Monday, February 17, 2014

Boko Haram

BOKO HARAM: Da farko, ina farawa da Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Labaran da muke ji na irin abin tashin hankalin da yake faruwa a kasar Ifriqiyyal-Wusd'a ko Afurka Ta Tsakiya, kusan shi ne babban abin da yake tayar mana da hankali, irin yadda muke ji, muke ganin irin halin da Musulmi suka shiga a hannun kiristocin kasar, inda ake kashe babba da yaro mace da namiji aci namansu danye, bayan an kone gidajensu, tare da wawashe kayansu a kan idanun mutanan da ake ce musu jami'an tsaron kiyaye zaman lafiya, ba tare da sun daga ko kara ba! Ni dai har ga Allah ban san laifin me wadannan Musulmi suka yi a wannan kasar ba, da ake yi musu irin wannan ta'addanci duniya tana kallo babu wanda ya hana. 

Wannan al'amari kusan shi ya ke tayarwa da duk wani mai Imani hankali a ko ina yake. Ba shakka, wadan da ake kashewa tare da azabtar da su ake sace kayansu, Ubangijinsu yana nan gaba garesu, kuma duk rokon da suka yi da wanda aka yi musu, yaji, watakila yana son daukaka darajarsu ne a ranar gobe kiyama ne shi ya sanya mutuwarsu ta wannan hanyar. Allah shi ne masanin gaibu!

Tare da wancan bakin labarin da yake faruwa a Afurka Ta Tsakaiya muke kwana muke tashi, ashe bamu sani ba, ga wata Afurka ta tsakiya a kusa da mu. Kamar yadda 'yan Anti-Balaka ke kashe Musulmi son ransu a Afurka Ta Tsakiya, muma nan ga wasu 'yan ta'adda miyagu Azzalumai  da ake kira Boko Haram suna kashe mutane babu ji babu gani. Hakika, alkaluman da na gani na adadin mutanan da wadannan Azzalaumai suka kashe a Fabrairun nan, abin ya munana, ya kazanta, yakai duk inda ya kai abin tayar da hankali ne. Wannan duk yana zuwa ne bayan irin daruruwan mutanan da aka dinga kashewa a baya a  Ben-Sheikh da sauran yankunan kan iyakar Borno da Yobe da kuma daidaiku da ake kashewa nan da can.

Wadannan azzaluman mutanan, masu jin kishirwar jinin Musulmi 'yan ina da kisa su aka ce wai a kwanakin baya ana tattauna yadda za'a yi musu ahuwa, kuma a basu makudan kudade su tafi abinsu, sun kashe banza. Su kuma wadan da aka kashe sai dai idan an hadu a Lahira su nemi hakkin jininsu da aka zubar ba dan sun cancanci hakan ba, zasu nemi kadin abinsu kamar yadda Allah ya fada a cikin Alqur'ani.

Lallai lokaci yayi, kuma dukkan wata tura ta riga ta gama kaiwa bango, dangane da wannan tashin hankali. Amfanin shugabanci shi ne hidmtawa al'umma da kare musu rayukansu da dukiyoyinsu da mutuncinsu da hankulansu, kamar yadda Larabawa suke cewa "Sayyidul Qaumu Hadumuhum" Idan duk za'a dinga yi mana irin wannan aikin ta'addanci, shugabannin da muka aminta su ne ke da hakkin jagorantarmu suna ji suna kallo ana karar da adadinmu ina amfaninsu yake a garemu? Wace irin rana zasu yi mana alhali muna raye? Ko sai bayan mun mutu baga daya? Ya zama tilas hukumomi su farauto wadannan miyagun mutane duk inda suke a kamosu a hukuntasu gwargwadon abinda suka aikata.

