Wednesday, June 25, 2014

Anya Za'a Iya Yiwa Mubarak Bala Hukunci A Dokar Kasa Kuwa?

ANYA ZA’A IYA YIWA MUBARAK BALA HUKUNCI A DOKAR KASA KUWA?

Matashin nan da rahotanni a jiya suka nuna cewar ya sauya addininsa daga Musulunci zuwa wani abin daban ya zo da sarkakiya a tsarin shari’ar kasarnan. Shi dai wannan matashin bayanai sun nuna cewar ba wai ya canza sheka daga Musulmi ne zuwa kirista ba, illa iyaka yace shi bai yadda da samuwar Ubgajinmu Mahaliccinmu ba, Babbar Magana! A kashin gaskiya irin wannan batu na Mubarak Bala ba wani sabon abu bane, domin wannan na daya daga cikin aqidar Dirwaniyanci (Darwinism) abinda kawai za’a iya zamewa mutane sabo shi ne, shi Mubarak Bala ya karanta sashin kimiyyar hada sinadarai ne (Chemistry), sabanin idan a ce ya karanta “Sociology” ne wanda amfi samun masu irin wannan ikirarin a cikin wadan da suka karanci tsantsar sociology babu karatun addini a tare da su.
Amma wannan abinda da Mubarak Bala ya aikata duk kuwa da cewar ana tuhumar hankalinsa, ko da gaske yake yi akan batunsa ko bad a gaske yake yi ba, to lallai mu sani Mubarak Bala yana da cikakkiyar kariya ta kundin tsarin mulki da ba za’a iya zartar masa da hukuncin kisa ba, ko da kuwa ya kekesa kasa akan batun da yake ikirari.

A kundin tsarin Mulkin Najeriya na 1999, sashi na 38 karamin kashi na daya (1) ya baiwa duk dan Najeriya damar yin addinin da yaga dama, sannan kuma ya canza addinin da yake bi a duk lokacin da yaga dama ba tare da an tuhumeshi da aikata wani laifi ba. Wannan na daya daga cikin sashin da ya baiwa wata baiwar Allah mai suna Aisha waddata ta koma Musulunci daga Kiristanci kwanakin baya a jihar Neja wadda batun ta ya janyo kace-nace.

Haka kuma, sashi na 36 karamin kashi na goma sha biyu (12) yace babu wani abu da mutum zai yi ace laifi ne har sai idan wannan abin ya kasance a rubuce cikin wata doka wacce Majalisar kasa ko ta jiha ta yi doka akansa. A dan haka, a bisa dogaro da kundin tsarin Mulkin Najeriya wanda dukkan masu Mulki sunyi rantsuwar tabbatar da zasu bashi kariya a kowanne irin hali, wannan matashi ba za’a iya zartar masa da hukuncin kisa ba ko da kuwa ta tabbata ridda ya yi.

Dan haka, wannan yana daya daga cikin inda aka samu tarnaki a kundin tsarin Mulki da ya sabawa koyarwar addinin Musulunci. Wannan kuma kalubale na babba ga majalisun dokokin da suke aiwatar da Shari’ar Musulunci. A dan haka, yana da kyau jama’a su sani, a dukkan wasu kundin dokokin Panel Code da aka samar a jihohin da suke aiki da Shari’ar Musulunci babu inda aka ayyana hukuncin kisa ga wanda ya bar addininsa zuwa wani addinin daban. Saboda haka, a tsarin da muke kai a Najeriya, babu wani alkali da zai iya yankewa Mubarak Bala hukuncin kisa a irin wannan lamari sai fa idan laifin ya kasance rubutacce ne a cikin dokar kasa, wanda wannan babu shi a rubuce.

Babu shakka wannan al’amari zai bude wani sabon babi a kundin tsarin Mulkin kasarnan, zai kuma janyo wani sabon cece-kuce na daban, Allah ya kiyaye. Gwamnati dai ba zata iya zartarwa da wannan matashi hukunci kisa ba matukar ba kotu ce ta sameshi da laifin abinda ya aikata bat a ce ga hukuncinsa.

Haka kuma, tsarin Mulkin Najeriya yace dukkan wata doka ko wani tsari da yaci karo da kundin tsarin Mulkin Najeriya, to “constitution” zai kasance a sama da wannan tsarin ko da kuwa koyarwar wani addini ne. Wannan kuma shi ne babban tarnakin da kundin tsarin Mulkin Najeriya ya yiwa koyarwar addinin Musulunci, wanda zamu iya komawa majalisun dokoki na jihohin dan yin wasu dokoki da suka dace da koyarwar addininmu na Musulunci.

Dan haka, yana da kyau al’umma su sani cewar babu yadda masu Mulkin da suka rantse domin kare kundin tsarin Mulki tare da yi masa biyayya zasu yi wani hukunci da ya saba masa, saboda haka, a kurkusa abinda za’a iya yi tunda ba zamu iya canza kundin Mulki a yanzu ba, shi ne, a samu Malamai da masana su zauna da wannan bawan Allah Mubarak Bala su yi masa wa’azi da Nasiha ko Allah zai karkato da hankalinsa ya fuskanci irin hadarin day a jefa rayuwarsa idan hart a tabbata cewa yana da lafiyayyan hankali ya dauki hukuncin day a zabawa kansa na kin amincewa da samuwar ubangiji.

Sannan kuma, ya zama dole a aiwatar da bincike na me ya sanya wannan bawan Allah ya bar Musulunci zuwa wani abin daban, dan a samu bakin zaren yiwa wannan tufkar hanci. Allah ya kare mana Imaninmu, ya sa mu mutu muna cikin Imani mu tashi muna masu imani da Allah da ManzonSa Sallallahu Alaihi Wasallam. A gaba kuma zamu zo da abinda Musulunci yace game da abinda Mubarak Bala ya aikata In Sha Allah.

YASIR RAMADAN GWALE
26-06-2014


No comments:

Post a Comment