Thursday, June 5, 2014

Me Ya Sa Mutanen Kano Basa Son Dan Chakare A Matsayin Wazirin Kano?[2]

ME YA SA MUTANEN KANO BASA SON DAN CHAKARE A MATSAYIN WAZIRIN KANO? [2]

A bayanin da na kawo jiya akan Malam Liman Dan Chakare, wasu suna cewar wai muna yiwa Malam Liman kazafi, babu shakka duk wanda yace abinda aka fada kazafi ne ko san rai, to babu shakka bai san waye Liman Dan Chakare ba. Akan wane dalili zamu yiwa Liman Dan Chakare kazafi bayan mun san laifin hakan yana da girma a Shari'ah. Wallahi duk wanda ya san waye Liman Dan Chakare to ya san cewa ba'a fadi komai akansa ba.

Ya isa abin misali a fahimci waye Liman Dan Chakare, ga duk wanda ya san badakalar da ta faru tsakaninsa da iyalin gidan Abacha zai tabbatar da dukkan maganganun da aka yi akansa. Malam Liman Dan Chakare ya yi amfani da sunan Mai Martaba Sarki Allah ya kara masa lafiya ba da sanin Sarki ba, ya dinga karbar kudi a hannun iyalin Abacha akan tsarewar da aka yiwa su Muhammad, karshe da dubu ta cika Maryam ce da kanta ta zo ta samu Sarki akan batun, Mai martba Sarki ya  tabbatar mata cewar shi bai taba sanya Liman Dan Chakare ya karbi wani abu da sunansa ba akan matsalar da ta faru. Wannan wata badakala ce da ta faru tun bayan tsare su Mohammed Abacha, wadan da suka san al'amarin sun sani, wadan da basu sani ba kuma iyalin Abacha na nan da rai za su bada bayani.

Bayan rasuwar Maarigayi Malam Isah Waziri, Mai Martaba Sarki ya tafi jinya Landan inda ya shafe kwanaki 78 baya gari, bayan dawowar Mai Martaba Sarki ne Liman Dan Chakare ya samu Sarki shi da shi suka gana, daga baya Liman Dan Chakare ya dinga bayar da sanarwar an nada shi WAZIRIN KANO, mukamin da daman ya jima yana neman a bashi. Ba tun yanzu Liman Dan Chakare ya so Wazirin Kano ba, tun bayan rasuwar Waziri Gidado Allah ya jikansa, ya so Mai Martaba Sarki ya bashi wannan Sarauta amma Mai Martaba bai yi hakan ba, duk da cewar Sarauta ce da mai martaba yake nada abokansa da aminansa, sai a yanzu da Shekaru suka yiwa Mai Martaba Sarki yawa gabbansa suka yi rauni, ajizanci ya riske shi abinda ya faru ya wakana.

A wannan nadin da aka yi masa, ta tabbatar cewar Fadar Masarautar Kano tana sauraron koke-koken al'umma, domin tun bayan sanarwar wannan nadi jama'a suka dinga kai korafinsu akan Malam Liman Dan Chakare da kuma bayanin irin halin da za'a iya shiga idan LDC ya cigaba da kasancewa Wazirin Kano. Wani abin da zai kara nunawa duniya waye LDC shi ne, daga bashi wannan Sarauta sai ya aikawa da iyalan Marigayi Malam Isah Waziri Allah ya jikansa da takarda yana umartarsu da su tashi daga gidan Wazirin Kano su koma wani wajen daban cikin awanni ashirin da hudu (24) yana san ganin Kangon gidan, iayalan Malam Isah Waziri sun shiga damuwa matuka da wannan wasika, kuma cikin nufin ubagiji Allah ya share musu hawaye aka ware masa nadin da aka yi.

Wadan da suka san Liman Dan Chakare sun san yadda yake kulafucin wannan Sarauta ta Wazirin Kano, an kuma sha jinsa yana maganar cewar ko sama da kasa zata hade sai ya zama Wazirin kano, cikin kaddarawa taSa Subhanahu Wata'ala, sama da kasa basu hade ba, Liman Dan Chakare ya zama Wazirin Kano na kwana hudu kacal! Wannan ko shakka babu dole tarihi ya rike, dole LDC ya shiga lissafin wadan da suka taba zama Waziran Kano. Har ila yau, da dama sunji LDC da bakinsa yana maganar wani Mafarki da ya ce yayi wanda duk mai hankali yasan wannan mafarki ba gaskiya bane, wanda wannan zai tabbatar da waye LDC. Wasu da dama suna koarin ai bamu fadi alkhairansa ba sai muke fadin kishiyarsu, mukam har ga Allah sai dai muce mun san cewa Malam LDC  Malami ne mai huduba mai Tamsiri, amma ayyukansa na zahiri su ne zasu tabbatar da gaskiyar ko waye shi, haka kuma, Shaidar da jama'a suka yi akansa kadai ta isa abin Misali akan waye shi.

Al'ummar kano da dukkan gwamnatocin da aka yi a kano masu tsananin biyayya ne ga mai martaba Sarki tare kuma da karbar dukkan wani abu da ya zo daga hannun mai martaba Sarki, amma akan Malam LDC al'umma suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan nadin, kuma Mai Martaba Sarki ya ji ya karba ya kuma Aminta ya kuma bada umarnin da a ware nadin da aka yi, muna kara jaddada godiya da addu'o'in fatan alheri ga Mai martaba Sarki, Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana. Shi kansa wannan nadi da abinda ya faru a lokacin nadin akwai al'amura da yawa a ciki masu ban mamaki wanda nan ba Muhallin fadinsu bane. Amma lallai al'umma su sani, babu wani abu da aka fada akan Malam Liman Dan Chakare wanda ba haka yake ba. kuma ina sake fada, duk wadan da suka Sanshi sun san ba'a fadi komai akansa ba. Malam LDC Dan uwanmu ne Musulmi, muna yi masa addu'ar Allah ya shiryeshi da mu baki daya shiriya ta gaskiya, Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu ikon aiki da ita, ya nuna mana kraya ya bamu ikon kauce mata. Wadan da suka ji haushin abinda aka fada sai su gafarce mu, dama shi harshe na gaskiya kaifi gareshi.

YASIR RAMADAN GWALE
06-06-2014

No comments:

Post a Comment