Wannan al'amarin kullum kara daure mana kai yake yi, ace har yanzu an gaza gano maboyar wadannan mutane, an gaza sanin su waye, kuma makamansu sun ki karewa. Shin aljanu ne ko Mala'uku Subhanallah! Wannan magana ce da zamu dawo daga rakiyarta, a yi mana bayanin gaskiya dangane da wannan lamari, shin su waye ke aikata wannan kisan rashin Imani da rashin tausayi? Na yi imani cewar a cikin Musulunci  babu inda aka yi umarni da kisan rashin Imani na mutanan da basu jiba basu gani ba. Duk wani wanda yake wannan ta'addancin da tunanin samun rahama ba shakka yana kara tonawa kansa wawakeken ramin azabar Allah ne.

Da can muna jin wannan al'amarin yana faruwa ne tsakanin su wadannan miyagun 'yan Ta'adda da jami'an tsaro masu damara. Amma yanzu kwata-kwata lamarin ya sauya daga yadda muka sanshi, an koma kashe talakawa har cikin gidajensu da kame matayensu! Wal'iyadhubillah.

Shakka babu, Allah da muke kira a kullum ya yi mana maganin wannan al'amari ba kurma bane, yana ji, yana gani, kuma wadan da ake kashewa bayinsa ne. Mu Musulmi munyi Imani Azabar Allah gaskiya ce, Allah bai yi wata halitta da zata iya jure tsananin azabarsa ba, babu kuma wanda ya taba kubucewa mutuwa Fir'auna ya mutu, Sharon ya mutu da sauran dukkan wadan da suka yi duk abinda suka yi na rashin mutunci da ta'addanci sun mutu kuma zasu riski Alkawarin Allah gaskiya ne, sunyi Imani ko basu yi ba.

Muna kara jan hankalin hukumominu akan lallai su sani wajibinsu ne kare mana rayukanmu da dukiyoyinmu, wallahi dole su zama ababen tuhuma a ranar gobe kiyama akan duk wanda ya rasa ransa ba tare da hakki ba. Za su yi nadama a lokacin da ba zata amfanesu ba. Dole ne a tashi haikan dan kawo aminci a dukkan garuruwan wannan kasar, babu wani dalili da zai sanya ace wani bangare na kasarnan yana zaune lafiya, amma wani yana cikin masifa da tashin hankali amma an kasa yin maganin abin.

Ya 'yan uwa, wata mashahuriyar kissa da muka sani ta wani Dattijo matafiyi, gajiyayye, mayunwaci, mabukaci a cikin halin tafiya, yana tsananin neman taimakon Ubangijinsa daga dukkan dangin abin bukata, ya daga hannu yana cewa Ya-Rab! Ya-Rab! Ya-Rab, amma ya kasance Abincisa Haram ne, abin shansa Haram ne, Tufafinsa Haram ne . . . Yana daga cikin Sharuddan amsa ko wacce irin addu'ah, sai idan ya kasance wanda yake rokon Ubangiji maji rokon bayinsa, ya tsarkake kansa daga cin Haram, da Shan Haram, da Tufafin Haram! Ya yan uwa masu girma, lallai ya zama wajibi a garemu mu tsarkake kawukanmu daga Haram, mu kuma tambayi kawukanmu Anya kuwa bama cin Haram? Kar mu wayi gari mun tsinci kanmu a cikin hali na gaba kura baya siyaki, mun samu kanmu a irin halin kissar wancan dattijo, muna tsananin bukatar agajin Ubangijinmu, amma mun cika cikkunanmu da haram, mun tufatar da kawukanmu da Haram, mun sha mun shayar da haram! Allah ya karemu.

Ya Allah mun tuba ka yafe mana, Ya Allah kajikan yara da mata da tsofaffi; Ya Allah ka kawo mana dauki ta inda bamu zata ba, Ya Allah ka bamu aminci a garuruwanmu. Allah ka kawo mana karshen wannan masifa da bala'i da 'yan uwanmu suke ciki a Borno da Yobe da Afurka ta Tsakiya da Suriya da Iraki da Palastine dukkan inda Musulmi suke. Ya Allah ka shiryi shugabanninmu.

YASIR RAMADAN GWALE 
17-02-2014

No comments:

Post a Comment