Tuesday, April 23, 2013

MASU KASHE MUTANE BAZA SU DAINA BA, HAR SAI . . .


MASU KASHE MUTANE BAZA SU DAINA BA, HAR SAI . . .

Wadansu musulmi su kan dauki wani tsarin rayuwa na daban marar dadi wanda ya sha bamban da irin rayuwar da Alkur’ani ya nuna. Daya daga cikin kusakuran da irin wadannan mutane masu raunin imani da alfahari, wadanda ba su damu da aikin yada sakon musulunci ta hanyar dabi’u masu kyau ba, shi ne yadda suka dauki rayuwar wannan duniya kawai ba ta wuce mutum ya yi aure ya tara da iyalinsa, ya haifi ‘ya’ya ya rene su sannan ya tara abin duniya ba. Tabbas wadannan abubuwa ne da ba su sabawa koyarwar musulunci ba. Amma inda kuskuren yake shine musulmi ya mance da babban dalilin zuwansa wannan duniya, wanda shine bauta da bin dokokin Allah, ya ta’allaka kawai kan aure da haifar ‘ya’ya, da kin tafiyar da ni’imomin da Allah ya yi masa akan tafarkin addini inda ya kan tafiyar da daukacin rayuwarsa cikin hanyar gulma da cin naman sauran musulmi alhalin ya watsar da kyawawan dabi’u na addini.

Sannan wasu sun dauki hanyar zubar da jinin mutanan da basu jiba, basu gani ba, muslumi ne ko kirista, wai ita ce hanyar jin dadi da morewa a wajensu. Shin wanne irin dadi masu kashe mutane suke ji idan sun aikata kisan nasu? Shin wanda ya kashe wani shi zai iya hana kansa mutuwa ne? Idan da ace zai iya hana kansa mutuwa TABBAS da yaci riba akan wanda ya kashe, amma tunda ba zai iya hana kansa zuwa barzahu/lahira ba, to ya sani ya sake laftawa kansa nauyi ne da ba zai iya dauka ba ranar alkyama. Allah ta'ala yana fada cewa:

Ranar da Alkiyama za ta tsaya, masu laifi za su yi rantsuwa cewa ba su zauna a duniya daidai da awa guda ba. Kamar haka suka kasance ana rudar da su.- Sura ta 30, aya ta 55

Yana da kyau mu sani cewar su wadannan miyagu azzalumai masu aikata kisan kai da alfasha, har duniya ta zo karshe baza su daina aikata irin wannan danyan aiki nasu ba, har sai lokacin da mutumin da za'a kashe ya tashi domin kare kansa! Dan haka ya zama dole a garemu mu tashi tsaye a cikin lungunanmu da unguwanninmu dan baiwa rayukanmu da na iyalanmu kariya. Shakka babu, abinda ya faru a Baga (Borno) da Gujba(Yobe) kisan kare dangi ne, amma abin takaici sai bayan awanni 48 sannan shugaban kasa ya bayyana cewa WAI a gudanar da bincike, wanda muna da masaniyar duk irin wadannan kashe-kashe da akeyi cewa ake a gudanar da bincike, bamu taba jin inda binciken ya tsaya ba, wannan shima haka abin zai wuce kamar yadda saura suka wuce, bama fata. Abinda ya faru karara ya tabbatar mana da cewa hukumomi ba zasu iya samar mana da tabbatacce kuma Ingataccen tsaron rayuka da dukiyoyinmu ba, bil hasali ma sune suke kara taimakawa 'yan ta'adda miyagu Azzalumai wajen cigaba da karkashe al'umma.

Kuma karya ne wallahi shugabanni su ce wai mu koma mu dinga ADDU'A! Shin su sun yarda da addu'ar ne? Ai Manzon Allah ba addu'ah yayi ya kwanta ba. Kowa yasan mutanan da suke aikata wannan ta'addanci ba MALA'IKU bane kuma ba AL'JANU bane, Bil-adama ne, dole hukumomi su tashi wajen baiwa al'ummarsu kariya ta dukiyoyinsu da rayukansu, ba wai kawai ace mu koma gida muyi addu'ah ba, idan haka ne, ina amfanin hukuma idan har addu'ah kawai za'ayi Allah ya bada zaman lafiya. Amerika ai ba addu'ah suke yi ba, aiki suke yi da gaske na kare al'ummarsu. Dan haka hukumominmu basu da wani dalilin da zasu kalli al'umma su ce wai su koma masallatai su yi addu'ah ba. Ina amfanin mas'uliyyar da take kansu? Ba ina inkarin addu'ah bane, tabbas akwai bukatar muma mu dage da addu'ah. Amma mu kwan da sanin baka yin addu'ah ka kwanta sai ka tashi kayi aiki da gaske sannan Allah zai taimake ka.

Dan haka, Kada ka taba zaton abinda yake faruwa ba zai zo kanka ba. Ya zama dole mu tashi muce YA ISA HAKA NAN, idan kuma ba haka ba zamu cigaba da zama cikin kaskanci da wulakanci a cikin gidajenmu. Allah ya kiyaye.

Yasir Ramadan Gwale
23-04-2013

No comments:

Post a Comment