Sunday, February 16, 2014

Abdul-Aziz Umar Fadar Bege

FADAR BEGE: Lokacin da naga jama'a na ta yin rubutu akan wannan bawan Allah da ya rasu, na yi ta karanta irin abinda aka dinga rubutawa akansa. Na kuma karanta irin baitocin wakarsa da su Yakubu Musa suka dinga sakawa. Na samu kalubale da yawa akan wannan mutumin, domin da dama sun aiko min da sako wai Yasir me yasa kowa yana yin rubutun fadin albarkacin bakinsa tare da yiwa Fadar Bege addu'ah amma kai baka yi ba, irin wannan sakon na same shi da yawa, wasu ma har akan Timeline dina suka dinga rubutawa, amma bana yin martani ga duk wanda ya turomin, illa nakan garzaya turakarsa dan fahimtar ko waye shi.

Wani abu da ya bani mamaki shi ne, yadda Abubakar Attahiru ya yi rubutu yake tambayar waye Fadar Bege dan shi bai sanshi ba, kuma bai taba jin wakarsa ba. Naga yadda mutane suka dinga karyata shi, wasu ma har da zagi wai kawai dan bai taba jin wakarsa ba. Nima irin ta Attahiru din, Ban san wannan bawan Allah ba, ban kuma taba jin wakarsa ba, sai da naga ana maganar rasuwarsa. Kuma dan mutane basu sanshi ko taba jin wakarsa ba, ai wannan ba shi ne zai rage darajarsa ba.

A kwanakin baya kuma naga ana ta yada wani zance a nan Facebook cewa WAI Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya gamu da gamonsa saboda ya yi wata magana akan Fadar Bege, aka yi ta yada karairayi akansa, har naji Shekhin Malamin da bakinsa ya sanya lada akan duk wanda ya fada masa inda ya yi maganar da aka ce yayi akan Fadar Bege. Ban sani ba ko an kawo masa kasset din da ya nema.

Abin da na ke so na kai gareshi shi ne, shin wa ye wannan Fadar Bage da har ake cewa wani Malami ya gamu da gamonsa saboda WAI ya zage shi. Shin ya matsayinsa yake idan aka kwatanta shi da Sayyadina Abubakar da Umar da Usman da Matan Manzon Allah iyayan Muminai da 'Yan Shi'ah suka cika duniya da zaginsu? Fadar Bege dai tasa ta kare, kuma nasan dai ba Dan Shi'ah bane, dan haka ina yi masa addu'ar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya yafe masa kurakuransa. Muma Allah ya jikanmu ya kyauta karshenmu.

Yasir Ramadan Gwale
16-02-2014

No comments:

Post a Comment