Thursday, May 29, 2014

RANAR DIMOKARADIYYA: Gwamnan Jigawa Sule Lamido Ya Ciri tuta


RANAR DIMOKARADIYYA: Gwamnan Jigawa Sule Lamido Ya Ciri Tuta

A yau 29 ga watan mayu da ake bikin ranar da mulki ya koma hannun farar hula a karo na 15. Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya tserewa sa'a a yayin wannan biki. Ba shakka dole na yi yabo da jinjina ga Gwamnan Talakawa Alh. Sule Lamido bisa irin yadda ya nuna cewa inganta rayuwar Matasa da al'umma shi ne burinsa, da yawan takwarorinsa Gwamnoni sun mayar da hankali akan batutuwa da suka shafi siyasa a wannan rana, amma shi a nasa bangaren Gwamna Sule Lamido masana da manazarta ya gayyato irinsu Alh. Abdulkadir Balarabe Musa da Farfesa Ahmad Dandatti Abdulkadir da Barr. Solomon Dalung ya kirawo domin su tattauna su bada hasken yadda za'a inganta rayuwar matasa. Ba shakka irin wannan halin kishin Talakawa da Sule Lamido yake nunawa firi-falo haka ya kamata dukkan shugabanni su siffanta da shi. Gwamna Lamido ya ciri tuta a wannan janibi.

Bana mantawa a bara ma a irin wannan rana, gwamna Lamido ya gayyato masana tattalin arziki zuwa Dutse jihar Jigawa domin tattauna yadda za'a bunkasa tattalin arzikin Jihar Jigawa sabuwar Duniya. Wannan abin a yabawa Gwamna Lamido ne akan irin kokarinsa na ciyar da rayuwar Talakawansa gaba. Haka nan kuma, bana mantawa Gwamna Lamido a lokacin da ya zama Gwamna a zangon farko a irin wannan rana ya kirawo taron Talakawa wanda ya sanyawa sunan TALAKAWA SUMMIT inda Gwamnan ya tattauna da Talakawa kai tsaye babu shamaki tsakaninsu, inda suka bashi shawarwari kuma suka yi korafe-korafe a gareshi. Irin wannan salon Shugabanci da Gwamna Sule Lamido yake yi wanda kadan ne daga cikin irin kayan gadon da marigayi Malam Aminu Kano ya barwa 'yan baya, shi ne abinda muke fatan dukkan shugabanninmu su mayar da hankali akai.

Shugabanni su ji tsoron Allah, su zauna su kallai rayuwar Talakawan da suke shugabanta, me aka gabatar musu wanda zai dadada ya kuma saukaka rayuwar al'umma, a kuma yi Nazarin halin da al'umma ta ke ciki domin samar mata da mafita sahihiya.

Daga karshe ina kara nuna jinjina da yabawa ga Gwamna Sule Lamido akan irin wannan manufa tasa ta nuna kishin al'ummar da suka zabe shi, ina kuma kira ga sauran Gwamnoni Makwabta da su yi koyi da Gwamnan jihar Jigawa Alh. Sule Lamido wajen shirya taruka irin wadannan da ake gudanarwa a Jigawa a irin wannan rana. Ina kuma taya Gwamna Lamido murnar cika shekaru 7 kan kujerar Gwamnan Jigawa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin al'umma lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
29-05-2014

No comments:

Post a Comment