Tuesday, June 24, 2014

Wasika Daga Mundubawa Gidan Sardaunan Kano

Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano
WASIKA DAGA MUNDUBAWA GIDAN SARDAUNAN KANO

Bayan gaisuwa da fatan alheri ga al’ummar jihar Kano. A yanzu haka muna cikin wani lokaci da aka jarrabe mu da fitina da motsuwar zukata, muna cikin yanayi mara dadi, addu’ah da riko da sababin karbar addu’ah zasu yi tasiri matuka wajen fitarmu daga cikin halin da muke ciki, ta yiyu Allah ya dubi gajiyayyu daga cikinmu ko yaran da hankalinsu bai nuna ba ya kawo mana dauki ta inda bamu zata ba.

Kamar yadda kowannemu ya sani, a jiya Litinin al’ummar jihar Kano musamman wadan da ke yankin unguwar Kofar Nassarawa da unguwar bayan gidan Malamai (TSB) da sabuwar Kofa da Rumfa Kwaleji sun shiga dimuwa sakamakon wata fashewa mai karar gaske da ta faru a makarantar School of Hygiene, inda daga bisani bayanai suka tabbatar da cewar harin Bam ne aka kawo! Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Ba shakka dole hankula su dungunzuma, zuciya ta karaya, sakamakon abinda ya faru kuma ya zo da asarar rayuka.

Dan haka, ko a APC mutum yake, ko a PDP mutum yake, abu mafi muhimmanci shi ne, mu al’ummar Musulmai ne, kuma ba muda wani gari da ya wuce Kano. Wannan ta’addancin mu aka yiwa, al’ummar Musulmi ne suka shiga damuwa sakamakonsa, mutanan da suka mutu a dalilin wannan hari ‘yan uwanmu ne ‘yan jihar Kano Musulmi.

Ya ‘yan uwa masu girma, yana da kyau mu sani, idan masifa ta zo bata tambayar katin jam’iyya balle waye dan gari ko bako kafin ta afkawa mutum. Abinda ya fi dacewa mu yi a irin wannan lokaci shi ne addu’ah tare da komawa zuwa ga Allah, ba yin cece kuce da ba zai iya dawo da rayukan wadan da suka rasu ba. Lallai mu yawaita ambaton Allah, mu kuma rage aikata ayyukan sabo, muji tsoron Allah a cikin mu’amalolinmu na yau da kullum mu nemi agajin Allah a halin da muke ciki.

Allah ka tsare mana Imaninmu da mutuncinmu da rayukanmu. Ya Allah ka amintar da mu a cikin gidajenmu da garuruwanmu, Allah ka yaye mana wannan damuwa a cikin zukatanmu, iyalanmu da ‘yan uwanmu da abokanmu da dukkan al’ummarmu Allah ka zama gatanmu.

Muna kuma yin addu’ah ta musamman akan wadan da suka rasu, Allah kajikansu ka gafarta musu ka sa bakin wahalarsu kenan, masu aikata wannan aikin ta’addanci Ya Allah idan sun faku a garemu kai basu faku a gareka ba, Allah ka bi mana hakkinmu, Allah karka baiwa ‘yan ta’adda dama akan al’ummarmu. Allah ka wargaza shirinsu ka mayar musu da kaidinsu garesu.

Muna mika sakon jaje ga Gwamnatin Kano da al’ummar jihar Kano baki daya. Allah ya kare Jihar Kano da Najeriya baki daya. Wannan sako ne a madadin Mai Girma Sardaunan Kano Mallam (Dr.) Ibrahim Shekarau da dukkan Masoya da ‘yan uwa da abokan Mudubawa Avenue Kano.

No comments:

Post a Comment