Wednesday, June 11, 2014

Fatanmu Sanusi Lamido Sanusi Ya Gaji Mahaifinsa


FATANMU SANUSI LAMIDO SANUSI YA GAJI MAHAIFINSA

Malam Sanusi Lamido Sanusi tsohon tubabben Gwamnan Babban Banki Najeriya CBN. Yana daga cikin wadan da wasu ke fatan samun wannan Sarauta ta jihar Kano, da dama suna fadin haka ne saboda ganin irin kusancinsa da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. Gwamna Kano shi ne zai yi zabi na karshe akan wanda zai zama sabon Sarkin Kano, bisa tattaunawa da shawarwari na manyan dattawa daga jihar Kano da kuma lura da inda ra'ayin al'umma ya karkata, kamar yadda a baya lokacin nadin Sarautar Wazirin Kano, Gwamna yace yabi ra'ayin al'umma wajen kin amincewa da Malam Nassir Muhd Nassir (LDC) a matsayin sabon Wazirin Kano.

Kamar yadda mafi rinjayen ra'ayin al'umma ya nuna, shi ne, suna fatan daga cikin 'ya 'yan Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero wai ya gajeshi, duba da irin yadda Sarkin ya shafe shekara da shekaru yana rike da sarautar Kano, wannan wasu na ganin ita ce karramawa da za'a iya yiwa Sarki bayan Ransa a baiwa Dansa wannan sarauta. Wanda kuma yafi cancanta kamar yadda daga cikin 'ya 'yan Sarki mutum Takwas (8) dake rike da Sarauta suke mika wuya da goyon baya ga babban Dan Sarki Muhammadu Sunusi Lamido Ado Bayero a matsayin wanda zai gaji mahaifinsu, muna fatan Gwamnati ta girmama wannan ra'ayi na al'umma.

Haka kuma, Malam Sanusi Lamido Sanusi da ake ganin hankalin Gwamnati yafi karkata gareshi, muna fatan shima zai gaji Mahaifinsa. Mahaifin Sanusi Alhaji Aminu Sunusi shi ne tsohon Chiroma Kano, ya rike wannan Sarauta har rasuwarsa, kuma d'a ne ga tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi, muna fatan, idan Allah ya baiwa Chiroman Kano sabuwar Sarautar Sarkin Kano, shi kuma zai nada Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon Chiroman Kano Hakimin Gwale dan shima ya gaji mahaifinsa. Allah ya tabbatar mana da alheri. Sunusi Ado Bayero Allah ya amince maka.

YASIR RAMADAN GWALE 
08-06-2014

No comments:

Post a Comment