Monday, January 12, 2015

Me Zai Hana A Gano 'Yan Matan Chibok?


IDAN HAR ZA'A IYA GANO JIRGIN AIR ASIA, ME ZAI HANA A GANO 'YAN MATAN CHIBOK?

Hukumomi a Jakarta-Indonesia sun bayar da sanarwa tsamo baraguzan jigin saman kamfanin Air Asia da ya lume a ruwa da kusan mutane 170. Bayan an tsamo gawarwakinsu an kuma tsamo dagargazazzun baraguzan jirgin daga cikin teku, sannan abu mafi muhimmanci, shi ne, an gano jakar da ake kira Bakin Akwatu, dan samun bayanan yadda jirgin ya fadi.

Shi dai wannan Jirgi na Air Asia, an daina jin duriyarsa ne gaba daya bayan da rahotanni suka ce ya tashi daga Surabayo a kasar Indonesia zuwa Singapore. Jirgin ya bace bat, kamar yadda hakan ta faru a makwabciyar Indonesia wato Malaysia a Shekarar da ta gabata. Tun daga nan, aka shiga laluben inda jirgin ya shiga, inda aka bazama nema ta sama ta kasa da ta cikin ruwa. Da taimakon Allah masu linkaya suka fara gano alamun cewa jirgin ya lume ne a ruwa.

Hukumomi a Jakarta sun dukufa haikan, wajen tsananta bincike a ruwa, har Allah yasa aka kai daidai inda jirgin ya fadi kuma aka tsamo garwakin mutane da yawa, sannan dirka-dirkan baraguzan jirgin da suka tarwatse a ruwa suka lume duk aka lalubo kuma aka dauko su zuwa gabar teku. Wannan wata muhimmiyar Nasara ce da Hukumomi suka ci a Jakarta-Indonesia wajen gano wannan jirgi.

A Najeriya shekarar da ta gabata aka bada labarin sace 'yan mata sama da 200 a makarantar Sakandiren Chibok, wanda kafin sace na Chibok sai da aka sace 10,20,30,40 a garuruwan Miri, Mafa, Konguga da sauransu. Sace 'yan matan Chibok ya daurewa mutane kai da dama a duniya, ta yadda d dama suna mamaki yadda  za'a ce an saci wadannan 'yan mata. Kusan da yawa sun karyata labarin faruwar hakan in banda su Boko Haram sun saki wani faifan Video da ya nuna wani sashe na 'yan matan.

Satar wadannan 'yan Mata ta dauki hankalin duniya sosai. Inda har hakan yayi sanadiyar samar da kungiyar #BringBackOurGils wannan ya karade kusan ko ina a duniya, inda aka dinga ganin manyan mutane da Hash Tag na kiran a dawo da 'yan Matan Chibok da suka hada da Matar Obama, McCain da Piraministan Burtaniya Cameron. Na tabbata wannan al'amari da a wata kasa ne ba Najeriya ba ko Afeika da tuni wani batun ake daban.

Lallai inda gaske ne kasashen duniya su taimakawa Najeriya wajen ganin an ceto wadannan mata na Chibok. Ya kamata kamar yadda muka ga an taru a Paris dan taya faransa Makokin mutane 12, to akalla Shugabannin Afurka gaba daya su taru a garin Chibok dan jajantawa iyayan wadannan 'yan mata, tare da matsawa Gwamnatin Najeriya tayi duk abinda ya kamata wajen ganin an kubutar da 'yan matan Chibok.

Gaskiya a shekarar 2014, batun sace 'yan Matan Chibok shi ne abinda yafi bani mamaki matuka da gaske, abin kamar wasan-kwaikwayo amma kuma gaskiya ne, ace an sace Mata sama da 200 kamar Tumaki. Satar wadannan Mata ba ita ce abu mafi ban mamaki ba, illah yadda akayi aka sace su din, domin a Najeriya wannan ba abin mamaki bane sace mutum, dan an taba sace Gwamna Chris Ngige yana matsayin gwamna aka ce an sace shi. Amma yadda aka sace din shi ne zai fi zama abin mamaki.

Watakila nan da wani lokaci Najeriya ta zama kasa mafi abubuwan al'ajabi a duniya, indai ba al'amura ne suka sauya. Domin abinda ake jin ba zai taba faruwa ba a wata kasar to  Najeriya yana faruwa. Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale
12-01-2015

No comments:

Post a Comment