Tuesday, June 24, 2014

ZABEN EKITI: Ekitawa Sun Guntulewa Bola Tinubu Yatsa Daya

Bola Tinubu Madugun APC

ZABEN EKITI: Ekitawa Sun Guntulewa Bola Tinubu Yatsa Daya

Zaben da aka yi a makon da ya gabata a jihar Ekiti, shi ne zabe na baya-bayan nan da hukumar zaben Najeriya karkashin jagorancin Farfesa Attahiru Jega ta bugi kirji da shi wajen cewa anyi tsantsar gaskiya da adalci a zaben, abinda ya kara gasgata hukumar zabe shi ne, sakon karbar kaddara da dan takarar APC kuma Gwamna me ci Kayode Fayemi ya fitar a ranar Lahadi, inda ya taya dan takarar PDP Ayo Fayose da ya samu nasara murna ya kuma yi masa fatan alheri.

Babu shakka Ekitawa sun zabawa kansu makomar da ita suke ganin ta fi zama a’ala a garesu. Gwamna Kayode Fayemi ya burgeni ainun akan abin da ya faru, inda ba tare da wani bata lokaci ba ya karbi sakamakon zaben ya kuma taya sabon Gwamna murnar samun nasara, irin wannan siyasar da muke gani a Amerika da sauran kasashen turawa muke fatan ‘yan siyasarmu su yi koyi wajen karbar kaddarar faduwa zabe ba tare da wani kunji-kunji ba, duk da cewa ba laifi bane wanda yake ganin an zalince shi ya je kotu dan a bi masa hakkinsa.

Sai dai wannan zabe ko shakka ba zai yiwa Madugun jam’iyyar APC Bola Tinubu dadi ba, domin daga cikin ‘yan yatsunsa guda biyar Ekitawa sun guntule masa daya a yankin da yake tunkaho da takama da shi, har ake yi masa kirarin mutum mafi buyawa a siyasar yankin Kudu maso yamma day a kunshi Yarabawa Zalla.

Amma ga duk wanda ya san tarihin siyasar sabon Gwamna Fayose ba zai yi mamaki da wannan nasara da ya samu ba. Domin ya yi gwamna a baya kuma ya nuna kwazo, gashi matashin manomi mai matukar kaunar Talakawa, mutum mai son shiga cikin jama’a yana mu’amala da su, wannan ta sanya talakawa suka saki jiki da shi sosai, mutane da dama sun bayar da shedar irin karamci da son jama’arsa da Fayose yake yi.

Yanzu kuma babu wani abu da ya rage illa mu tsumayi zaben jihar OSUN da shima yake tafe nan gaba a wannan shekarar ta 2014. Shin suma Osunawa zasu sake guntulewa Tinubu yatsa ko kuwa zai sake karfafa ikonsa a siyasar jihar, wannan lokaci ne kawai zai bayar da amsa, amma dai ba shakka Gwamna Rouf Aregbesola na daga cikin gwamnonin da suke kamanta gaskiya a tsakanin Gwamnonin yankin Yarabawa. Da alheri.

23-06-2014

No comments:

Post a Comment