Wednesday, June 4, 2014

Me Ya Sa Mutanen Kano Basa Son Dan Chakare A Matsayin Wazirin Kano?[1]

 
ME YA SA MUTANEN KANO BASA SON DAN CHAKARE A MATSAYIN WAZIRIN KANO? [1]

Da farko yana da kyau mu san waye Dan Chakare. Asalin Nassir Muhd Nassir da aka fi sani da Dan Chakare almaijiri ne na Malam Liman Dan Amo da yake a unguwar Daneji a cikin birnin kano, a lokacin da Dan Chakare yake matsayin almajiri bai cika maida hankali akan karatun addini ba, illa iyaka ya shahara da baiwa 'yan uwansa almajirai labarin Sarakunan zamanin da suka Shude irin tarihihi na Alfu-Laila-Wa-Laila ko Dare Dubu Da Daya, da Malam Liman Dan Amo ya lura cewa Nassiru baya karatu sai bayar da labarai barkatai, sai yake sanar masa cewa tunda ka iya bada labari ni zan kaika fadar Mai Martaba Sarkin Kano dan ka dinga sanya Sarki Nishadi da irin wadannan labarai naka, haka kuwa aka yi, Malam Liman Dan Amo ya je wajen Mai Martaba Sarki ya gabatar da Nasiru Muhd Nasiru a matsayin zai dinga kawo shi yana Nishadantar da Sarki, idan sarki ya bukaci yin nishadi sai ya sanar da Malam Liman Dan Amo, shi kuma ya zo da Nasiru fada dan ya baiwa Sarki Dariya da labaransa. Haka kuwa aka yi, duk lokacin da Sarki ya yi nishadi sai ya tura a sanar da Malam Liman Dan Amo ya zo da Nasiru dan ya baiwa sarki Dariya.

Ana haka, sai Dan Chakare ya samu shiga wajen Sarki, har ta kai yana zuwa ya baiwa Sarki labari shi kadai ba tare da ya sanar da Liman Dan Amo ba, ana haka sai Dan Chakare ganin ya samu shiga a wajen Sarki ya dinga yin rashin kunya ga manyan Hadiman Sarki, sannan kuma ya dinag Shiga Gidan Sarki babu Sallama. tafiya ta tafi har suka samu sabani da sarki ya daina zuwa wajen Sarki bayan da Sarki ya sa aka koreshi.

Daga nan ne ya koma wajen Khalifa Isyaka Rabi'u inda yake zama wajensa suna yin hira yana bashi labari, har ta kai shima, Malam Isiyaka Rabi'u ya yarda da dan Chakare ya dinga yin 'yan tafiye-tafiyensa na kasuwanci tare da Dan Chakare, a saboda amince masa da isiyaka Rabi'u ya yi, sai ya fara damfarar Isiyaka Rabi'u yana yi masa abubuwa na rashin gaskiya. Wannan ta sanya Khalifa Isiyaka Rabi'u ya kira taron Manema labarai ya nesanta kansa da Dan Chakare ya kuma yi kira ga dukkan abokan huldarsa da su kauracewa mu'amala da Dan Chakare.

Bayan da suka yi baram-baram da isiyaka Rabi'u sai Dan Chakare ya sake dawowa jikin Sarki bayan ya nemi afuwa da kuam 'yan dabarce-dabarcensa na Almajiranci, wannan karon ya cusa kansa fiye da yadda yake a baya a cikin fadar Sarki. Daga nan ne sarki ya fara sanya shi a cikin lamuransa. Har ya zama Alkali ya dinag aikata rashin gaskiya da musgunawa jama'a, wannan ta sanya a Unguwar Danaeji da Dan Chakare yake zaune Jama'a suka yi masa dukan tsiya suka koreshi daga unguwar, daga nan ne ya koma Unguwar Hausawa dake kusa da Kundila. Yana zaune yana zuwa wajen sarki yana gayawa Sarki karya da gaskiya kuma yana bin Sarki da 'Yan Tsatsube-tsatsubensa na ganin ya samu shiga a wajen Sarki har Mai Martaba Sarki ya sanya aka nadashi babban Limamin Masallacin Waje, wanda shi ne masallaci na biyu a Kano. Ko da Dan Chakare ya fara Limanci a Fagge ya dinga tsanantawa mutane ta hanyar yin doguwar huduba da karanta Doguwar Sura da nuna isa da gadara a cikin Huduba, domin yana yawan kiran Masu Saurarensa da Matsiyata ko Talakawa fakirai da sauran kalamai marasa dadi, haka nan kuma yakan sanya a kundume bishiyun masallaci a lokacin da ake tsananin zafin rana.

