Sunday, June 23, 2013

TY. DANJUMA YA CANCANCI SARAUTAR DA SARKIN ZAZZAU YA BASHI


TY. DANJUMA YA CANCANCI SARAUTAR DA SARKIN ZAZZAU YA BASHI

A karshen makon nan ne, aka yi bikin nadin sarautar da sarkin Zazzau (Sarkin Adon Sarakuna), Maimartaba Shehu Idris ya tabbatarwa da Gen. Yakubu T. Danjuma. Hakika wannan sarauta ta JARMAI ZAZZAU da aka baiwa Danjuma, duk da cewa bani da masaniyar amfaninta a masarautar zazzau, amma ko shakka babu Maimartaba Sarki ya bayar da wannan sarauta ga mutumin da ya dace. Lallai Arewa tana da zakakuran ‘ya ‘ya wadan da suka hidimta mata kuma suka sadaukar da rayuwarsu, dan ganin cigaban yankin Arewa, irin wadannan mutane ba laifi bane idan an saka musu da irin wadannan sarautu.

Malam Yakubu T. Danjuma, daya ne daga cikin zakakuran ‘yan Arewa na tun farko, wadan da duniya ta shaida aikinsu. Hakika mutum irin Danjuma idan ba’a yabeshi ba to shakka babu idan aka zageshi akan Arewa, an zalunce shi. Da yawan mutunan Arewa musamman matasa da suke da karancin sanin me ya faru a baya, kusan tun zamanin su marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, an basu gurbataccen tarihin waye Danjuma, domin nakan ji masu san su soki Danjuma, sukan ce shi din makiyin Musulunci ne da Musulmi. Wannan kusan ita ce maganar da take fitowa daga bakunan masu san sukar Danjuma ko kuma kushe shi.

A matsayinmu na Musulmi Allah ya riga ya fada mana cewa kafurai makiya ne ga Musulmi. Wannan kam abu ne “wadeh” wanda Al-Qur’ani ya tabbatar kuma dukkan Musulmi yayi Imani da haka. Amma kuma, Allah cikin nufinsa da kaddarawarsa ya hada Musulmi da wanda ba musulmi ba zama waje guda, dan haka ya zama dole dukkan bamgarori su san yadda zasu zauna da juna lafiya, “ladarara wala dirara” babu cuta babu cutarwa. Allah masani!

Danjuma kusan dukkan mutanan da ake kira dattijan Arewa, babu wani mutum sama da shi, idan banda sa’o’insa irinsu Malam Adamu Chiroma. Tun zamanin Marigayi Sardauna Danjuma ya nuna kwazo da kishin Arewa, ina zatan wannan shine dalilin da ya sanya Sardauna a wancan lokaci ya ja mutane irinsu Danjuma a jiki, dan ya nunawa al’ummar Arewa musamman Musulmi muhimmancoin tafiya da mutanan da suke ba Musulmi ba, wajen ciyar da yankin Arewa gaba. Idan za’a yi Magana ta gaskiya, kuma za’a yi adalci. Dole ne mutanan Arewa su yabawa Danjuma, domin shine kadai Mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa a lokacin da aka kashe Sardauna, duk masu ihu da karadin Arewa, da cika duniya da surutu, watakila lokacin da Danjuma yayi wannan kasadar wa rayuwarsa dan ankashe Sardauna su suna zanin goyo, ko basu ma zo duniyar ba. Basu san lokacin da Danjuma yayi wannan kasadar ba. Ance Danjuma Igwa ya dauka zai tunkari mutanan kudancin kasarnan akan kashe Sardauna da aka yi. Allah shine masani!

