Sunday, April 7, 2013

KUSKURE NE AFUWA GA BOKO HARAM


KUSKURE NE AFUWA GA BOKO HARAM
 
Sai bayana da al'amura suka rincabe a yankin Arewa baki daya aka kai Arewa kasa ta fuskar tattalin arziki da tsaro da zaman lafiya, sannan idon shugabannin Arewa ya bude, suke ta kiran WAI a yiwa wadannan mutane wanda duk 'yan Najeriya sun amince, cewa 'yan ta'addane ahuwa. Mutanan da suka dauki makamai da bama-bamai suke kashe mutane, babu ji babu gani, sun kashe Sojoji sun kashe 'yan siyasa sun kashe Malam Addini, sun kashe Musulmi sun kashe Kirista, da manyan masu rike da mukamai, daman talakawa ba'a maganarsu. Ankashe talakawan da Allah ne kadai yasan adadinsu a Jihohin da wannan lamari yayi kamari.

Tun bayan bayan dubban mutanan da aka kashe a 2009 a jihar Borno da sunan kodai ana zarginsu da cewa 'yan Boko Haram ne ko kuma wadan da 'yan Boko Haram din da kansu suka kashe 'rana zafi, inuwa kuna' al'amura suka rincabe a kusan baki dayan babban birnin Maiduguri na jihar barno da wasu sassan jihar. Haka kuma, gwamnatin tarayya da sunan farautar wadannan tsageru marasa tsoron Allah 'yan ta'adda da ake kira Boko Haram, ta kawo sojojin hadin guiwa dan suyi aikin tsaro a jihar ta Borno wanda al'amarin maimakon ya gyaru sai ya sake kazancewa inda babu wanda ake cuta a wannan al'amari sai talakawa bayin Allah, domin su wadancan mutane 'yan ta'adda sun kashe, sannan suma sojoji sun kashe. Abin har ya tsallaka makociyar jihar Yobe nan ma ya kusa durkusar da jihar ko ma ya durkusar da Birnin Damaturu gaba daya.

Tafi-tafi abin ya bar yankin da ake ganin nanne inda wadannan mutane suka yi kaka-gida ya tsallako jihohin Kano da kaduna da sauran jihohin Arewa maso yamma. Wadannan mutane sun kashe daruruwan bayin Allah a jihohin nan, mutanan da basu san hawa ba basu san sauka ba. Jama'a suka shiga tsaka mai wuya da tsananin firgici da damuwa da tsoro da tashin hankali, ga tsanantawar jami'an tsaro ga tashin hankalin 'yan ta'adda.

Abin da yake daurewa kowa kai shine yadda ake samun musayar harbe-harben bindgogi a duk lokacin da aka ce ga wani bom ya tashi. lamarin akwai daure kai ainun domin dole mu tambaya, shin su waye suke wadannan harbe-harbe, da zarar Bom ya tarwatse? shin su 'yan ta'addan ne suke yi ko kuwa jami'an tsaro ne? Haka nan abin yake wucewa baka jin kadin abin. 'Yan ta'add 'yan Boko Haram sun kashe, jami'an tsaro sun kashe jama'a na cikin wahala kiraye-kirayen samun zaman lafiya ya fara yawaita a Arewa, sannan sarakuna da wasu dattabai suka fara kiran anemo bakin zaren warware wannan al'amari.

Dattawa daga Arewa suna kiran a yiwa wadannan 'yan ta'adda ahuwa! Abin ko dadin ji babu! Shakka babu lamarin akwai daure kai ta yadda idan wasu a Arewa ya rufe cewa lallai sai anyiwa wadannan mutane Afuwa! Ai abinda ya kamata suyi shine su matsawa gwamnati lallai ta samar da cikakken tsaro ga al'umma, tunda hakkinta ne kare 'yan kasa ta hanyar da baza a tsanantawa mutane ba. Babu yadda za'a ce gwamnati ko hukumomin tsaro sun kasa sanin yadda al'amarin yake, domin me ya sanya a Arewa ne kadai wadannan tashe-tashen hankula ke faruwa? Me ya sanya ba'ayi a kudancin kasarnan? Ya aka yi hukumomi suka iya samar da cikakken tsaro a yankin kudu amma suka kasa samarwa a Arewa? Wadannan da ma wasu shine abinda su wadannan dattawa na Arewa ya kamata su tambayi gwamnatin tarayya, dan sanin yadda aka yi aka haihu a rugga. Dole a bibiyi wannan idan har gaskiya muke so, ba rufar kura da fatar akuya ba.

