Saturday, January 10, 2015

Abinda Sheikh Gumi Ya Tsoratar Da Faruwarsa


ABINDA SHEIKH GUMI YA TSORATAR DA FARUWARSA

Allah ya sakawa Sheikh Dr. Ahmed Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da alheri, kusan wannan shi ne abinda yayi nuni da faruwarsa a siyasar 2015, dan kaucewa fadawa wannan yanayi SHEIKH GUMI yayi kira ga GEJ da GMB da su hakura da tsayawa wannan zabe, abinda aka kasa fahimtar Malam Gumi. Bankawa motocin shugaban kasa a Jos wuta wannan Sam ba dai dai bane, haka kuma na kara tabbatar da zargin da ake mana na tada hankali.

Alhamdulillah, na ji dadin da Buhari da kansa yayi Allah-wadai da wannan aikin 'yan ta'adda wadanda basarwa nufi Najeriya alheri, ya kuma nesanta kansa da duk wanda yake zaton yayi haka dan nuna goyon baya gareshi, wannan shi ne dattaku abinda GMB yayi. Yana da kyau musani duk abinda bamu tsaya mun sameshi cikin sauki ba tashin hankali ba zai bamu ba. Duk mutumin da kewa GMB fatan yaci zabe ba abinda yake so kamar ayi zabe lafiya. 

Wannan abin a musulunce haramun ne, domin barna ce, lalata dukiya ne, almubazzaranci ne, Allah kuma ya hana almubazzaranci. Haka kuma, indai mun fahimci manufar siyasa shi ne a kyale kowa yayi ra'ayinsa, na meye, wasu zasu hana wasu ra'ayinsu? Kada mu manta GMB yana bukatar goyan baya a kudanci dan cin zabe, kamar yadda yake a Arewa, dan haka bai kamata mu bayar da kofar da za'a ci zarafin magoya bayan GMB a kudu ba. Dan haka mutane suji tsoron Allah su kaucewa tashin hankali cikin wannan zabe. 

Allah ya la'anci masu tada fitina. Allah ya bamu zaman lafiya, ya sa ayi siyasa cikin kwanciya hankali. Ayi zabe lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
10-01-2015

No comments:

Post a Comment