Thursday, June 5, 2014

Yadda Aka Yi Nadin Wazirin Kano Da Gwamnati Ta Taka!!!

YADDA AKA YI NADIN WAZIRIN KANO DA RAWAR DA GWAMNATI TA TAKA!!!

Kamar yadda na yi bayani a rubutun da ya gabata a jiya, bayan rasuwar Wazirin Kano Sheikh Isah Waziri Allah ya jikansa, Mai Martaba Sarki ya tafi jinya Landan inda ya shafe kwanaki 78 baya Kano. Bayan dawowar Mai Martaba Sarki ne, Malam LDC ya je gaida Sarki da yi masa barka da zuwa da ya jiki, sun kuma tattauna da Sarki a kebe, bayan fitowar Malam LDC ne ya fara bada sanarwar nadashi a matsayin sabon Wazirin Kano. A bisa al'ada ta Mai Martaba Sarki (Allah ya kara masa lafiya), babu wani nadi da yake yi na wata Sarauta face ya shawarci Emirate Council dan tattaunawa da jin shawarwarinsu akan mutumin da ya dace a baiwa Sarauta kaza. Amma cikin kaddarawa tasa Subhanahu Wata'ala, a wannan marra sai Mai Martaba Sarki ya tabbatarwa da Malam LDC Sarautar Wazirin Kano ba tare da shawarar Emirate Council ba, wannan kuma ta sanya da dama daga cikin Manyan Hakimai da manyan fada da suka ji labarin nadin haka daga sama, abin ya zo musu da bazata.

Bayan da labari ya fara bazuwa ne daga Malam LDC cewa na nada shi Wazirin Kano, sai wasu daga cikin manyan 'yan Majalisar Sarki suka tambayi Uwar Soro gaskiyar wannan labari, nan ta ke ta garzaya ta tambayi Sarki akan rade-radin da suka ji a gari cewa mai Martaba ya nada Malam LDC sarautar Wazirin Kano, Mai Martaba kuma ya tabbatarwa da Uwar Soro cewa eh shi ya yi wannan nadin! A shekaru 51 da Mai Martaba Sarki ya shafe yana Sarautar jihar Kano kusan komai yana yinsa ne da Shawara, amma cikin jarrabawa ta ubangiji aka jarrabi Mai Martaba Sarki akan wannan nadi, dan haka ne da dama suka karbi wannan a matsayin ajizanci irin na dan Adam, duba da cewa Shekaru sun yiwa Mai Martaba Sarki yawa, gabbansa sunyi rauni, Allah ya kara masa lafiya.

Bayan wannan nadi da mai martaba Sarki ya yi, ya kuma sauya wasu Sarautu tare da nadin Sabon Hakimin Kura sannan aka sauya masa Sarauta daga Tafidan Kano Hakimin Kura zuwa Dan Darman Kano. Mai Martaba Sarki kuma ya yi umarni da a rubuta takarda a sanar da gwamnati wannan nadi da aka yi. To a gefe guda kuma jama'a suka fara yin gunaguni akan cancanta da dacewar Malam LDC akan wannan kujera ta Wazirin Kano, inda da dama suka yi korafi ta hannun manyan fada akan su roki Sarki ya sake Shawara akan wannan nadi da ya yi. A dab da faruwar wannan lamari kwana uku ko hudu kafin wannan nadi Mai Martaba Sarki zai yi, Mai Girma Gwamnan Kano ya je gidan Sarki inda ya gana da Sarki yake nemawa Dan Majen Kano Malam SLS Hakimcin Kura, Sarki ya baiwa Gwamnan hakuri akan tuni an riga anyiwa Bello Bayero sauyin Sarauta zuwa wannan sarauta kasar Kura.

Daga nan turka-turka ta kunno kai akan wannan nadi, inda gwamna ya samu irin wadancan korafe-korafe da aka yiwa Fada akan nadin Malam LDC, nan shima ya hau kujerar naki akan wannan nadi, labari yaje har kunnen Sarkin Musulmi a bisa abinda ke faruwa akan wannan nadi da Mai Martaba Sarkin Kano ya yi da kuma tirjiyar da gwamnatin Kano ta yi akan wannan nadi, cikin gaggawa Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya aiko da Manzo na musamman daga Sakkwato domin yazo ya binciki me ke faruwa tsakanin Gwamnati da Masarautar Kano, an turo Magajin Garin Sakkwato domin ya ji me ke faruwa kuma ya yi kokarin sasantawa idan zai iya. Cikin ikon Allah aka lallabi Sarki akan ya duba koken da al'umma suka yi ya yi wani abu da zai sanya farinciki a zzukatan al'ummar kano akan wannan batu. Mai Martaba Sarki ya gamsu ya sauya ra'ayinsa akan wannan nadi.

A gefe guda kuma ita Gwamnati ta ki karbar nadin da aka yiwa Hakimin Kura da kuma Wazirin Kano da sarautu guda hudu da aka sauya. Daman akwai jikakkiya tsakanin Mai Girma Gwamna Dr. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso da wanda aka nada a matsayin Wazirin Kano, amma ko kusa wannan ba shi ne dalilin da ya sanya gwamna ya ki yarda da nadin ba, illa wasu al'amura da suka wakana wanda nan ba muhallinsu bane.

Bayan anyi wannan nadi Malam LDC na shirin fara tafiyar da Sarautar Waziri, al'amura suka yi dumi dangane da nadin, har ta kai Mataimakin Gwamna ya yi magana da yawun Gwamnti cewar basu aminta da wannan nadin ba. kamar yadda na fada a baya, bayan da aka roki sarki kuma ya aminta yabi abinda jama'arsa ke so ya bada umarnin a warware wannan nadi kwana uku bayan an nada Malam LDC, a nan ne murna ta koma ciki ga Malam LDC sannan a gefe guda kuma jama'a na murna da jinjina ga Mai Martaba Sarki a bisa yadda ya karbi koke-koken al'umma ya sanya farinciki a zukatansu. A dan haka ne aka umarci Wamban Kano babban Dan Majalisar Sarki ya yi taron manema labarai ya shaidawa duniya cewar an warware wannan rawani da aka nadawa Wazirin Kano Malam LDC.

A dan haka, wanda yafi cancanta da a yaba masa a wannan al'amari da ya faru shi ne Mai Martaba Sarki Alhaji Dr. Ado Bayero Allah ya kara masa lafiya, domin Sarauta ce da hakkinsa ne ya nada duk wanda yaga dama, amma ya sarayar da wannan hakki nasa dan sanya farinciki a zukatan al'ummar Kano, sannan bangare na biyu su ne Manyan 'yan Majalisar Sarki da kuma manyan hakimai da suka tsaya kai da fata wajen ganin kimar Masarautar Kano bata zube kasa ba akan wannan sarauta, sai kuma sashi na uku, wanda ita ce Gwamnatin Kano, wanda itama a nata bangaren ta yi kokari wajen ganin ta saurari koke-koken al'umma ta kuma yi abinda ya dace akai.

Alhamdulillah, yanzu kusan dukkan wata 'kura da ta taso tsakanin Fadar Mai Martaba Sarki da Gwamnatin Kano akan wannan nadi ta lafa kuma an fahimci juna an kuma yafewa juna akan abinda ya faru na 'yar turka-turkar da ta faru a tsakani. A hakikanin gaskiya wannan shi ne zahirin abinda ya wakana a yayin wannan nadi da aka yi illa iyaka na tsallake wasu abubuwa da ba lallai ne a fadesu a bainar jama'a ba. Muna fatan Malam LDC zai karbi wannan abu a matsayin kaddara da ta fada masa, muna kuma yi masa fatan alheri tare da kira a gareshi ya ji tsoron Allah ya kyautata tsakaninsa da Allah, sannan kuma ya kyautata tsakaninsa da al'umma. Akwai abin tsoro matuka ace al'umma su yiwa mutum mummunar Shaida. Allah ya tabbatar da mu akan gaskiya ya bamu ikon aiki da ita.

YASIR RAMADAN GWALE
06-06-2014

No comments:

Post a Comment