Shi kansa shugaban kasa ya rude akan wannan al'amari, yana ta kwan-gaba kwan-baya. Abin da yake nuna cewa su kansu hukumomin suna da masaniyar yadda akayi wadannan abubuwa suke faruwa. Ya zama dole a yiwa al'ummar kasa jawabin yadda aka yi aka kasa magance wannan al'amri na tsaro, shin matsalar daga ina take?  Shin gazawar hukumomin tsaro ne? ko kuwa abin ne yafi karfinsu gobara daga kogi! Lallai akwai bukatar a yiwa al'ummar kasa bayanin yadda akayi aka kawo har ya zuwa wannan lokaci ba tare da cin karfin al'amuran tsaro ba.

Sannan a rahotannin da suke biyo bayan ziyarar da dattawa daga Arewa suka kai fadar shugaban kasa dan yin kira gareshi yayi wa wadannnan 'yan ta'adda miyagu azzalumai ahuwa, ance shugaban kasa ya kafa kwamitin da zai tsara yadda wannan ahuwa zata kasance. Nayi Imani muddin aka yi wannan ahuwa to gwamnati da kanta ta yiwa kanta kirari a kofar kasuwa kuma ta dabawa kanta wuka. Domin daga bayanan da muke ji ance su wadannan 'yan ta'adda masu kashe mutane da ransu za'a basu wasu maqudan kudade da samar musu da manyan gidaje irin na alfarma, ban sani ba ko wannan al'amari gaskiya ne.

Tabbas idan haka ta kasance wadannan mutane sun kashe banza, sunci bulus, anyi musu afuwa gobe kuma Allah ne kadai ya san irin kungiyoyin da zasu sake barkowa suna kashe duk mutumin da bai yi musu ba, ko kuma ya saba da aqidar da suke akai, musamman mun san akwai masu mafarkin yin juyin juya halin da zai basu damar kifar da gwamnati su kafa irin wadda suke so, kuma su kashe wanda suka ga dama, shakka babu yin wannan ahuwa bude babbar kofa ce ta barna da Allah ne kadai ya san iyakar adadin rayukan da zasu salwanta ta sanadiyar wannan ahuwa. Domin tun lokacin da aka fara kiran sasantawa da wadannan miyagu 'yan Boko Haram aka samu bullar wata kungiya Ansarul Muslimeen Fi biladis Sudan, wannan shine irin misalin da yake nuna barkowar irin wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda a nan gaba. Wannan alamace da take nuna cewa wani babban bala'in da yafi na Boko Haram yana tunkaro kasarnan a shekaru masu zuwa nan gaba! Allah ya kiyaye.

Dan haka dole, gwamnati ko dai ta janye wannan batu na ahuwa ta kame wadannan tsageru miyagu azzalumai 'yan ta'adda ta hukuntasu daidai da abinda suka aikata ko kuma, ko kuma dukkan mutanan da wannan al'amari ya taba shafa ko ya rutsa da su a biyasu diyya, sannan  kuma wadan da suka rasa rayukansu ta sanadiyar wadannan mutane a biya iyalansu diyyar rayukansu, domin babu yadda za'ayi mutane su dauki makamai suna kisa babu kakkautawa kuma ayi musu ahuwa a basu kudade, sannan ace kuje babu komai. Tab! Sannan ace shi kuma mutumin da abin ya shafa bai san hawa ba bai san sauka ba ambarshi haka, hannu rabbana, idan ba haka ba kuwa Gwamnati zata dauki alhakin dukkan wasu bala'o'i da suke tun karo kasarar nan a nan gaba Allah ya kiyaye.
Sannan ya zama dole hukumomin da abin ya shafa su fito da cikakku kuma gamsassun bayanan su waye wadannan mutane? A ina suke samun kudade? Su wanene suke taimaka musu a gida ko a kasashen waje, idan ba haka ba kuma zargin da aka jima ana yi na cewa Gwamnati itace kanwa uwargami dangane da wannan al'amari.

Daga karshe ina mai rokon Allah ya jikan wadan da suka rasa rayukansu ta sanadiyar wannan al'amari wadan da basu yiwa kowa laifi ba, Allah ka yafe musu kura-kuransu. Su kuma wadannan 'yan ta'adda, Ya Allah kada ka basu zaman lafiya duniya da lahira, Ya Allah ka hadasu da dukkan dangin masifa da bala'i a duniya da lahira. Ya Allah ka nuna musu kurakuransu tun anan Duniya. Ya Allah kaine gatanmu, Ya Allah bamu da kowa sai kai YA ALLAH.

Yasir Ramadan Gwale
P.O.Box 2145
Kano.

No comments:

Post a Comment