Saturday, June 22, 2013

BAYYANAR YAJUJU DA MAJUJU (Gog And Magog)


BAYYANAR YAJUJU DA MAJUJU (Gog And Magog)

A karshen duniya wasu al’ummu guda biyu zasu bayyana, zamanin Allah ya dawo da Annabi Isah Dan Maryam Alaihis Salam. Wadannan mutane (yajuju da Majuju) zasu bayyana ne bayan zuwa da tafiyar Dujjal. Allah madaukakin Sarki zai halakar da Yajuju da Majuju a cikin dare daya, bayan Annabi Isah (AS) ya roki ubangiji akansu.

Abu-Huraira Allah ya kara yarda a gareshi, ya ruwaito daga Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, yana cewa “A kowacce ranar Allah wasu al’umma (Yajuju da Majuju) suna nan suna hake wata Katanga, da zasu shigo cikin wannan duniya tamu, sai sun yi haka har sun gaji, sannan zasu fara hango harsken rana, abinda yake nuna hakarsu ta kusa cimma ruwa, sai kawai shugabansu, ya umarce su da su koma su kwanta gobe zasu dawo su cigaba! Cikin hukuncin Ubangiji washe gari suna zuwa, sai su tarar Allah ya shafe wannan Katanga ta kara karfi da kwari, sama da yadda suka sameta a jiya, haka zasu sake cigaba da tone ko kwarzane wannan Katanga, su sake komawa, washe gari su sake ganinta kamar basu taba haketa ba, hakan nan zasu yi ta yi, har sai lokacin da Allah ya hukunta fitowarsu. Idan sunyi aiki har sun bula katangar sun fara hango hasken rana, anan ne shugabansu zai umarce su da su koma su kwanta, gobe idan sun dawo zasu cigaba, amma zai ce INSHA ALLAH wato yayi togaciya kenan! Bisa fadin Insha Allahu da shugabansu ya yi sai Allah ya amsa, washe gari idan sun komo zasu sami wannan Katanga yadda suka barta jiya!

Bayan dawowarsu ne, washe gari, zasu ci gaba da yin aikinsu na kwakwule wannan Katanga. Kuma cikin nufin Allah, zasu shigo cikin wannan duniyar daga katangesu da Allah yayi da al’umma, idan suka fito zasu shanye dukkan wani ruwa da sukayi ido hudu dashi, sannan zasu cinye dukkan wani abinci da suka gani, kai kusan dukkan wani abu da suka gani sai sun cinye shi, kama daga Bishiya tsirrai da dabbobi, sannan zasu shiga kisan mutane babu ji babu gani! Hasbunallahu wani’imal wakeel.

A wannan lokacin Yajuju da Majuju zasu dinga harba kibau sararin samaniya. Suna harba kibiyoyi da masuna, sannan suna fadowa kasa suna masu digar da jini a jikinsu, anan ne Yajuju da Majuju zasu ce, mun gama da al’ummar da take a ban-kasa sannan kuma wadan da suke sama suma mun gama da su! A lokacin da suka yi wannan ikirari ne kuma, Allah zai yi musu ruwan wasu irin tsutsotsi wadan da zasu dinga makalemusu a wuya suna cizonsu, haka nan, wannan tsutsa zata hakalasu gabaki dayansu a cikin dare daya! Allah buwayi gagara Misali, tsarki ya tabbata a gareka Ya Allah! Bayanin wannan Hadisi na Abu-Huraira yazo cikin Tirmuzi karkashi Tafsirin suratul Kahfi (hadisi 5160), 8/597-99. Haka kuma, kitaab al-fitan, (hadisi 4080), 2/1364, da kuma musnad na Imam Ahmad, 2/510, 511.).

