Thursday, May 29, 2014

NAJERIYA: Aikin Kamfani Ko Aikin Bauta?

A Najeriya dokar kasa ta ce duk wasu da zasu kafa kamfani a wani waje a fadin tarayyar Nigeria dole ne su dauki Personnel Manager dan asalain wajen da aka kafa kamfanin. Personnel manager shi ne zuciyar kamfani, amma a KANO dukkan wani kamfani da yake aiki na 'yan China da indiyawa da kwarori da na Sadarwa babu wani kamfani da aka dauki Personnel manager dan asalain jihar kano. Ba komai ya janyo haka ba sai CIN-HANCI duk masu kafa kamfani sun san da wannan doka, amma sun bayar da cin-hanci ga manyan gari an dauke kai daga kansu suna yin abinda suka ga dama. Kaje dukkan wani kamfani da yake aiki a Chalawa/Panshekara, Sharada, Dakata, Bompai kaga yadda ake cin zarafin al'ummar jihar Kano, kwara ko dan china ya fellawa ma'aikaci dan Kano mari akan laifin da bai kai ya kawo ba kuma ya mari banza babu abinda za'a yi sai dai ma'aikacin ya yi kukansa ya yi Allah Ya isa!

Da yawan ma'aikatun 'yan Indiya da kwarori da 'yan Chana suna hana ma'aikatansu zuwa Sallar juma'a, Sallar azahar da la'asar da magriba da Isha kuwa lokaci suke bayarwa duk wanda ya d'ara ana dandana masa kudarsa ko a zaftare a cikin albashinsa da bai taka kara ya karya ba. Wannan fa duk yana faruwa ne karkashin igiyar 'YANCI da muke da ita a kasarmu da mutanenmu suke shugabantarmu ba Bature farar fata ba. Duk wani ma'aikacin Kamfani ko wanda ya taba yin aikin kamfani musamman a Kano yasan da wannan dama wasu al'amura masu muni.

Sannan kuma, da yawa damar samun gurbin aikin da muke da ita a matsayinmu na 'yan Asalain jihar Kano raba dai-dai muke yi tsakaninmu da mutanan Kudancin Kaduna da Arnan Jos da Katafawa da sauransu. Mun zama masu matacciyar zuciya cima zaune, abubuwan da ya kamata mu ci gajiyarsu mun bari wasu daga nesa sun cin moriyarsu. kaje duk wasu Kamfanunuwa da Bankuna masu hada-hada yau da kullum kai ka ce ba a kano yake ba, domin tun daga kan masu Gadi wadan da sune koma baya a cikin ma'aikata zaka fahimci irin yadda aka kwashe mana kafafu! Kai ba kamfanoni ba hatta wasu daga cikin Ma'aikatu har da na Gwamnati zaka taras da Mai Gadi ba Bahaushe bane balle kayi maganar mutumin Kano.

Mun taba yunkurin kawo dauki akan wani kamfanin sadarwa da ya dinga binne wayoyinsa a kasa, danganin al'ummarmu sun ci moriyar abin cikin wadan da aka yi wannan yunkuri da su har da Dakta Aliyu Jibia, amma abinda aka sanar mana shi ne jefa rayuwarmu zamu yi cikin hatsari idan har muka dage sai anyi gyara akan haka. Gyara ba zai taba yuwuwa ba a Najeriya sai an yaki CIN-HANCI bilhakki da gaske a dukkan fannoni.

YASIR RAMADAN GWALE
29-05-2014

No comments:

Post a Comment