Sunday, June 1, 2014

Tsakanin Larabawa da Turawa da bakaken fata!!!

Da ba dan Turawa ba da har yanzu Larabawa suna cikin duhun kai da nuna isa da Girman Kai da fariya da alfahari da nuna tsananin kyama ga wanda ba Balarabe ba musamman Bakar fata. A yanzu babu wadan da Larabawa suka dauka da mutunci kuma suka dauka su ne mutane suke girmamasu kamar Turawa, amma kuma shi Bature baya kyamar mutane dan saboda launin fatarsu a halin yanzu, sukan dauki mutane duk daya, wannan ta sanya Larabawa suka fara dawowa daga rakiyar karkataccen tunanin kyamar Bakaken mutane domin Turawan da suke zakwadi akansu su basa kyamar Bakar fata a zahiri idan Mu'amala ta hada kamar yadda Larabawa suke yi babu kunya babu tsoron Allah. Kadan ne daga cikin Larabawa wadan da suka yi Ilimi suka waye ta fannin Addini da Rayuwa suke girmama mutum ba tare da la'akari da launin fatarsa ba.

Zaka sha mamaki idan aka ce maka idan banda 'yan wadansu Shekaru kalilan Larabawan Palasdinu da Mafiya yawan Bakar fata Musulmi suke jin zafi da radadin halin da suke ciki na kunci da kaskanci arkashin danniya da muzgunawar Israela cewa sun tsani bakar fata, haka sauran larabawa da dama suke, Larabawan gaskiya da na karya! Domin da yawan larabawan da suke cewa su Larabawa ne a yanzu Barbarar yanyawa ne galibinsu kabilu ne, idan ka cire Sa'udiyya da Yemen da wani sashi na Iraqi da Bahrain da Palasdinu da Kuwaiti da Daular Larabawa da Qatar, amma mafiya yawancin sauran ba Larabawan gaskiya bane irinsu Masar da Jordan da Syria da Lubnan da Oman da Aljeriya da Morocco da Tunisiya da wagairuhum, kamar yadda galibin 'yan Israela suma ba Yahudawan gaskiya bane.

Da yawan Larabawa indai kai Bakar fata ne kawai su a wajensu Musulunta ka yi, dan haka suke mu'amalantar bakaken fata musulmi kamar sabbin Musulunta. Wani abin almara da ya taba faruwa da ni, wata Malamarmu Balarabiya kanta babu dankwali siket dinta iya kwabri, gani da gemu irin na Ustazai ga tabon Sallah a goshi na amma wai tana tambaya ta wai ko ni din Musulmi ne! kaji Larabawan zamani. Alhamdulillah, ya zuwa yanzu jinsin Bakar fata na kara wanzuwa sosai a tsakanin kabilun Larabawa domin hatta a gidan Sarautar Saudiyya akwai Bakar fata kuma tsatson Al-Sa'ud domin ta tabbata Sarki Faisal Allah ya jikansa ya auri Bakaken fata masu asali daga Afrika. Allah da yayi mutanan Turkiyya farare Tas ya yi mutanan Khaleej masu haske shi ne wanda ya yi Bakaken fata a Kenya da Sudan Ta Kudu da Burkina faso. Babu wanda ya fi wani a wajensa Subhanahu Wata'ala sai wanda yake da TsoronSa. Ya Allah ka azurtamu da tsoronka.

YASIR RAMADAN GWALE
01-06-2014

No comments:

Post a Comment