Tuesday, April 30, 2013

BARAWON JARABAWA MA BARAWO NE


BARAWON JARABAWA MA BARAWO NE

A karshen makon da ya gabata, dalibai da dama ne suka rubuta Jarabawar UTME ko JAMB. Kusan bayanai sunce dalibai sama da miliyan da rabi ne suka rubuta jarabawar, Amma abinda ya bani mamaki irin yadda naga wasu da hankalinsu suka dinga bayar da satar amsa firi palo ko kunya basa ji, wani har kuri yake yi, wai shi ya taimakawa masu jarabawa! Shin yanzu da satar jarabawa za'a shiga jami'ah sannan kuma ayi abin kirki? Lallai abin akwai daure kai da tashin hankali, musamman idan muka yi hasashen makomarmu a nan gaba. Wadannan barayin jarabawa sune fa nan gaba zasu zama shugabanni, idan har zasu yi satar jarabawa akwai tabbacin idan suka ga dukiyar al'umma baza su sata ba?

Ilimi shine gishirin rayuwa, duk al'ummar da bata da masu "Ingantaccen Ilimi" tana cikin babbar matsala. Domin duk shekara makarantun gaba da sakandare zasu yi ta yaye jahilan dalibai a matsayin wadan da suka kammala karatu. Alabashshi daga baya su shiga siyasa duk su rikata al'amura su hana kasar tafiya yadda ta kamata. Naji wani daga cikin masu bayar da satar jarabawar yana ikirarin cewa "Ai kawai a sata idan an shiga Jam'iah komai zai ware" Haka naga wani ya fada! Tayaya komai zai ware tare da kayan sata? Da idona wani lokaci a baya naga wani Malamin Jami'ah yana sayar da Takardar Jarabar "post UME" abin ya dauremin kai matuqa, yadda malamin Jami'ah zai daurewa satar Jarabawa Gindi.

Lallai 'yan uwana dalibai da matasa sai an zage dantse anyi karatu. Idan ba haka ba kuwa za'ayi da nasani mara amfani, da yawanmu muna ta bata lokaci a facebook da sauran shafuka bayan ga abubuwa masu muhimmanci a gaba amma ba'a kula su ba. Lallai ne duk dalibin da yake son ganin ya fito da kyakykyawan sakamako sai ya dage yayi karatu da gaske ba da wasa ba, kuma ba da dogaro da satar jarabawa ba.

Yanzu ba dole nan gaba gine-gine suyi ta ruftawa da mutane ba, saboda Injiniyoyin da sukayi aikin mafiya yawancinsu barayin jarabawa ne ba kwararru bane. Likitoci suyi ta yanka mutane suna kashesu. Abin akwai ban tsoro matuka idan muka tuna makomar masu zuwa nan gaba. Domin al'amarin kullum kara tabarbarewa yake yi, Ingancin Ilimi yana kara yin kasa. Ana ta samar da dubgaggun malaman Firamare da sakandare da sauransu.

Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale
30-04-2013

1 comment:

  1. Amin, wannan mu'kala tayi duk da idan mukai la'akari da yadda tsarin karatun 'kasar nan yake kai kace an nemi 'Dalibai da suyi satar jarabawa ne, saboda tsarin koyarwar ya sa'ba da tsarin sauran 'kasashe da suka cigaba, yadda ake tsauwalawa ga 'Dalibi abu ne mai matu'kar wahala ace kowa ne yaro yayi irin wannan 'ko'karin duk da nasan wad'ansu zasu iya. Ana neman creadit biyar ciki har da turanci da lissafi bayan ka kawo hakan to aiki bai 'kare ba, sai ka zana Jarabawar JAMB ita ma a'kalla kaci 180 wad'ansu Jami'oin kanma sa 200, kuma du ace sai ka zauna Post UME. Idan kai dubi da karatun 'kasashen waje zakaga ba'a wahalar da 'Dalibi har haka kuma ko su shugabanni da Doktoci da furofasoshi da lauyoyi da muke da su a yau ba haka su kai nasu karatun ba, wad'an sun su da (Pass-Pass) suka je kai! Wad'an su kan ma da (mock) ne. Sa'banin na yanzu da suke ganin koda sun dage da karatun ba zasu kawo wad'annan tarkace da ake bu'kata ba, gara ma su shanta'ke sui sata kawai.

    Da za'a rage abinda ake nema ga 'Dalibai da hakan ya rage satar Jarabawa.

    ReplyDelete