Friday, April 19, 2013

KAICO! INA MA BAN AIKATA BA!!!




KAICO! INA MA BAN AIKATA BA!!!

Wata rana ana shagalin bikin Kuluwa a shekarar aluf da dari tara da tasa'in da uku (1993) an gayyato Dan-Asabe me kalangu yana ta casheeewa abinsa yana ta kida 'yan mata na ta tikar rawa, samari kuwa sai shewa suke ana tafi wasu ma har da yin fito gami da buga kafafu a kasa dan nuna irin yadda suke gangwajewa a wajen bikin kuluwa, ana cikin haka sai ga Jimmai nan ta taho, kan kace kwabo ta shigo filin kalangu ta fara gantarewa, ji kake wajen nan ya rude da sowwa da hayaniya, nan fa kallo ya koma sama, domin hatta 'yan matan da suke rawa suna cashewa sai da suka tsaya kallon yadda Jimmai ke cashewa. Me kalangu kuwa ya karkata hula ya kunna taba ya saka ta a gefen baki ya fara kadawa Jimmar "saba-da saba da, ga zomo ya fito zai koma . . ." Jama'a kuwa sai sowwa suke ana ta tafi daga bangaren samari wasu 'yan matan kuwa har guda suke yi, domin Jimmai dai ta biya kowa a wajen nan dan ta girgiza iyakar girgizawa gaba da baya ko ina ya motsa, filin nan ya dare kwal Jimmai ce kadai ke cashew abinta, ta daura wani dan-kwali ruwan makuba a kugunta sai juyi take abinta. Haka dai aka yi ta kidan kalangu har magriba tayi, kowa kuwa sai labarin Jimmai yake domin tayi rawa irin wadda samari suke son gani danko ina ya motsa a jikinta, abin sai wanda ya gani. Haka dai aka waste daga wajen bikin Kuluwa ana ta labain irin rawar da Jimmai ta ringa yi babu ko kunya.

Ana nan ana nan, bayan shekara baya da bikin Kuluwa aka daurawa Jimmai aure a shekarar 1994. Haka, suna nan zaune da mijinta har Allah ya basu Albarkar aure suka hayayyafa. Kwatsam wata rana a cikin shekarar 2012 Jimmai da 'yart budurwa mai kimanin Shekaru 17 suka je wata unguwa gidan kawarta, abin mamaki suna zuwa sai suka tarar ana kallon kasset din bikin Kuluwa da akayi a shekarar 1993, ga mai daukar hoto ya hasko Jimmai tana ta cashewa abinta, a lokacin Nan jimmai tana gani sai ta tuno abubuwan da suka faru, gata nan an nuno ta tana rawa tana girgiza jama'a na ihu! Jimmai ta gani kuma diyarta ma ta gani, abin da ya fito dga bakin Jimmai shine KAICO! INA MA BAN AIKATA HAKA BA. Wato a lokacin kwata-kwata bata ganin aibun abin da ta yi sai yanzu bayan shekaru 20 sannan taji ciwon abin. To wai tsakanin Jimmai da 'yarta waye zaifi jin kunya? Ita Jummai da ta ringa tikar rawa matasa na murna, ko kuwa 'yarta da taga an hasko uwarta na fama tikar rawa cikin samari?

Wata rana wasu 'yan mata zasu yi wasannin Nishadi a makarantarsu sai suka shirya yin wani wasan kwaikwayo. Mero tace zata fito a matsayin 'yar iska! Anan aka yi ta ja inja wasu suna cewa zata iya wasu kuma suna cewa bazata iya ba, ganin haka sai La'azaru ya kirawo Mero yace bari na baki labarin wani abu da baki sani ba. Ya kwashe labarin abin da ya faru da Jimmai a bikin Kuluwa tsaf ya gaya mata, yace mata ba hana ki fitowa nayi a matsayin 'yar iska ba, amma shawara nake baki KIYI KUNU AMMA KADA KIYI KUNU KI ZO KINA SHAN KUNU!

Sau da yawa wasu daga cin matasa musamman 'yan mata sukan so su yi abubuwa na morewa da gwangwajewa a lokacin da suke tsaka da 'yan matancinsu basa tunanin wani abu da zai iya faruwa!. Wata idan tace zatayi wani abin aka hana ta zata ga duk duniya ita anshiga rayuwarta ne, amma bata sani ba a she gaba ake jiye mata. Yanzu idan muka kalli Labarin Jimmai zamu ga cewa ita a lokacin da take tikar rawa a gaban Dan-Asabe Me kalangu a bikin Kuluwa bata jin komai, amma bata ji ciwon Abun ba sai bayan shekaru 20. Lallai mai hankali shine yake gane dingishin kwado. Dan haka Kukan kurciya . . .

No comments:

Post a Comment