Thursday, January 22, 2015

Sarkin Saudiyya Na Shida (6) Abdullah Ya Kwanta Dama



SARKIN SAUDIYYA NA 6: ABDALLAH YA KWANTA DAMA

Yau juma’a daya daga cikin manyan ranaku a Musulunci, Allah ya karbi rayuwar Sarki Abdullah Ibn AbdulAzizi Al-Saoud na Saudiyya. Allah yayi Sarki Abdullah rasuwa bayan ya sha fama da jinya ba mai tsanani ba, kamar yadda rahotanni suka nuna Sarki Abddullah ya jima yana fama da cutar Numoniya har zuwa lokacin da hukumomi a Riyad suka bayar da labarin kwantar da shi a wani asibii dake Riyar a makwannin da suka wuce. Abdullah Ibn AbdulAzizi ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya, ya rasu yabar ‘ya ‘ya da jikoki masu yawa, haka kuma, Sarki Abdullah shi ne Sarki na Shida (6) tun bayan kafa daular Saudiyya a Shekarar 1930.

Marigayi Sarki AbdulAziz Ibn Abdulrahman Ibn Muhammad AlSaud wanda ake yiwa lakabi da Abu-Turki Akhu-Noura, shi ne ya jagoranci Jihadin kafa Daular Sa’udiyya a yankin Hijaz. Bayan rasuwar Sarki AbdulAziz Alsaud a shekarar 1953, yarima mai jiran gado wanda shi ne babban dansa Sa'ud Ibn AbdulAziz ya gajeshi a matsayin Sabon Sarki na biyu bayan kafa Mamlakatul Araabiyat Ass-Sa’udiyya.

Sarki Saud Ibn AbdulAziz ya karbi Sarauta daga mahaifinsa har zuwa shekarar 1964 lokacin da Allah yayi masa rasuwa. Kafin rasuwarsa Saud Ibn AbdulAziz shi ne wanda ya fara samar da majalisar ministoci a masarautar da suka hada da Ilimi, lafiya da kuma kasuwanci. Haka kuma, Sarki Sau’d ya zabi Gwamnan Riyad na lokacin wanda shi ne kaninsa Faisal Ibn AbdulAziz a matsayin Yarima mai jiran gado, inda bayan rasuwarsa Yarima Faisal Ibn AbdulAziz ya zama sabon sarki na uku.

Sarki Faisal shi ne mutumin da ake ganin har yanzu Sa’udiyya bata yi shugaba kamarsa ba, ana ruwaito Sarki Faisal a matsayin wani mutum mai ra’ayin bin addini sau da kafa, mutum ne mai san yin abu da gaggawa, bai cika wasaba, an bayyana shi a matsayin mutumin da bai cika yin dariya a bainar jama’a ba. Kullum maganarsa itace yadda za’a ciyar da addinin Musulunci gaba da kasashen.
A lokacin Sarki Faisal ne Masarautar Sa’udiyya ta fara samar da kamfanoni da kulla alaka da kasashen Gulf dan habaka tattalin arzikin yankin. Sarki Faisal ne ya jagoranci kafa kungiyaar kasashen Musulmi ta OIC, haka kuma, shi ne Sarkin da ya kafa garin Jeddah a matsayin cibiya ta kasuwanci. Sarki Faisal ya damu da harkokin addini ainun a zamanin Mulkinsa.

Sarki Faisal ya rasu a shekarar 1975, inda bayan rasuwarsa ne Yarima na lokacin kuma Gwamnan Riyadh, Khalid Ibn AbdulAziz ya zama sabon Sarki na hudu. Sarki Khalid shi ne Sarki na Farko da ya fara tsallaka Hijaz zuwa kasar Amurka domin yin ziyara da kuma bude ido. Sarki Khalid yayi kokari wajen kulla alakar kasuwanci tsakanin kasashen yankin Gulf inda ya samar da kungiyar GCC da ta hada Qatar, Kuwait, Bahrain, Oman, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Saudiyya.
Bayan da Allah ya yiwa Sarki Khalid Rasuwa a shekarar 1982 ne Fahad Ibn AbdulAziz ya zama sabon sarki. Sarki Fahad shi ne Sarki mafi dade a kan karagar Mulkin Saudiyya domin ya shafe Shekaru 23 a matsayin Sarki. Sannan kuma, shi ne mutum na farko da aka fara yiwa lakabi da Khadimul Haramain Ash-Sherifain (Custodian of the two holy mosques), Sarki fahad ya kawo sauye sauye masu yawa a kasar Saudiyya ta fuskar lafiya da ilimi da gina kasa da habaka tattalin arziki.

