Wednesday, January 7, 2015

ZABEN 2015:Babu Sauran Ci-Da-Buguzum


ZABEN 2015 BABU SAURAN CI-DA-BUGUZUM

An dade ana magana akan irin yadda wasu 'yan siyasa ke fakewa da farin jinin wasu mutane dan samun nasarar zabe, kuma su kasa tabuka wani abin kirki bayan sunci zabe, sai dai ga dukkan alamu wannan ci-da-buguzum yazo karshe a wannan zaben. Domin kuwa Idan muka duba batun kaddamar da takarar da GMB yayi a Jihar Ribas, ya isa ya zama ishara ga duk masu jiran ci-a-bagas cewa wannan lokacin na kowa tasa ta fishsheshi ne, dan kuwa shi, GMB ya gabatar da kansa gaban dumbin jama'ar da suka taru ya gaya musu sunansa Muhammadu Buhari yana neman takarar Shugaban kasa, kuma yana rokon su zabe shi, dan kawo sauye-sauye a harkar tafiyar da Gwamnati a najeriya. 

Abinda hakan ya nuna a wannan karon, shi ne cewar Siyasar GMB ta sauya, domin kuwa a Ribas GMB bai daga hannun kowa ba, abinda yake nuna sai dai kowa tasa ta fishsheshi, dan haka wannan babban albishir ne GMB ya yiwa masu jiran ci-a-bagas cewa babu hannun wanda zai daga dan ya rabu da shi yaci zabe, dole kowa tasa ta fishsheshi, wadan da suka kwanta a gida suna jiran GMB yazo jihohinsu ya daga hannunsu dan ci-da-buguzum wannan lokacin ya wuce.

Ina kuma jinjinawa GMB akan wannan mataki da ya dauka, ba shakka wannan abin yabawa ne, kuma wani cigabane a Demokaradiyya. Babu sauran shiga rigar Buhari a ci zabe, mun san GMB na kowa ne, yana da mutane a ko wace Jam'iyya.

Yasir Ramadan Gwale
07-01-2015

No comments:

Post a Comment