Tuesday, January 6, 2015

Duna Wakilin Arna


DUNA WAKILIN ARNA

Sau da yawa nakan ji irin wannan magana ana yinta, kuma kai tsaye a jingina ta ga Malam Ibrahim Shekarau. Kalmomi ne guda uku kalmar DUNA da WAKILI da kuma ARNA, wadannan su ne suka bada jumla mai bada maa'ana. Idan muka dauki kalmar DUNA wannan kalma tana nufin wani LAUNI mai duhu ko kuma ace baki, launi shi ne ko ita ce color da turanci, ya Allah wannan launi na mutum ne, ko dabba, ko wani abu da ababen halitta suka samar. Ana jingina kalar DUNA ga Malam Ibrahim Shekarau saboda yanayin launin jikinsa da yake da duhu!

Allah buwayi gagara misali, shi ne mamallakin mamallaka. Shine ya Halicci Abu Jahal da Abu Lahab daga cikin dangin Bamu Hashim, cikin kabilar Kuraishawa a cikin Larabawa. Idan akayi maganar al'umma aka ce larabawa to su ne karshe, domin Allah buwayi gagara misali ya sanya Manzon Allah SAW cikamakin Annabawa ya zam balarabe kuma cikin kabila mafi buyawa a tsakanin kabilun Larabawa, hakanan ya sanya Manzon Allah ya fito daga tsatso na gidi wato irijinal din, BANU HASHIM, ga kasancewarsu Larabawa ga kyaun suffa, ga shi Annabin da Allah ya ce shi ne cikamakin Annabawa ya fito daga cikin wannan kabila, wannan ya isa abun alfahari, idan ana cikin muhalli na alfahari.

Kasancewar mutum Bahashime Bakuraishe Balarabe, wannan ba zai amfaneshi da komai ba face yayi Imani da Manzon Allah shi ne cikamakin Annabawa, kuma yazo da addinin gaskiya. Wannan shi ne kadai lasisin da zai baiwa mutum saduwa da Allah lami lafiya. Na kawo wannan bayani ne dan na buga mana Misali, domin ga Abu Lahab ya fito daga cikin kabilar Manon Allah SAW amma cikin kaddararwarSa Subhanahu Wata'ala ya sanya shi cikin wadan da basu yi Imani ba, dan haka ne ya zama katafaren Arne makamashin wuta a ranar gobe alkiyama.

Haka kuma, Allah Buwayi gagara Misali, ya sanya Malam Ibrahim Shekarau mai duhun fata ko baki daga kabilar Babur, wanda a jihar Borno bata ita ce Madaukakiyar Kabila ba, Allah ya zabi Malam daga cikinsu ya azurtashi da Ni'ima ta Musulunci. Sannan ya daukaka darajarsa, ya zama Gwamnan katafariyar Jiha a Najeriya Jihar Kano, duk da wasu daga cikin Madaukakiyar Kabila a yankin jihar Borno sunyi masa Hassada da kyashi amma shi Allah babu ruwansa da hassadarsu Subhanahu Wata'ala. Bayan ya zamar da shi Gwamnan Jihar Kano, ya bashi mukamin Ministan Ilimi na tarayyar Najeriya baki daya, wannan wata falalace daga Allah. Watakila Allah ya bashi wannan dan ya jaraba Imaninsa.

Masu yi masa yarfe da cewa shi din DUNA ne, to Allah cikin kaddarawarsa ya sanya shi fitowa daga kabilar Babur kuma mai duhun fatar da wasu ke cewa DUNA. to duk wanda ya kushe Malam Shekarau saboda launin jikinsa ba shakka yana kalubalantar Allaah ne makagin Malam Shekarau ya sani ko bai sani ba, domin ba'a yi shawara da iyayan Malam Shekarau ba kafin sanya dantayinsa a cikin mahaifiyarsa. Allah shi yaga dama ya hallicemu yadda muke, Manzon Allah kuma ya gaya mana cewar wanda yafi wani a wajen Allah, shi ne wanda yafi Imani a cikinmu. Na san kuma a zamantaakewa irin ta rayuwa babu wanda zai yi maka gori a kasar bakaken fata cewa kai baki ne indai ba shi din ubansa ZABIYA bane. Zan cigaba In Sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
06-01-2015

1 comment: