Sunday, April 7, 2013


LABARIN WANI YARO DA YA KWAIKWAYI MALAMINSU

Wasu yara ne su uku suke zuwa makarantar Firamare, daga cikin yaran nan uku akwai wani mai suna Halifa ya lura sosai da yadda malamin PEnsu malam Salisu yake sanya hula. Dan haka ya hadda ce, duk ranar Juma'a Halifa da sauran 'yan uwansa sukan tafi masallaci tare da mahaifinsu, duk lokacin da aka yi musu wanka aka saka musu kaya aka saka musu hula sai Halifa ya karkata hularsa yadda yaga Malam Salisu yana sakawa. Duk sati haka yake yi, Mahaifiyar Halifa ta lura da yadda yake saka hula yana karkata ta, rannan sai tace masa kada ka sake karkata hula irin ta 'yan iska, budar bakin Halifa sai yace "Ai Malam Salisu ma haka yake sa Hula" akayi juyin duniya Halifa ya gyara hularsa yaki, sai yace ai malam salisu ma haka yake sakawa. Da labari yaje kunnen Mahaifinsu Halifa, sai yace masa kada ya kara karkata Hula, yaro ya dage cewa Ai haka malam Salisu yake saka hula. Rannan dai Mahaifinsu Halifa yace shi kuwa sai yaje yaga Malam Salisu, yana zuwa Ofishin Head Master, ya tambaya cewa yazo ne yaga malam Salisu Malamin Ajinsu Halifa, aka ce ya jira za'a nemo Malam Salisu, cikin Kankanin Lokaci sai ga Malam Salisu yana tahowa daga Nesa, Mahaifin Halifa yace Lallai wannan mai tahowar shine Malam Salisu, domin irin yadda ya karkata Hularsa babu bambanci da yadda Halifa yake karkatawa. Da Malam Salisu ya shigo suka gaisa da mahaifinsu Halifa, sai yake gaya masa ai Halifa ne duk lokacin da aka saka masa Hula sai ya karkataa yace Ai haka Malam Salisu yake saka, Munyi munyi ya daina amma sai yace Haka kake sakawa, Shine na ce ni kuwa sai na zo naga Malam Salisu, kuma abin mamaki shine yadda ka karkata haka Halifa yake karkatawa kamar kaine kake saka masa. Jin haka sai malam salisu ya gyara hularsa ta koma dai-dai, yace Insha Allah daga Yau na daina Karkata Hula. Wannan labari a gaske haka ya faru. Wannan kuma yake kara tabbatar mana da cewar Iyaye ba su kadai ne zasu baiwa 'ya 'yansu tarbiyya ba, Malamai ma suna da gudunmawa me yawan gaske da zasu iya bayarwa wajen kyautata tarbiyyar yaran da aka basu Amana. Domin anan zamu ga yadda Halifa yaki yarda da maganar mahaifinsa amma ya gwammace ya kwaikwayi Malaminsa wannan ya nuna tasirin Malamin sosai, ko shakka babu irinsu Halifa suna da yawa.

Hakika a yadda al'amarin ya nuna cewa Yara da yawa musamman 'yan Firamare suna koyar dabi'um Malamansu, na kirki ko akasin haka. Wannan kuma kalubale ne ga Malamai Lallai suyi shiga mai kyau, kuma su nuna kyawawan halaye a yayin da suke koyar da dalibansu, domin da yawan yara suna koyar malamansu ta dabi'a ko magana ko yanayin sanya sutura. Abubuwa marasa kyau ko da malamai suna yi to lallai su kaurace musu a duk lokacin da suke cikin makaranta wajen Dalibansu, musamman SHAN TABA, ko dura ASHAR ko GWALNAGWASO ko RANGWADA dama dukkan wasu abubuwa da basu kamata ba. Lallai YARA MANYAN GOBE, Allah ya taimaki Yara.

No comments:

Post a Comment