Tuesday, May 13, 2014

Tsakanin Amerika Da Boko Haram Waye Abin Tsoro? [3]


TSAKANIN AMERIKA DA BOKO HARAM WAYE ABIN TSORO? [3]

Wasu da dama suna da tunanin ai babu yadda za'a yi Musulmi ya dinga kai ire-iren wadannan hare-hare na rashin imani da Boko Haram suke kaiwa. Dan haka ne suke kaddara cewa duk wanda zai kai irin wannan hari to ba Musulmi bane. Ko dai gwamnati ce a yadda wasu ke cewa wanda jagornta ba Musulmi bane, ko kuma  kungiyar Kiristoci ta kasa CAN wanda suma duk ana zarginsu. A kashin gaskiya duk wanda yake da tunanin cewa Muslmi ba zai iya yin abinda Boko Haram suke yi ba, to yana kishirwar sanin tarihin Musulunci. Domin Musulmi wadan da suke ikirarin Musulunci da fatan shiga Al-Jannah su ne suka kashe Sahabin Manzon Allah SAW kuma surikinsa Uthman Ibn Affan Allah ya kara yarda da shi, haka kuma Shia da suke ikirarin Musulunci suka kashe Al-Husain Ibn Ali jikan Manzon Allah SAW, dan haka, duk wanda ya san tarihin Khawarij a Musulunci, ya kuma karanta tarihin Sarkin Musulmi Hajjaj Bin Yusuf Ath-thaqafy to ba zai taba yin mamaki ba idan duk hare-haren da ake kawai Musulmi ne sike yinsu wadan da ake kira Boko Haram.

Addinin Musulunci ya yi tir da dukkanin wani aikin Ta'addanci da ya hada da kisan rayukan bayain Allah da basu san hawa ba, basu san sauka ba, yayi hani ga lalata dukiyoyin al'umma haka siddan. Dan haka, dan Musulunci ya yi hani ga aikata aikin Ta'addanci irin wanda Boko Haram suke aiwatarwa,, wannan ba shi ne zai sanya idonmu ya rufe har mu dinga ganin Musulmi ba zai iya yin abinda ke faruwa ba, dan haka dole idan an bigi jaki a bigi mangala. Amma ba zamu yi mamaki ba idan ance ana taka sawun barawo acikin al'amarin Boko Haram, wannan ce hikimar da Musulunci yace idan an san farkon Masifa to ba'a san karshenta ba, dan haka Allah ya la'anci dukkan masu tayar da ita.

Aganina zai zama tufka da warwara, idan aka ce Gwamnatin da ake zargi ita ce ke kai hare-haren da ake kaiwa Musulmi a Arewa da sunan Boko Haram, amma kuma ana zargin ta da gazawa wajen magance matsalolin tsaron! Tayaya gwamnatin da muke zargin tana kashe mu, kuma mu dinga kiran ta shawo kan al'amuran tsaro?  Babu shakka  Gwamnati ta gaza matukar gazawa wajen dakile ayyukan Ta'addanci irin wanda Boko Haram ke aiwatarwa, anyi sakaci mai girman gaske wajen tsare rayukan al'ummar kasa da dukiyoyinsu, hakki ne na wajibi akan hukuma da Allah ya dora mata alhakin tafiyar da al'amuran al'umma ta tsare musu jininsu da Mutuncinsu da Hankalinsu da dukiyoyinsu. Amma a nan hukumomin tsaro basa daukar irin matakin da ya dace wajen samar da cikakken tsaro ga al'ummar kasa da magance matsalar Boko Haram.

Zarge-zargen da ake yiwa Gwamnati na hannu a cikin abubuwan da ke faruwa, wannan ita ce zata kare kanta daga dukkan wani zargi mai tsuhe da mara tushe. Musamman tambayoyi irin, a ina Boko Haram suke samun kudi da Makamai? Ya aka yi batun ya kawo har yanzu bai zo karshe ba, duk kuwa da irin kudin da aka lafta a bangaren tsaro. Wani karin magana na Hausa da yake cewa KIFI NA GANINKA MAI JAR KOMA, a tunani na kamar fassara ne na irin abinda Boko Haram ke yi, domin karin maganar ba cewa ya yi Mai Jar Koma Yana Ganin Kifi ba; a har kullum shi mai laifi ko mai shirin aikata laifi, yana ganin hukuma amma ita hukuma bata ganinsa, dan haka kamar yadda Kifi yaga jar komar Masunci zai yi dukkan mai yuwuwa wajen zillewa fadawa cikinta, sai dai fa idan kaddara ta fada masa, to haka shima mai aikata laifi, kullum tunaninsa da basirarsa ita ce ya za ayi ya kaucewa fadawa komar hukumomi, dan haka ba zai zama abin mamaki ba a gareni idan ance wadannan masu aikata ta'addancin suna yin abinda suke yi ba tare da sun fada komar jami'an tsaro ba.

Ta bangarenmu kuma akwai sakaci mai girma daga jagororinmu da suka hada da Sarakuna da Masu Mulkin Siyasa da Kuma Malaman Addini da wadan da ke kiran kansu Shugabannin Arewa, domin tun farko ana ji ana gani Boko Haram suka dinga ikirarin abinda suke yi Musulunci suke karewa, kuma Shari'ah suke son aiwatarwa, amma kusan wadan da Mas'uliyyar ta ke a hannunsu suka ja baki suka tsuke, ko dai dan tsoron fushin Boko Haram ko dan ko inkula da sauransu, Allah ya jikan Sheikh Jaafar Mahmoud Adam da Sheikh Adam Albani da suka yiwa al'umma bayani akan wadannan miyagun mutane.

Har ila yau, bisa ga zato na Adalci da kyautatawa juna zato, babu yadda Gwamnatin tarayya zata dauki Makamai tana kashe jama'a a Arewa da sunan Boko Haram, amma Sarakuna da Masu Mukaman Siyasa suna ji suna gani su yi shiru ana kashe al'ummarsu ba su dauki mataki ba. Saninmu ne cewar Boko Haram sun kaiwa Shehun Borno hari, sun kaiwa Sarkin Fika hari, sun kaiwa Sarkin Dikwa hari, sun kaiwa Mai Martaba Sarkin Kano hari amma ace duk suna da masaniyar Gwamnati ce ke da alhakin abinda ke faruwa amma su ja baki su tsuke gwamnati na neman halaka su. Bana jin wani abu mai kama da haka zai iya faruwa.

Zan cigaba In Sha Allah.

YASIR RAMADAN GWALE 
13-05-2014

No comments:

Post a Comment