Monday, November 18, 2013

Shin Jega Ne Matsalar Zaben Najeriya?

SHIN JEGA NE MATSALAR ZABEN NAJERIYA?

Zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar ranar 16 ga watan nuwamba, kusan shi ne ya bankada asirin hukumar zabe ta kasa karkashin jagorancin kwararren malamin jami’ah masanin kuma mutafannini a harkar siyasa Farfesa Attahiru Muhammad Jega, dan gane da kurari da karajin da ya dinga yi a baya cewa ya nazarci dukkan kurakuran da suka fuskanta a zaben 2011 da ya gabata, ya kuma sha cin alwashin cewar sai ya tsaya kai da fata wajen ganin an aiwatar da sahihi kuma tsarkakken zabe daga dukkan nau’in magudi a babban zaben kasa na 2015 da ake ta tsumayin lokacin. Sai dai Hausawa sunce “juma’ar da zatai kyau akan fara gane ta ne tun daga asubahin ranar laraba” sai gashi abin mamaki da ta’ajibi laraba ta yi har rana ta fadi ana shirin wayar gari Al-hamis babu wasu alamu da suke nuna cewar juma’ar da zata zo gaba kyakykyawa ce da jama’a zasui murna da farin ciki da ita.

Wannan zaben na Anambra da aka gudanar mai cike da kace-na-ce da tababa, shi ne zaben da ‘yan Najeriya suka sanyawa ido a matsayin wani ma’auni ko zakaran gwajin dafi akan zaben da zai gudana na kasa a shekarar 2015. Sai gashi duniya ta shaida tsiraicin hukumar zaben da Jega ya dinga shan alwashi akan zasu aiwatar da sahihin zabe. Almundahanar da aka tafka a wannan zaben ba wai ta tsaya akan al’adar nan ta ‘yan siyasa ta sayan kuri’u da rarraba kayan masarufi ga masu yin zabe ba, abin har da jami’an hukumar zabe aka samu da hannu dumu-dumu wajen yin kaci-baka-ci-ba baka-ci-ba-kaci, aka raunana zaben, aka hana wasu yin zabe, aka sossoke wasu kuri’u. Na san da cewa da daman ‘yan Najeriya abin da ya faru a Anambra dangane da ‘yan siyasa bai basu mamaki ba, dan dama mai hali baya fasa halinsa, illa kawai abin mamaki shi ne, ashe hukumar zabe shararata ta dinga yi dangane da wannan zabe.

Ba shakka, ya zuwa yanzu mutane da dama sun sallama da samun sahihin zaben da aka tsammata a 2015 wanda Jegan ya sha alwashin aiwatarwa. Dukkan wani kyautatawa hukumar zabe zato da aka yi akan zaben 2015 a yanzu dai hukumar zaben ta zubewa ‘yan Najeriya kasa warwas idan banda ‘yan Fidifi bangaren shugaban kasa. Babu wani kwarin guiwa da muke da shi akan hukumar zabe dangane da samun sahihin zabe da zamu iya aminta da sakamakonsa. Abinda ya faru a baya watakila a zaben 2015 ya ninka ninkim-ba-ninkim na almundahana da cuwa-cuwa da satar akwati da hadin baki tsakanin jami’an tsaro da ma’aikatan hukumar zabe da baragurbin ‘yan siyasa masu san cin zabe ta kowace irin hanya.

To amma abin tambaya anan shi ne, shin Farfesa Attahiru Jega shi ne matsalar zaben Najeriya? Ba shakka Jega shi ne shugaban hukumar zabe ta kasa, shi ne yake da dukkan wani alhaki na ganin ya tsaya kai da fata wajen ganin anyi gaskiya, anyi adalci a matsayinsa na shugaban hukumar zabe. Sauran jama’a masu zabe su kuma a nasu bangaren su tabbata sunyi zaben gaskiya wanda bai sabawa doka da ka’ida ba.

Tuni har wasu sun fara yin kira akan Farfesa Attahiru Jega ya kama gabansa ya san nayi. A ganina yin murabus din Jega ba shi ne mafita ba dangane da samun sahihin zabe, ba shakka Shugaban hukumar zabe yana da dama mai girman gaske wajen ganin anyi zaben gaskiya, amma yana da kyau idan anbugi jaki a bugi taiki, domin su kansu jama’a da dama ba gaskiya suke da itaba, dole mu hada karfi da karfe wajen ganin ansamu zaben gaskiya. Yana da kyau mu sani ko Jega ya sauka, Shugaban kasa Me-Malafa shi ne dai zai sake nada sabon shugaban hukumar zabe, kuma ba shakka, shugaban rashin gaskiyarsa da rashin tsoron Allahnsa sun bayyana karara kamar wata darn goma sha hudu, dan haka ba zai taba nada wani mutum mai gaskiya da zai jagoranci hukumar zabe dan ya aiwatar da sahihin zabe ba.

A ganina gara Jega ya cigaba da zama a matsayin shugaban hukumar zabe har zuwa karshen wa’adinsa, tunda mun riga mun sanshi, munga irin kamun ludayinsa. Muna kuma da yakinin cewar yayi Imani da Allah, ya yi Imani da Wutar Jahannama ya yi imani da Al-Jannah, ya kuma san cewa Marasa gaskiya maciya amana masu jefa rayuwar al’umma cikin mummuna hali da garari ba zasu hada hanya da al-jannah ba. Wallahi Jega idan yayi gaskiya yasan makomarsa kyakykyawa ce a ranar gobe kiyama, idan kuma yayi rashin gaskiyar da muke zarginsa ba shakka yasan makoma ta munana ga mutanan da suka aikata aiki irin na marasa gaskiya makiya gaskiya, makiya cigaban kasa.

Ko shakka babu, bamu yanke tsammani daga wajen Allah ba dan samun Shugabanni na gari masu gaskiya da tsoron Allah wadan da zasu ji-kanmu su fitar da mu daga cikin halin fatara da talauci da kuncin rayuwa, da samar mana da dukkanin abubuwan bukata, da kare mana martabarmu da rayukanmu da dukiyoyinmu. Allah muke roko Al-Azizu ya wargaza dukkan wani shiri da nufi na Azzalumai ko su waye, Ya Allah kasansu ka san abinda suke kullawa, Allah ka yi mana maganinsu. Ya Allah! Bad an halinmu ba, ka arzutamu da samun shugabanni na gari Adalai.

Yasir Ramadan Gwale

18-11-2013

No comments:

Post a Comment