Friday, June 21, 2013

LABARIN WATA MATA DA DANTA MAI CIKE DA BAN AL-AJABI

Wannan labari dai gaskiya ne, ya faru kamar shekaru goma da suka gabata. Jaridar Al-ahram ta kasar Sudan ta ruwaito shi. Wata rana wata mace da jaririnta ta je tashar mota zata hau mota dan yin balaguro. Matar rike da jaririnta a hannu ta samu mota saura mutum biyu ta cike, zuwanta ya sanya saura mutum guda ake jira, tana zuwa aka bata waje ta z...auna kafin ta shiga motar ta baiwa wani mutum jaririn nata ya rike idan ta zauna ta nutsu ya miko mata shi; mutumin yana mika mata jaririn sai kawai yaro ya tsandara kuka irin me firgitarwa dinnan, matar tayi ta rarrashi amma yaro yaki yin shiru, sai wani mutum daga bayan motar yace "malama ki fita waje ki rarrashe shi idan yayi shiru sai ki dawo" abu kamar wasa tana fita yaro yayi shiru, ganin haka sai ta koma cikin mota, tana zama yaro ya sake barkewa da kuka, ta sake fitowa yaro ya sake yin shiru. Sai da suka yi haka har sau hudu. Sai jama'a suka ce mata tayi hakuri tunda ga mutum biyu sun zo ta hau wata motar su zasu tafi, matar nan tana rokon su kyaleta zata rarrashi danta a haka, amma mutanan suka ce gaskiya bazasu tafi da ita yaro na kuka haka ba! Matar nan ta hakura ta hau wata motar abin mamaki tana zama da yaronta a hannu sai yaro yayi shiru yana dariyar kamar ba shine yake kuka a daya motar ba, bayan da mota ta cika aka fara tafiya can sun isa wani waje sai suka hangi wannan motar da matar ta shiga yaron ya dinga kuka, Motar tayi hatsari kuma duk mutanan da suke ciki sun mutu babu ko mutum daya da yake numfashi! Allahu akbar, ganin haka matar nan ta rungume yaronta tana kuka. Tana ta'ajibin abinda ya faru.

Yasir Ramadan Gwale
19-06-2013

No comments:

Post a Comment