Thursday, February 20, 2014

Sanusi Lamido Sanusi: Abinda Ka Shuka Shi Zaka Girba!

SANUSI LAMIDO SANUSI: ABINDA KA SHUKA SHI ZAKA GIRBA!

Kamar yadda Malam Sanusi Lamido Sanusi ya fada, wannan dakatarwa da aka yi masa bata zo masa da wani mamaki ba ko bazata. Haka kuma, da daman 'yan Najeriya wannan dakatarwa bata zo mana da mamaki ba, domin kamar yadda Malam SLS ya fada, duk wanda ya yi irin abinda ya yi, to, ba shakka, sai wani abu ya biyo bayan haka. Kamar yadda gidan talabijin na Aljazeera ya fada cewa, Malam Sanusi ya yi bankadar abin kunya mai muni a cikin wannan gwamnati ta Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Wanda a bayyane take cewa hankalin Gwamnati bai kwanta ba tunda Malam SLS ya kwarmata badakar bacewar Dala Biliyan 20.

Ko shakka babu, muna alfahari da aikin da Malam Sanusi ya yi a Babban Bankin kasa, ya shuka alhairai masu yawa, kuma zai girbi alheri a nan gaba In Sha Allah. Ya tsaftace tare da inganta harkar Banki a Najeriya, ya sanya nutsuwa a zukatan masu ajiya a cikin bankuna. Abu mafi muhimmanci da ba zamu manta da shi ba, shi ne yadda ya tsaya kai da fata wajen samar mana da Banki Musulunci wanda baya ta'amuli da Riba, wannan kadai ya isa ya sanya mu cira masa tuta.

Muna masa fatan alheri a rayuwarsa, Allah ya musanya masa da aiki na gari wanda zai hidimtawa al'ummar Najeriya. 

YASIR RAMADAN GWALE 
20-02-2014

No comments:

Post a Comment