Saturday, June 22, 2013

TSAKANIN GWAMNA JANG DA KWANKWASO WAYE MAKIYIN AREWA?


TSAKANIN GWAMNA JANG DA KWANKWASO WAYE MAKIYIN AREWA?

Kusan a ‘yan makwannin nan babu wasu abubuwa da suka dauki hankalin Siyasar Najeriya kamar zaben Majalisar Gwamnonin day a gabata. Tun bayan zaben ne, majalisar gwamnonin ake ta cigaba da yamutsa hazo da tayar da kura, a tsakanin gwamnonin Najeriya akan wannan zabe. Kurar dai tafi turnikewa ne a jam’iyyar PDP wanda wannan zaben ake wa kallon zakaran gwajin dafi ne, da yake nuna waye zai iya zama dan takarar shugaban kasa a zaben 2015 da yake tafe a cikin jam’iyyar.

Tun bayan dawowar mulkin demokaradiyya a 1999, ba’a taba samun wani lokaci da aka samu hannun gwamnatin tarayya dumu-dumu a sha’anin majalisar gwamnoni ba, sai karkashin wannan gwamnati ta shugaba Jonathan. Majalisar gwamnonin Najeriya wani jigo ne babba wadda take taka muhimmiyar rawa wajan samar da dantakarar shugaban kasa, duk kuwa da cewa majalisar bata da wani gurbi a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Idan bamu manta ba, a watan mayun da ya gabata ne, wannan majalisa ta gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin shugabanta kuma gwamnan Ribas, Mista Rotimi Amaechi ta gudanar da zaben sabbin shugabannin majalisar, inda gwamna me ci Amaechi ya sake darewa kan wannan kujera, inda ya kayar da gwamnan Jihar Plateau Jonah Jang, wanda ake ganin kamar bisa sahalewar gwamnonin Arewa ya fito wannan takara. Sai dai bayanai na hakika sun nuna cewar gwamnan ya fito ne bisa goyon bayan gwamnonin da suke dasawa da fadar shugaban kasa, abin da yake nuni da cewa fadar shugaban kasa tana da hannu wajen fitowar gwamna Jang neman wannan kujera. Haka kuma, bayan da sakamako ya nunar da cewar Gwamnan Jang ya sha kaye, Shi (Jang) din yaki amincewa da Gwamna Amaechi a matsayin sabon shugaban majalisar, wannan ce ta sanya ficewar wasu daga cikin gwamnonin Arewa daga majalisar gwamnonin Arewa irinsu Gwamna Isa Yuguda na Bauchi da Gabriel Suswam na jihar Bunuwai.

Haka kuma, wannan ce ta sanya Gwamnan da ya sha kaye Jonah Jang ya ja tunga tare da gwamnoni 16 da suke mara masa baya a wannan zabe. Sai dai a lokacin da yake maida martini akan wannan dambarwa ta majalisar gwamnonin Najeriya Gwamnan Jihar Kano Engr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi wata ganawa ta musamman da ‘yan jaridu a Abuja a wannan makon me karewa, gwamnan ya soki lamirin Gwamna Isa Yuguda na Bauchi da Suswam na Bunuwai akan ficewarsu daga majalisar gwamnonin Arewa.

Gwamna kwankwaso yayi Karin haske akan yadda wannan zabe ya gudana, da kuma yadda suka ki marawa Gwamna Jang baya, inda ya sha kaye a hannun Gwamnan Ribas Mista Rotimi Amaechi. Sai dai kuma a shafin farko na Jaridar SUN ta juma’a 21 ga wannan watan na Mayu, 2013, an ruwaito kakakin gwamnatin Jihar Plateau Rabaran Yiljip Abraham yana zargin Gwamna Kwankwaso da cewa “makiyin Arewa ne”. Haka kuma, abinda manazarta zasu tambaya daga wannan bayani da ya fito daga fadar gwamnatin Jihar Plateau tsakanin gwamna Jang da Kwankwaso waye hakikanin Makiyin Arewa?

Sanin kowa ne cewar a tarihin Arewa ba’a taba samun wata jihar da ta zama makwarar jinin jama’ar da basu san haba basu san sauka ba, kamar Jihar Plateau musamman lokacin wannan gwamnan Jonah Jang. A kusan shekaru shida da Gwamna Jang ya shafe a matsayin Gwamnan Jihar Plateau anyiwa al’ummar Hausa Fulani Musulmi kisan kiyashi a wannan jiha babu dare babu rana, ankashe al’umma babu sididi babu sadada. A tarihin Najeriya ba’a taba samun wani tambadadden Gwamna wanda ya nunawa al’ummar Musulmi Hausa Fulani kiyayya muraratan irin Jang ba. Labarin kashe al’umma da lalata dukiyarsa shine babban labarin da yake fitowa daga Jihar Plateau a kullum ta Allah.

Ba’a taba samun wani lokaci a tarihin kasarnan ba ko a jihar Plateau da aka mayar da kisan jama’a wani abin Karin kumallo ba sai lokacin Jang. Wannan kisan kiyashi mun san cewar an fara shine tun zamanin Gwamna Joshua Chibi Dariye, kafin daga bisani tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya sa gwamnan ya shiga taitayinsa. A dan haka, wannan bayani da ya fito daga fadar gwamnatin Plateau akan Gwamna kwankwaso babu wani abu da za a iya kiransa face tabarmar kunya ce wadda ake rufe ta da hauka, Gwamna Jang ya kidime yana ta hauma hauma da shirme da shirirta shi yasa yake iya shegensa yadda yaga dama. Sanin kowa ne cewar, irin kisan kiyashin da Jang yayiwa al’ummar Musulmi a tsawon Mulkinsa ba’a taba samun ko kwatankwacinsa ba, a zamanin mulkin gwamna Kwankwaso tundaga 1999 har zuwa yau dinnan a jihar Kano.

Jihar Plateau da ake yiwa kirari da cibayar zaman lafiya, ta zama kamar “Mogadishu” a kasar somaliya. Gwamnan Jang ya maida jihar mallakin kabilar Berom ce kadai da sauran tsirarun kabilun da suke tare da Berom. Bazamu taba mancewa da Watan Nuwamban 2008 ba, lokacin da tashin hankali ya lakume rayukan al’ummar Hausa Fulani Musulmi a wannan jihar. Haka kuma, kowa yasan da cewar, Jihar Kano jiha ce da take a matsayin gida ga kusan dukkanin al’ummar Najeriya Musulmi da Kirista.

Idan da ace Gwamna Jang zai sanya a gudanar masa da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar Najeriya, cewa wane Gwamna ne wanda wanda al’umma suka fi tsana, to lashakka zai samu kashi dari bisa dari sun zabe shi a matsayin wani mugun gwamna marar Imani wanda ya mayar da kisan al’umma a matsayin wani aiki da aka turoshi yayi.

Yasir Ramadan Gwale
22-06-2013

No comments:

Post a Comment