Friday, May 30, 2014

SHEIKH BALA LAU: Adalin Jagora Abin Koyi!

SHEIKH BALA LAU ABDULLAHI: Adalin Jagora Abin Koyi!

Tun bayan zamansa sabon Shugaban kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Bala Lau Abdullahi ya nuna shi shugaba ne mai dattako da tausayi da taimako da sauraren koke-koken al'ummar da yake jagoranta. Sheikh Bala Lau ba shi da bukatar a yiwa al'umma dogon ta'arifinsa, domin a bayyane yake ga duk wanda yake bibiyar ayyukan Kungiyar Izala ya san yadda Shugaban yake yin jagoranci abin misali wajen nuna kulawa da halin da al'umma ta ke ciki tare da nuna damuwa akan irin mawuyacin halin da ake ciki a kasa baki daya da bayanin hanyoyi na gaskiya da za'a kubutar da al'umma daga halin ni 'ya su.

Irin yadda Shugaba Sheikh Bala Lau yake nuna damuwa da halin da Talakawa da Marayu suke ciki na daga cikin irin Jagoranci abin koyi da Sheikh Bala Lau yake nunawa, kullum burinsa yaya al'umma zasu samu saukin rayuwa, dan haka bai taba gajiyawa ba wajen kutsa kai cikin talakawa musamman marayu dan ganin irin halin da suke ciki tare da yi musu goma ta arziki da share musu hawayen maraici da ya kwanranya a idanunsu.

Yana daga cikin irin kyakkyawan jagoranci abin Misali da Sheikh Bala Lau yake yi na kokarin hada kan Malaman Kasar nan Mabiya Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam wajen ganin an gudu tare an kuma tsira tare, an yi aiki tare wajen taimakawa al'umma dan rage musu radadin halin da suke ciki da kalamai na hikima.

Sheikh Bala Lau Abdullahi yana daga cikin sahun farko na Malaman da suke damuwa da irin halin da kasarnan ta ke ciki, kuma su gayawa Shugabanni gaskiya ba tare da shayi ko fargaba ba, a koda yaushe ya samu fursa ta haduwa da Shugabanni yana iyakar kokarinsa wajen ganin ya isar musu da sakon gaskiya tare da kira a garesu wajen sauke nauyin al'umma da yake kansu. Da dama daga wadan da suka san Sheikh Bala Lau sun shaideshi cewa Mutum ne mai kankan da kai mara girman kai bashi da kwadayi ballantana rowar abin hannunsa koda yaushe hannunsa a bude yake wajen tallafawa mabukata.

Hatta wadan ba Ahlussunnah ba Allah yana matsa bakinsu su fadi magana ta gaskiya akan Sheikh Bala Lau. Haka kuma, Sheikh Bala Lau yakan kai ziyarce ziyarce asobitoci domin duba halin da al'umma suke ciki tare da basu tallafi, ya isa abin misali, Sheikh Bala Lau shi ne kadai Shugaban wata kungiya ta Musulmi da ya kai ziyara babban asibitin kasa da ke Abuja dan jajantawa wadan da harin bom din Nyanya ya rutsa da su, ya kuma basu tallafi kamar yadda ya saba.

Yana daga cikin halin dattako irin na Sheikh Bala Lau girmama mutane da girmama ra'ayinsu, mutum ne da kofarsa a bude take wajen ganin ya saurari al'umma tare da karbar shawarwari daga garesu ba tare da wani jidali ba. Muna yi masa addu'ar Allah ya yi masa jagora a wannan Shugabanci abin misali da yake yi, Allah ya kare shi daga sharrin masu sharri, Allah ya haskaka masa hanya wajen bin dai-dai tare da aiki da gaskiya. Allah ya taimaki Sunnah da masu Da'awar kira zuwa ga Sunnah.

YASIR RAMADAN GWALE
30-05-2014

No comments:

Post a Comment