Haka kuma, duk da irin gurbataccen tarihin da ake baiwa ‘yan Arewa akan Danjuma, a cikin manyan sojojin da suka rike manyan mukamai da ‘yan siyasa da wahala ka samu wanda ya taimakawa talakawa da dukiyarsa irin Danjuma (Bance babu ba). Danjuma bai rike mukamin shugaban kasa ko mataimakinsa ba, amma ya rike mukamin munista, kuma daya ne daga cikin mutanan da Allah ya yiwa arziki a yankin Arewa, abinda mutane da yawa basu sani ba, Danjuma kusan gaba daya dukiyarsa Musulmi ‘yan Arewa sune suke alkinta masa. Na tabbata mutane suna sane da irinsu Alhaji Amadu Chanchangi na Kaduna, da irin taimakon da yayiwa al’umma da Musulunci, sanin kowa ne cewar Chanchangi babban na hannun dama ne ga Danjuma, wanda kusan dukiyar da Amadu yake tafiyarwa ta Danjuma ce gaba daya, shin idan da Danjuma makiyin Arewa ne zai yarda ya danka amanar dukiyarsa a hannun irinsu Amadu Chanchangi?

Watakila wasu su ce ai Danjuma ya taimakawa da kungiyar CAN da maqudan kudade. Anan sai nace Danjuma ya taimakawa abinda yayi Imani da shi ne da kuma addinin sa, a kuma wannan gaba ne zamu kalubalanci dukkan manyan da Najeriya tayi musu wando da Riga dalilin Arewa suka kudance suka yi arziki dare daya, su me suka yiwa talakawan Arewa? Kowa yasan da cewa mutanan da suka rike manyan mukamai irinsu IBB da Abacha da AbdusSalam masu arzikin gaske ne, amma tsakaninmu da Allah wace Gidauniya suka kafa domin taimakawa talakawa da dumbin dukiyar da suka samu? Bar ta batun taimako, shin Zakkar da Allah ya umarci dukkan Musulmi su bayar suna bayarwa kuwa? Bari mu buga misalin irin dumbin arzikin da mutanan nan suka mallaka. IBB shine shugaban kasar Najeriya na soja, yayi tasarrufi da riyojin man kasarnan yadda yaga dama, a wannan lokacin ne ya baiwa Danjuma, kyautar rijiyar Manfetur ladan ganin ido. Kaji masu abin!

Wannan rijiyar manfetur da aka baiwa Danjuma kyauta ne, bayan ya kwashe tsawon lokaci yana amfanarta, sannan ya sayarwa da wani kamfanin kasar Koriya da wannan rijiya akan kudi Naira Biliyan Dubu, tashin hankali! Wadannan kudade da Danjuma ya samu, ya kafa Gidauniyar TY Danjuma, inda ya ware mata Naira Biliyan 15 domin kawai a taimakawa talakawa da marasa galihu da masu karamin karfi. Wannan kadan ne daga cikin misalin irin yadda Danjuma yayi tasarrufi da dukiyarsa.

Mukoma kan IBB, tunda shine muntahar, dan Allah mai karatu a tunanika IBB rijiya nawa zai baiwa kansa da iyalansa? Nawa kake zatan ya mallaka? Idan har mutum irin Danjuma an bashi rijiya daya ladan ganin Ido ya sayar da ita Naira Biliyan Dubu? Ba wannan ba ma, a lokacin IBB ne fa gwamnatin Najeriya karkashin jagorancinsa, zata tono danyan manfetur ta sayarwa da Matatun manfetur na IBB da yake dasu a Kwadebuwa da Benin sannan ya tace, ya dawo da tataccen ya sayarwa da gwamnati. Tirkashi, kaji mutum da kasar ubansa!

Kamar yadda bayanai suka nunar cewar Danjuma ya taimakawa da CAN da kudade a cikin waccan Biliyan Dubun dan gudanar da ayyukanta. Dan Allah kungiyar IZALA da IBB yake jingina kansa gareta Biliyan Nawa ya taba bata domin ayyukanta? Ko kuma kungiyar Jama’atu Nasrul Islam JNI nawa ya taba basu? Wace irin gidauniya IBB ya kafa dan taimakon Musulmi da Talakawa da ya fito daga cikinsu? Wannan IBB kenan fa kadai, ina ga irin dukiyar su Abacha da AbdusSalami da Aliyu Gusau da sauran manyan sojoji da suka kwashi dukiyar Najeriya kamar ta ubansu? Amma saboda san KAI da rashin fahimtar yadda gaskiyar lamura suke, sai mu kyale su IBB suna watayawarsu da dukiyarmu da suka sace, muna zagin su Danjuma. Allah ya kyauta!

Yasir Ramadan Gwale
23-06-2013

No comments:

Post a Comment