Thursday, February 13, 2014

GENERAL MURTALA MOHAMMED: Najeriya Ta Yi rashin Shugaba


GENERAL MURTALA MUHAMMAD: NAJERIYA TA YI RASHIN SHUGABA

Yau Laraba 13 ga watan fabrairu, tayi dai dai da ranar da marigayi General Murtala Ramat Muhammad ya cika shekaru 38 da rasuwa, kwatankwacin Shekarunsa na rayuwar duniya, Ya rayuwa a duniya Shekaru 38, yanzu ya shafe tsawon wadannan shekaru kwance a Kabarinsa, a irin wannan ranace akayiwa wannan dan tahaliki kisan gilla, awani yunkuri na juyin mulki wanda baici nasaraba. Da ace Gen. Murtala yana raye har wannan shekarar, da ya cika shekaru 76 a wannan duniyar, an haifeshi a shekarar 1938 a tsakiyar birnin kano, Gen. Murtala ya rasu yana matashi domin bai cika shekaru 40 a duniya ba, an kasheshi a lokacin da yake da shekaru 38 da haihuwa, ya rasu yana begen ganin wannan kasar ta sami ingataccen shugabanci, da cigaba mai dorewa, sai dai har yanzu wannan buri da ya rayu kuma ya rasu tare da shi bai cika ba.

Zaiyi kyau a ce gwamnati ta sauya darussan Social Studies domin karantar da yara manyan gobe irin gudunmawa da nagartar mutane irinsu Gen. Murtala Muhammad. Hakika gwarzo ne abin koyi da tarihin kasarnan bazai cika ba idan babu tarihin irin gudunmawar da ya baiwa cigaba da wanzuwar wannan kasa da kuma wannan nahiya tamu ta Afrika, abin kaico, shi ne yara da dama kawai suna ganin hotonsa ne ajikin takardar kudi ta Naira 20 ba tare da sun san hakikanin waye shi ba. Ka kamanta dukkan wani shugaba mai kishin al’umma da son cigabansu da kaunar kasarsa da irin so da kaunar da wannan dan tahaliki ya nunawa wannan kasa, shin ko Asibitin Murtala dake birnin kano da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da titunan Murtala Muhammad dake galibin jihohin kasarnan sun isa su biya abinda wannan bawan Allah ya yi wa kasarnan a kwanaki 199?

Gen. Murtala kusan ya shafe kwanaki 199 a kan kujerar shugabancin kasar nan a matsayin Head of state, ya hau mulki daga 29 ga watan yuli 1975, zuwa 13 ga watan fabrairun 1976. Murtala shi ne mutum na biyar a jerin shugabannin kasar nan goma sha biyar, a iya tsawon kwanakin da ya shafe yana shugabanci bai kama ko kadangare ya daureba da sunan tuhumarsa da cin amanar kasa, kusan tarihi ya nuna cewa shi ne shugaban da bai taba daure kowaba a mulkin wannan kasar, haka kuma shi ne mutumin da ya fara assasa cewa mulki zai koma hannun farar hula, wanda mataimakinsa da ya dora daga inda ya tsaya Gen. Olushegun Obasanjo ya cika wannan alkawari a shekarar 1977, inda Shehu Aliyu Usman Shagari ya zama zababben shugaban kasa, haka kuma, shi ne ya kirkiro jihohi da dama da kuma inganta al’amarin kananan hukumomi, haka nan kuma shi ne mutumin da ya kafa harsashin maida cibiyar mulki daga Legas zuwa tsakiyar Najeriya inda ake kira Abuja, yanzu mutumin da ya yi wadan nan muhimman ayyukan ya dace tarihi ya mance da shi? Ko shakka babu amsar zata zama a’a, don haka ya zama dole gwamnati ta yi wani tsari domin koyar da yara halayyar mutanan kirki irinsa.

