Thursday, May 22, 2014

Dangane Da Batun Sheikh Sunusi Khali Da Hamza Almustapha


DANGANE DA BATUN SHEIKH SUNUSI KHALIL DA HAMZA ALMUSTAPHA!!!

Jiya da na yi magana akan abinda ya faru tsakanin Sheikh Sunusi Khalil da Manjo Hamza Almustapha, na samu sa’kwanni da yawa, inda wasu da dama suke ganin tayaya zamu yiwa Malamin Sunnah wanda d’an uwanmu ne irin maganganun da suka gabata! Wasu sunyi maganganu masu muhimmanci wasu kuma sunyi shirme. Amma abinda na sani Adalci shi ne, dan Malamin Sunnah ya yi irin abinda Malam Khalili ya yi ba zamu dauke kai daga gareshi ba mu binne abin wai dan kada 'yan Shi'ah su gani su yayata mu ko su yi mana dariya.

A zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, wata mata daga cikin Musulmai ta yi sata a farko-farkon Musulunci, kuma kayan da ta sata na Bayahude ne, Sahabbai suka shiga cikin damuwa suna tattauna yadda za'a boye abin dan kada Yahudawa su gani su zargi Musulmi, dan gudun kada hakan ya sanya dari-dari ga masu shiga Musulunci a lokacin. Manzon Allah SAW har ya karkata zuwa ga ra'ayin Sahabbai na a rufawa matar Asiri kar a tona maganar dan kada Yahudawa su samu abin fada, Ta ke Allah Subhanahu Wata'ala ya saukar da ayar Al-Qur'ani yake umarni da yi wa duk wanda ya aikata laifin sata hukuncin haddin sata! Wannan ya kore dukkan wata kara dan Musulmi ya aikata wani aiki na ba dai dai ba a rufa abin a boye dan kada wasu su yi magana.

A lokacin da ake jihadi, sahabin Manzon Allah SAW Kahlid Ibn Walid, ya bi wani Muhsriki zai kashe shi, sai Mushrikin ya yi Kalmar Shahada, amma duk da haka Khalid ya fille wuyansa, da Manzon Allah ya samu labari baiyi wata-wata ba wajen barranta daga Abinda Khalid ya aikata, duk kuwa da cewa Khalid yana da tarin Alkhairai masu dumbin yawa dab a zasu lissafu ba a Musulunci amma Manzon Allah bai yi masa kara ba a matsayinsa na wanda ya fito Gwagwarmayar tabbatar da wanzuwar addinin Allah a ban kasa. Haka batun yake, idan muka koma kan Kissar su Ka’ab Bin Malik.

Duk wanda ya saurari kalaman Sheikh Sunusi Khalil akan irin maganganun da ya yi akan Almustapha zai tabbatar da cewar Malamin da gaske yake, domin ya yi rantsuwa da Allah cewa abinda ya fada dai-dai ne kuma gaskiya ne, har yake ikirarin wajen da aka zauna aka nakasha abinda yake ikirari, ya kuma kalubalanci duk wanda ke san sanin hakikanin abinda ya faru ya garzaya kotu dan shi Malamin ya baje kolin hujjoji, akan tuhumar da yake yiwa Almustapha na amfani da ake das hi dan cutar da al’ummar Musulmi.

Da muka ji cewar Almustapha yaje kotu munyi farinciki domin muna san ganin irin hujjijin da shi Malam Sunusi Khalil ya dogara garesu dan fayyacewa al’ummar Musulmi irin Makircin da aka hada baki da Almustapha wajen shirya mana. Haka kuma, ya zama kamar wajibi akansa ya bayyanawa al'umma wadannan hujjoji domin ya nuna cewa za'a cutar da Musulmi ne, tunda kuwa yana da masaniyar hakan wajibi ne ya bayyana dan kare rayuwar al'umma.

