana yin kashi da zuba shara a cikin masallacin, laifinsu kawai shine sunyi Sallar Azahar karfe daya na Rana!

Haka kuma, idan muka kalli Jami'ar Bayero kusan nanne inda Izala bata samu wata tirjiya ba wajen yin wa'azi. Wannan kuwa baya rasa nasaba da cewa Dalibai da malamai na Jami'ah suna da cikakkiyar wayewa ta fahimtar rayuwa da fahimtar inda duniya ta sanya a gaba, dan haka ne Masallacin Jami'ar ya zama wani dandalin Izala a cikin kwaryar birnin Kano. Masu magana sukance Duniya Labari, yanzu Izala har a tsakiyar Tudun Nufawa da Makwarari da Madabo da Kofar Wambai da sauran unguwanni na cikin birnin Kano.

Wannan ne dalilin da ya sanya wasu daga cikin Malaman da suke ganin Izala matsala ce a garesu idan har al'umma suka fahimce su suka fara saduda tare da zubawa sarautar Allah ido. Amma kuma dole wasu suka tashi haikan wajen bincike da Nazarin Ilimin addinin Musulunci, domin tsira da mutunci dan kada mutanan da sukewa kallon yara matasa su ringa kuresu tare da tsiraita iliminsu.

Bayan kafuwar Izala, ta assasa WA'AZIN KASA wanda ake hada kafatanin Malaman da suke Izala a wata jiha domin yin wa'azi tare da kira zuwa ga Al-Qur'ani da Sunnah. Wannan wa'azi da Izala take yi yayi tasiri kwarai da gaske wajen janyo hankulan mutane, tare kuma da sanya 'yan uwantaka ta addini a tsakanin Ustazai. Wani abin sha'awa shine a duk lokacin da Izala ta shiga wata Jiha domin yin wa'azi to shakka babu mutanan wajen da za'ayi wa'azin sukan samu habakar tattalin arziki, domin masu kankanan sana'o'i kanyi ciniki sosai na hajojinsu, a filin wa'azi wani Ustazu zai zo ya karkace ya kirawo Me Ganda ya saye daron gaba daya yace a yankawa jama'a suci su sha romo, wannan ko shakka babu ya kara karfin 'yan uwantaka ta addini a tsakanin Matasa. 

Yasir Ramadan Gwale 
09-06-2013

No comments:

Post a Comment