Tuesday, April 9, 2013

MU KEWAYA DUNIYA

MU KEWAYA DUNIYA

Assalamu Alaikum, Ina fatan 'yan uwana Gizagawa suna nan cikin koshin lafiya, haka kuma ina fatan za a yi min afuear kutsen da shirin yayi ba akan lokacin da ya kama ta zo ba, wannan kuwa ya faru ne sakamakon wasu dalilai, da fatan za'a gafarceni.

Yau insha Allah zamau yi bayani ne akan wata kasa da Nasan da yawan mutane basu san da ita ba, wasu ma ina zatan basu taba jin sunanta ba. Amma ko kun san da cewa akwai Kasar Turai da babu Jami'a (University) ko daya a cikinta? To ku karkade kunnanku ku sha labari. Domin yau zamu danna can cikin tsakiyar kasashen Turai ne, kuma zamu isa zuwa wata 'yar karamar kasa amma kuma babbar kasa ta fuskoki da yawa.

Wannan kasa sunanta LIECHTENSTEIN ko kuma Likstantain da Hausa. Ita dai wannan kasa tana a tsakiyar kasashen turai ne, sannan tayi iyaka ne da kasashe guda biyu kacal, wato tayi iyaka da kasar Switzerland daga yankin kudu da yamma, sannan kuma tayi iyaka da kasar Austria daga yankin Arewa da kuma Gabas. ita dai wannan kasa 'yar kara mace kwarai da gaske ta fuskar yawan jama'a, domin gabaki dayan mutanan kasar su 36,000 ne kwata-kwata, wato idan zan kwatanta ta da mazabar Gwale dake karamar hukumar Gwale sai nace mazabar Gwale ta ninka wannan kasa yawa sau biyu. Tabdi jan!

Haka kuma, kasar tana a fadin kafa 160 murabba'i. Babban birnin kasar sunansa VANDUZ, sannan kasar tana da larduna ne guda shida. Sannan, ta fannin tsarin shugabanci kasar tana da Sarki ne irin na gargajiya wanda ake gada, amma kuma suna da majalisar dokoki waan a sune suke tsarawa kasar dokoki kuma zabarsu ake yi duk bayan shekaru hudu.

Wannan kasa itace kasar da tafi kowacce kasa karancin Bashi a duniya. Haka kuma tana daga cikin kasashen da tattalin arzikinsu yake da karfi sosai, domin ta fuskar masana'antu yawan kamfanonin dake kasar sun haura yawan al'ummar kasar, gwarigwari zamu iya fahimtar cewa duk dan kasar ba zai rasa aikin yi ba kenan.

Ta fuskar addini kuma Musulmi suna da kashi 4.8 na adadin al'ummar kasar, kiristoci mabiya darikar Katolika sune suke da kashi 78.4, sannan kiristocin Reformed Church suke da kashi 7.9. Musulmi sune suke da matsayi na uku.

Idan kuma muka koma ta fuskar al'adun mutanan kasar. Kasancewarsu basu da yawa, wannan ya sanya al'adun kasashen da ke kewaye da su ya mamaye kasar. Da kuma al'adun kasar Jamus, domin yaren kasar shine Jamusanci. Dan haka mutanan kasar suna da sha'awar kide-kide irin na gargajiyar turawa da kuma wasan kwaikwayo. Haka kuma kasar tana da gidan tarihi kasaitacce da ake kira Kunstmuseum Liechtenstein, dan yana daga cikin abinda yake samarwa da kasar kudin shiga. Mutanan kasar dai sun dogara ne da irin yanayinsu mai dadi na lambuna da shuke-shuke da duwatsu masu tuntsuro da ruwa daga sama wajen samun kudin shiga, manazarta sunce wannan kasa tana daga cikin kasashen da sukafi yanayi mai dadi a duniya, wannan ce ta sanya mutane da yawa musamman Turawa suke zuwa kasar yawan bude Ido da kuma shakatawa.

Ta fannin tsaro kuma, wannan kasar itace kasa mafi karancin aikata laifuffuka domin akwai gidajan yari da ko tsuntsu babu a daure da sunan ya aikata laifi. Sannan a cikin shekara guda ne kacal ake samun mutum guda ya aikata laifin da za'a iya daureshi. Abinda ya sawwaka kenan a shirinmu na wannan makon sai kuma mako mai zuwa inda zamu sake Nausawa zuwa wata kasar.

Amadadin wanda ya sadani da ku Abubakar Idris FCT, Ni Yasir Ramadan Gwale da na shirya na gabatar nake cewa Wassalamu Alaikum.

No comments:

Post a Comment