Ance kusan shi ne mutumin da ya fara daidaitawa ma’aikatan gwamnati sahu musamman ta wajen zuwa aiki akan lokaci da hukunta dukkan wanda ya karya doka. A wani littafi da fitaccen marubucin nan Mista Chinua Achebe ya rubuta mai suna The Trouble with Nigeria, ya yi bayanin kwanakin Murtala na farko-farko a mulkin wannan kasa, yace ko wane ma’aikaci na dari-dari da aikinsa da kuma tsoron karya doka musamman a birnin Legas inda nanne fadar gwamnati a wancan lokaci ta ke. Yace sau da yawa Gen. Murtala ya kanyi bazata ya fito kan titi da safe ya tsallaka ba tare da danja ta bashi hannun ba domin ganin matakin da ‘yan sanda zasu dauka, ance wata rana ya tuka mota danja ta tsaidashi amma ya wuce abinsa, da yalo fifa ya kamashi yace sai sunje caji ofis, ya nemi ya bashi dan na goro amma dansandan nan yace atafau, domin laifine akama ka kuma ka bada kudi domin fansa, suna zuwa ofishin ‘yan sanda kawai sai ya ware nadin da ke fuskarsa nan da nan DPO ya gane shugaban kasa ne inda ta ke ya sara masa, yalo fifa kuma yace kafa me naci ban baki ba domin yana tunanin ya gamu da gamonsa. Haka dai Achabe ya cigaba da bayyana Gen. Murtala wajen nuna kwazonsa da jajircewarsa, akan wannan kasa.

Gen. Murtala wadan da suka sanshi, sunce mutumne mai kwarjini da babu alamun wasa a tattare da shi, ance da zarar ya kalleka da ido idan baka da gaskiya sai kaga mutum ya hau tsuma yana kyarma, haka kuma Murtala mutumne da yake son yin abu da gaggawa ba tare da bata lokaci ko jin kiri ba, don haka ne akoda yaushe yake yawan maimaita kalmar "DA GAGGAWA" , Allahu akbar irin mutanan da Arewa ta fitar a wancan loakcin kenan, Bahaushe mutumin kano a birnin ikko ikon Allah. Ance lokacin da yake Head of state gidansa da yake aciki a lokacin da yake rike da mukamin Director of army signal corps kafin zamansa shugaba bai fita daga ciki ba domin haka kullum yake fita daga shi sai direba zuwa Dodan Barrack a Legas, shi mutumne da bai cika son wasa ba, don haka ko jerin gwanon motoci baya yi, haka kuma, baya kunna jiniya a lokacin da yake fita ko dawowa, shi kadai, daga shi sai direbansa suke zuwa kano tun daga Legas a motarsa ba ta gwamnati ba, tafiyar sama da kilomita dubu 1000.

Wani marubuci, Aliyu Ammani ya bayyana Murtala a zaman wani gwarzo a lokacinsa wanda aiki kawai ya sanya a gaba, mutum mai saukin kai kuma maras girman kai. Yace wani tsohon Lauya kuma tsohon malamin jama’ar Legas mai suna Dr. Obarogie Ohanbamu ya rubuta a Mujallarsa mai suna African Spark cewa Gen. Murtala ya azurta kansa kafin ya zama shugaban kasa da mallakar dimbin dukiya da gidaje, amma duk da haka Gen. Murtala baiyi amfani da ikon da yake da shi ba wajen ci masa mutunci ko sanyawa a kameshi tare da gana masa gwale-gwale kamar yadda aka san sojoji da yi a Najeriya, kawai sai ya kai shi kara zuwa Igbosere magistrate Court a Legas domin ayi musa shari’a da mutumin da ya bata masa suna a cikin jarida, ance kotu ta zauna ta saurari wannan kara, kuma ta dage zaman zuwa 17 ga watan maris 1976, Allah mai yadda yaso Gen. Murtala bai riski wannan lokacin ba Allah ya cika masa ajalinsa, sai dai a wata hira da abokin Gen. Murtala na kusa ya yi da jaridar The Punch ta ranar 4 ga watan mayu 1982, marigayi Cif MKO Abiola ya ce Gen. Murtala ya rasu ya bar Naira bakwai da kwabo ashirn da biyu(N7.22) a cikin asusunsa na ajiya, tabdi jan! kaji fa shugaban kasa kenan! Allahu Akbar! Haka kuma ya bar duniya bashida gida ko katuwar gona ko gandun daji da gandun dabbobi.

