Sunday, January 11, 2015

Abinda Soji Sukaiwa 'Yan Agajin Izala


ABINDA SOJI SUKAIWA 'YAN AGAJIN IZALA

Yau mun wayi gari da labari mara dadi daga cikin irin labaran da suke fitowa kowacce safiya daga garuruwanmu, cewa wani Shu'umin soja azzalumi dan ta'adda ya bude wuta ga tawagar 'yan Agajinmu na Izala a lokacin da suke dawowa daga garin Misau a daren jiya bayan kammala wa'azi. Bayanai sun nuna cewa sojojin da ke kan hanya a shingen masu bincike sun tare wannan mota, bayan gamsuwa da bayanai sojojin suka baiwa motar umarni ta shige.

Bayan haka, tashin motar daga shingen jami'an tsaron ke da wuya aka ce wani soja ya budewa motar wuta, wanda hakan yayi sanadiyar jikkatar dan uwa dan agaji. Akan wanne dalili aka budewa wannan mota wuta? Wannan cikaken zalinci ne da sojojin da muke tausayawa a lokacin da aka yankewa wasu daga cikinsu hukuncin kisa bisa abinda ake gani zalinci ne wannan hukunci. Wadannan sojoji su ne mukewa fatan alheri tare da yaba musu akan yadda suka bayar da rayuwarsu dan kare kasarmu, amma abin takaici mu da muke musu fatan alheri mu zasu dinga budewa wuta akan hanya!

Ba shakka munyi Allah-wadai da wannan aikin ta'addancin da soja sukai mana, muna kuma kiran da lallai ayi bincike dan kamo wannan soja da ya aikata wannan aikai-aika dan a hukuntashi bisa tanadin dokar kasa. Adalci shi ne zai zaunar da mu lafiya ba zalinci ba. Babu yadda za ayi ace sojojin da muke tausayawa a lokacin da suke cewa an zalince su kuma ace akanmu zadu dinga huce haushi.

Lallai mun san cewa jami'an tsaronmu suna kokari wajen kare Najeriya daga hare-haren 'yan ta'adda, wannan kuma ba zai taba zama dalilin da zai baiwa Sojoji lasisin aikata mana zalinci ba a lokacin da suke guduwa daga garuruwa suna barin aiki.

Muna fatan Allah ya sanya mana aminci da nutsuwa a kasarmu. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya. Ina kuna amfani da wannan dama wajen mika sakon na na taya jaje ga Shugaban Izala na kasa Sheikh Bala Lau Abdullahi a bisa wannan abu da ya faru Allah ya kiyaye aukuwar haka anan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
11-01-2015

No comments:

Post a Comment