Bayan da yaga ya samu Shiga a wajen Sarki ya dinga yiwa dukkan mutanan fada Girman Kai da nuna isa, ta yadda baya ganin kimar kowa a fada idan ba Sarki ba. Nan Sarki ya sanya shi ya dinga yin Limancin Sallar Idi idan Limamin Masallacin cikin gari ya tafi Makkah Umara ko aikin Hajji, haka dai Dan Chakare ya dinga nuna isa da dagawa da takamar cewa shi wani ne. Ya cusa kansa a dukkan wasu al'amura da suka shafi addini a fadar Masaraurat Kano.

Kasancewar Dan Chakare ya yi karatu a Madina, Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba (Darul Hadith) da suka yi karatu tare ya taba cewa Malam Nassir yana daya daga cikin Dalibai masu hazaqa a tsakanin daliban lokacin, mutum ne mai kaifin kwakwalwa, amma yace babu ko shakka akan cewa Malam Nassir ba karamin tadari bane a lokacin da yake Dalibi a Madina, domin yana dalibi ya taba aske gemunsa ya zuba a cikin ambulan ya kaiwa Sheikh Bin Baz saboda nuna tsageranci, ya ce wannan kadan ne daga cikin irin takadaranci irin na Malam Nassir a lokacin da yake Madina,

Wadan da suka san Dan Chakare sun shaide shi da cewa mutum ne mai girman kai da san nuna isa da san Mulki. Mutum ne mai Shaddadawa a cikin al'amuransa, a dukkan cikin Malam da suke kano babu wani malami da ya nunawa Sunnah kiyayya a fili irin Dan Chakare domin yana daga cikin Malaman da suka san meye Sunnah amma suke mata zagon kasa da shirya mata dukkan kutunguila da Makida wajen ganin an tadiye tafiyar Sunnah a Kano. Malam Jaafar Adam (Rahimahullah) ya fada a cikin wata lakca da aka yi a Masallacin Usman Bin Affan Gadankaya mai suna #GwagwarmayaTsakaninKaryaDaGaskiya, cewa Limamin Waje yana bin dukkan hanyoyi a fada wajen ganin an kuntatawa Sunnah da Ahlussunnah.

Abu mafi muni a tattare da Dan Chakare shi ne yadda yake nuna goyon bayansa ga SHI'AH dan muzgunawa Ahlussunnah. A baya lokacin da Masallacin Aliyu Bin Abi-Talib dake dab da Randabawul na dangi a Kano, 'yan Shi'ah sun yi kokarin mamaye Masallacin ta hanyar shirya taruka da wa'azozinsu a wajen, wannan ce ta sanya 'yan Boko masu fahimtar Addini dake Sallah a Masallacin suka sanar da Manya a Kano dan a sauyawa masallacin suna daga Masallacin Aliyu Bin Abi-Talib zuwa Masallacin Umar Bin Khattab, cikin nasarar ubangiji kuwa aka sauyawa masallacin suna, tun lokacin da Masallacin ya koma sunan Umar Bin Khatab 'yan Shi'ah basu sake zuwa masallacin dan yin taro ko lakca ba, a dan haka ne, Dan Chakare ya kiraye su zuwa Massalacin Waje da aka fi sani da Masallacin Fagge inda yake limanci ya basu cikakkiyar damar yin dukkan tarukansu da al'amuransu, ba dan komai ba sai dan nuna tsananin kiyayyarsa da gabarsa ga Sunnah.

Zan cigaba In Sha Allah zuwa gobe, ku dakace ni.

YASIR RAMADAN GWALE
04-06-2014

No comments:

Post a Comment