Tun da aka fara wannan Shari'ar wasu daga cikin Malaman Sunnah suka fahimci cewa lallai idan aka kai karshen yanke hukunci tabbas za'a ji kunya, dan haka aka yi ta rokon shi Manjo Hamza Amustpaha akan ya yi hakuri ya janye karar da ya kai kotu, Hamza Almustpha ya ce ba zai janye ba sai Kotu ta tabbatar da gaskiyar lamari akan batun, idan har an sameshi da laifin da malamin ya fada baya shakkar a yi masa dukkan hukuncin da Shari'ah ta tanadar, aka tursasawa Almustapha akan janye maganar a gaban kotu, a tattauna ta bayan fage dan warware batun, har daga bisani ya mika lamarin a hannun Sheikh Dr. Ahmad Gumi inda ya yi alkawarin biyayya ga dukkan matsayar da Gumi ya zo da ita akan batun. Dan haka dukkan wata tattaunawa akan wannan batu ta takaitu ne tsakanin shi Malam Sunusi Khalil da Dakta Ahmad Gumi, dan haka duk wanda y ace Sulhu aka yi, to ya fada dan ya gyara zancen domin zaman bad a Almustapha aka yi shi ba.

A bisa bincike da bayanan da suka fito yayin wannan tattaunawa, shi kansa Malam Khalil abinda ya fada din ba maganarsa bace, domin wasu ne suka yi amfani da shi tare da alkawarin bashi hujjojin da suke tattabatar da maganar, suka yi masa ingiza mai-kantu ruwa, amma da ya tashi yin jawabi sai yayi magana sabanin yadda ya samu labarin, su kuma wadan da suka ingiza shi yin maganar suka dare suka barshi. Har ta bayyana karara cewar abinda ya faru Kazafi ne aka yiwa shi Almustpha.

Wasu da dama suna batun cewar ai Malam kuskure ya yi, kuma ya gane kurensa dan haka ya janye maganarsa. Wanda ko kusa wannan ba a kiransa da kuskure, domin a jawaban Malam Sanusi Khalil Magana yake da karfin halin cewar yana da hujja akan abinda ya fada. Mu Ahlus-Sunnah ne, Muna da yakini akan cewa babu wanda baya yin kuskure, hasalima shi ne cikar Dan-Adamtaka mu kasance masu aikata kuskure, da saninmu ko babu sani, amma abinda Sheikh Khalil ya yi ganganci ne, haka kuma, duk wanda yake bibiyar Da’awar Sunnah irin wadda Sheikh Sunusi Khalil yake yi, Da’awa ce mai cike da abubuwan tuhuma, dan Malamin ya cika mafiya yawancin maganganunsa da kalamai na Rantsuwa da Tsinuwa, ya ambaci shigabanni ya tsine musu yace kowa yace Ameen, wanda yaki cewa Ameen shima Allah ya tsine masa! Wannan duk wanda yake bibiyar karatuttukansa haka yake fada, kuma wannan ya sabawa koyarwar Sunnah.

Yanzu dan Allah, da wane irin ido Sheikh Sunusi Khalil zai kalli Hamza Almustapha a matsayin wanda ya gina maganganu akansa wanda ba gaskiya bane? Yaya Hamza Almustapha zai dinga kallon shi Sheikh Sunusi Khalil a nan gaba? Kamar yadda na fada, babu wani Malami wanda yake Ma’asumi da baya kuskure kowa na yi, amma na Sheikh Sunusi Khalil ganganci ne ba kuskure ba, domin ikirari ya yi ya kuma cika shi da rantsuwa da Allah mahalicci. Duk da ya bayyanawa duniya cewar dukkan bayanan da ya yi akan Hamza Almustapha din ba gaskiya bane, dole abin ya yi mana ciwo mu shiga cikin damuwa, akan irin abinda ya faru.

Tabbas wannan al’amari zai bude wani sabon babi akan dukkan wasu maganganu da malamai zasu dinga yi musamman ga ‘yan siyasa. Fatana Allah ya kare malamai daga gurfana a gaban kotu dankare irin maganganun da suka yi watakila bisa kuskure. Allah ya shiryemu shirin Addini ya nuna mana gaskiya mu fahimce ta ya kuma bamu ikon aiki da ita ko daga wa ta ke.

Yasir Ramadan Gwale
16-05-2014

No comments:

Post a Comment