Sunday, May 11, 2014

Tsakanin Boko Haram Da Amerika Waye Abin Tsoro?

TSAKANIN AMERIKA DA BOKO HARAM WAYE ABIN TSORO?

Shekara da shekaru 'yan Boko Haram suna kashe mutanen da ba su san hawa ba basu san sauka ba, sun kashe mata, sun kashe maza, sun kashe tsoffi, sun kashe Malamai sun kashe dalibai, sun kashe da dama daga cikin al'umma babu sididi babu sadada akan laifin da jama'a basu aikata ba, aka kawo karshen rayuwarsu ba dan sun zabi hakan ba. sun kashe Musulmi a cikin masallatai kuma suna ikirarin Musulunci! Wannan wane irin musulunci ne haka! Bayan mun san cewa ko a yakin Fathu Makkah, Manzon Allah SAW cewa ya yi duk wani Mushriki da aka bi za'a kashe matukar ya shiga gidan Abu-Sufyan sarkin Makkah na lokacin to ya tsira! To ina ga jinin Musulmi a cikin Masallaci inda yake yin Munajati tsakaninsa da Allah Mahalicci?

Boko Haram sun sanya tsoro da firgici da razani da gigita a cikin zukatan dubban al'ummar da basu san laifin da suka yi ba, sun sanya da dama sun yi hijira sun bar garuruwansu na asalai ba dan suna so ba, sai domin ceton rai, sun tafi sun bar dukiyoyinsu da duk abinda suka mallaka ba dan sun yiwa kowa laifi ba. Sun kona dubban gidajen jama'a, sun bankawa kasuwannin da Musulmi suke neman abinci, sun bankawa Masallatai wuta! Subhanallah.

Boko Haram sun aikata dukkan dangin ta'addanci da zalunci da cin mutunci da cin zarafin dan Adam, kuma duk da haka suna ikirarin Addinin Musulunci suke karewa! Alhali tun daga surar Farko ta Al-Qur'ani har zuwa sura ta karshe babu inda Allah ya yi umarni da kisan ran da bai ji ba bai gani ba irin wanda Boko Haram suke yi. Duk wani Musulmi na gari yasan cewa dukkan aikin ta'addancin da Boko Haram suke aikatawa babu ko daya da ya yi kama da Musulunci, bil hasalima adadin Musulmin da suka rasa rayukansu ta sanadiyar Boko Haram ya ninka ninkim ba ninkim na adadin wadan da ba Musulmi ba da suka rasu ta sanadiyar Boko Haram.

Ciki da wajen Najeriya kowa na Allah wadai da ayyukan ta'addancin Boko Haram ko dai a sarari ko a fake. Addu'ar al'umma a koda yaushe ita ce Allah ya kawo karshen wannan zaman zullumi da razani da Boko Haram suka jefa al'umma ciki dare da rana, birni da kauye.

Zan cigaba In Sha Allah.

YASIR RAMADAN GWALE
09-05-2014

No comments:

Post a Comment