Saturday, May 31, 2014

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!!

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!

Daga Allah muke kuma gareshi zamu koma! Hakika jiya wasu abubuwa guda biyu sun tayar min da hankali. Abu na farko wani Video da Kabiru Danladi Lawanti ya yi sharing a Timeline dina wanda IG Wala ya saka shi, inda naga ana yanka mutane da ransu kamar Tumaki, babban abin da ya tayar min da hankali shi ne, mutanan da ake yankawa a gabansu ake yanka dan uwansu, sannan kuma wanda za'a yanka din ba daureshi aka yi ba, hannu kawai za'a sanya a dafe shi wani ya yanka, Subhanallah! Kuma suma wadan da ake yankawa din suna zaune suna kallo ba tare da sun nuna wani yunkuri na guduwa ko nuna damuwa ba. Wannan al'amari ya tayar min da hankali matuka!

Da farko na yi zaton cewa abin da ya faru a kasar Afurka ta Tsakiya ne, amma da na sake kallo sai naji Turancin da ake yi Pidgin English na Najeriya ne, haka ita ma gurbatattar Hausar da aka yi irin ta yankin Arewa Maso Gabas ce. Abinda na kasa ganewa shi ne, shin su waye suke aikata wannan mummunan aikin yanka mutane? Sannan su waye wadan da ake yankawa? Abin ya tayar min da hankali ainun!

Abu na biyu kuma, labarin da na ji a BBC cewa an sace Sarakuna masu daraja ta daya a Borno, ciki kuwa har Sarkin Gwoza ya samu Shahada. Ba shakka hankali na ya tsahi da jin wannan labari ace hatta Sarakuna basu tsira  daga wannan mummunan Bala'I na shekara da Shekaru ba! Manzon Allah ya yi gaskiya, yace ku guji tayar da fita domin tana shafar wanda ya janyota da wanda bai san hawaba balle sauka. Allah ya la'anci masu tayar da Masifa.

Ya Allah mun tuba daga laifukanmu, Ya Allah mun zalinci kawukanmu, Ya Allah mu masu laifi ne, Ya Allah kaine ka ce mu roke ka zaka amsa mana, Ya Allah kaga irin halin da muke ciki na tsanani da damuwa da tashin hankali Ya Allah ka kawo mana dauki. Ya Allah ka ceci rayukanmu. Ya Allah, Ya Allah Ya Allah ka kawo mana karshen wannan masifa da Bala'I.

YASIR RAMADAN GWALE
31-05-2014

No comments:

Post a Comment