Yajuju da Majuju dai, tsatso ne, na ‘dan Annabi Nuhu Alaihis Salam. A zamanin Annabi Ibrahim akwai wani sarki da ake kira Zulkarnaini, shi wannan sarki, Allah ya bashi iko da kuma Mulki tundaga Bangon Gabas har zuwa yamma, kuma mutumin kirki ne da ya shimfida Adalci, shine ya gina wannan Katanga da ta raba wannan duniya tamu da Yajuju da Majuju. Haka kuma, wannan Katanga an gina tane da narkakken karfe da duwatsu da kwalta da ruwan dalma. A zamanin Zulkarnain wadannan al’umma (Yajuju da Majuju) sun addabi mutane, shine al’ummar da Zulkarnaini yake mulka suka rokeshi da ya gina musu katangar da zata rabasu da Yajuju da Majuju.

Yajuju da Majuju sunyi ta kokarin fasa ko bula wannan Katanga su fito amma kuma sun kasa. Sunyi dukkan irin dabarunsu su yi tsalle su fito amma Allah bai basu iko ba, shine tun daga wancan lokaci har kawo yau suna nan suna kwakwule wannan Katanga domin su samu su fito, amma Allah ba zai basu iko ba, sai a karshen duniya.

Haka kuma, idan muka kalli Hadisin da Ibni Mas’ud Allah ya kara yarda a gareshi ya ruwaito daga Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam yana cewa. A daren da Manzon Allah yayi Isra’I ya hadu da Babansa Annabi Ibrahim da Annabi Musa da kuma Annabi Isah, dukkansu sun tattauna akan shin yaushe ne Alkiyama zata tsaya, sun fara tambayar Annabi Ibrahim yace bai sani ba, daga nan Annabi Musa yace shima bai sani ba, daga nan sai Annabi Isah yace babu wanda ya san wannan ranar sai Ubangiji mamallakin ranar sakamako, Tsarki ya kara tabbata a gareshi! Annabi Isa ya cigaba da cewa, abinda Ubangijina ya gayamin shine a karshen duniya, Dajjal zai bayyana, haka kuma, idan ya hadu da ni zai dinga narkewa yana zagwanyewa, Haka nan Allah zai halakar da shi (Dajjal), sannan Musulmi zasu yaki kafurai, har sai takai matsayin da Idan kafiri ya buya a bayan wani dutse ko bishiya, zasu yi Magana su kirawo musulmi suce masa zo ga kafiri ka kashi shi. Allah buwayi gagara misali!

Daga nan kuma, adalci zai yadu a ban kasa tsakanin Musulmi, can kuma sai Allah ya fito da Yajuju da Majuju. Zasu barko cikin wannan duniya ta gabas da yamma kudu da Arewa, suna shanye ruwa, suna cinye dukkan wani abu da suka yi arba das hi. Lahaula Walakuwwata Illabillah! A lokacin ne al’umma zasu je ga Annabi Isah suna mai rokonsa da ya roki Ubangiji Allah ya kade musu wannan Masifa da Bala’I na Yajuju da Majuju. Sai Annabi Isah ya daga hannu ya roki Ubangiji, Allah mai girma da daukaka ya amsa, sannan ya dinga saukar musu da tsutsotsi daga sama, suna halakar da su, bayan sun mutu duniya gabaki daya zata cika da warin gawarwakinsu da jinanansu, daga nan kuma Sai Allah ya saukar da Ruwan Sama wanda zai wanke duniya gabaki daya ya wanke dukkan dattin gawarwakin Yajuju da Majuju. Annabin Allah Isah dan Maryan Alaihis Salam, ya cigaba da cewa, daga zarar Allah ya saukar da wannan ruwa, to babu wani abu da yake gab da zuwa face Alkiyama, misalin haka shine, kamar matar da ta ked a juna biyu kuma ta shiga watan haihuwarta, daga lokacin da watan ya kama a kowanne lokaci zata iya haihuwa, to irin haka ne misalin yadda Alkiyama zata tsaya a wannan lokaci. Ya Allah ka sa mu mutu muna masu Imani kuma mu tashi cikin masu Imani, Ya Allah ka karemu daga fitinar Dujjal. Wannan hadisi yana nan a cikin ( musnad na Imam Ahmad 1/375da  ibn majah, cikin littafin kitaab al-fitan (hadisi 4081), 2/1365, 1366)

Yasir Ramadan Gwale
22-06-2013

No comments:

Post a Comment