Haka kuma, Sarki Fahad shi ne mutumin da ya tsaya kai da fata wajen ganin an samu ‘yantacciyar kasar Palasdinu, da kuma tsayawa wajen warware mamayar da Iraqi ta yiwa Kuwaiti, haka kuma ya tsaya kai da fata wajen ganin an warware rikicin kasashen Bosnia-Herzegovina, Kosovo, Checniya, Afghanistan, Somaliya da kuma yankin Kahsmir. Bayan haka, a lokacin Sarki Fahad ya maida hankali wajen taimakawa kasashen Musulmi matalauta da suka hada da Somaliya da Bosniya da Afghanistan da sauransu. Allah ya yiwa Sarki Fahad rasuwa a shekarar 2005, inda Yarima mai jiran gado Marigayi Abdullah ya gajeshi, Abdullah shi ne mutumin da yafi kowa daukan lokaci a matsayin Yarima mai jiran gado.

Bayan zamansa Sarki na shida ne Abdullah Bin AbdulAziz ya zabi kaninsa Nayef a matsayin Yarima mai jiran gado, sai dai cikin kaddararSa Subhanahu Wata’ala, Yarima Nayef ya riga Sarki Abdullah rasuwa, inda aka maye gurbinsa da Yarima Salman a matsayin sabon yarima mai jiran gado. Sarki Abdullah za’a jima ba’a manta da shi ba, domin ya cigaba da amsa sunan Khadimul Haramain Ash-Sherifain inda ya kawo sauye sauye masu yawa a Masallacin Makkah da Madina da ba’a taba gani ba a tarihin Saudiyyah. Yayi aiki tukuru wajen ganin ya hidimtawa Masallatan Allah masu alfarma. Ya taimaki addinin Allah gwargwadan iko.

Sarki Abdullah ya samar da manya-manyan jami’o’in kimiyya da fasaha da kere-kere guda biyu da suka hada da Jami’ar King AbdulAzizi da kuma Jami’ai Noura ‘yar uwar mahainsu. Kafin zamansa Sarki Abdullah ya rike mukamai da yawa na Minista inda ya rike ministan tsaro da kasuwanci da cikingida sannan ya zama Gwamnan Riyadh. Sarki Abdullah Bin AbdulAzizi ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya a lokacin da Saudiyya ta cika Shekaru 84 da kafuwa. Za a jima ana tunawa da Sarki King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud wajen tsayawarsa kai da fata akan kasar Bahrain wajen ganin bata fada hannun 'yan Shiah ba.

Yanzu dai Yarima Salman Ibn AbdulAziz dan shekara 79 shi ne zai zama sabon Sarki na bakwai (7), inda shima ya zabi wani matsahi Yarima Mukrim a matsayin mai jiran gado, kuma shi ne ake zaton mutum na karshe daga ‘ya ‘yan AbdulAziz da zai rike Sarautar Mahaifinsu. Yau in sha Allah bayan kamala Sallar Juma’ah za ayi jana’izar Sarki Abdullah. Muna yi masa adduar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya sa Aljannah ce makomarsa, Allah ya biyashi ladan hidimar da yayi dakunanSa masu alfarma a Makkah da Madina, Allah ka yafe masa kurakuransa. Allah ya kyauta bayansa. Allah ka jikan Musulmi.

Yasir Ramadan Gwale
22-01-2015

No comments:

Post a Comment