Ammani, ya cigaba da cewa a ranar 11 ga watan Janairun 1976, Gen. Murtala ya kada hantar kasashen yamma da wata kasida da ya gabatar a taron kasashen Afrika na OAU da akayi a birnin Adis Ababa na kasar Eithiopia akan ‘yancin kasar Angola mai taken Africa has come of age. Gen. Murtala ya yi jawabi kamar haka, ya ce “ ya mai girma shugaba, idan ina tuna irin yadda fararen fata suka bautar tare da nuna wariya ga bakaken fata a kasar Afurka ta kudu, zuciyata tana tafarfasa tana kara bugawa ne, wannan al’amari yana dugunzuma tunani na matuka kamar yadda dukkan wani mai kishi yake jin ciwo idan ya tuna wani abu irin wannan” haka Gen. Murtala ya ci gaba da jawabi yana cewa “ yanzu fa kasar Afurka ta kawo karfi, babu wata kasa da zata cigaba da bamu umarni muna bi, kowacece kuma duk karfinta, dole mu hada karfi da karfe wajen yakar wannan cin-kashi da aikin bauta a cikin 'yanci da akeyi mana domin kwatowa ‘yan uwanmu ‘yanci ko da kuwa hakan zai kai ga salwantar rayuwarmu” Allahu akbar haka ikon Allah yake Gen. Murtala yana wannan jawabi ne a lokacin da tuni Allah ya rubuta cewa kwanaki 34 ne kacal suka rage masa a duniya, haka dai ya cigaba da jawabi mai cike da armashi da kwarin guiwa da nuna rashin tsoro ko gazawa.

Haka Gen. Murtala yake da karfin hali da rashin nuna tsoro ga kuma kwarjini. Kamar yadda marigayi Sunday Awoniyi yace shi mutumne da ko da yake a makaranta a Barewa College Zariya baya fada da sa’anninsa sau da dama zaka samu yana fada da na gaba da shi akan anzalinci na kasa. Kamar yadda masana sukayi bayani ana son shugaba jarumi mai kwarjini maras tsoro da kuma karfin hali, hakika Gen. Murtala ya cika dukkan wadannan abubuwa da suka sanya zai iya zama kowane irin shugaba.

Haka dai mutanan kirki suke cigaba da gushewa a wannan rayuwa, a dai-dai lokacin da ake bukatar juriyarsu da jajircewarsu. Hakika Najeriya ta yi rashin gwarzo abin koyi, daya tamkar da dubu, muna addu’ar Allah ya jikan Gen. Murtala ya kai rahama kabarinsa ya sanya mutuwa ta zamo hutu a gareshi, Ya Allah ka arzurta wannan al’umma da mutane masu karfin hali da kwazo irin nasa koma wadan da suka fishi. Allah ya jikan General Murtala Ramat Muhammad . . . Yallabai kamar yadda ka nuna kishi da kauna garemu da kuma kasarmu muma muna yimaka addu’ar fatan alheri, duk da nasan bakajina a halin yanzu, amma inada yakinin insha Allah addu’ata zata riskeka. Allah ya hadamu a darussalam da alheri. Bahaushe yana cewa kada Allah ya kawo ranar yabo! Amma nikam ina fatar Allah ya cigaba da nunamin ranar da zan yabi mutanan kwarai irinka. 

Yasir Ramadan Gwale 
13-02-2014

No comments:

Post a Comment