Saturday, February 25, 2012

Su Wa Ke Da Alhakin Lalacewar Ilimi A Yankin Arewa?

Ilimi garkuwar dan Adam, kamar yadda wani mawaki yake cewa “can hakika bada tangarda ba, an lura mai ilimi shike morewa kwalkoliyar daraja shi hau shi dare dam, shi ko marar ilimifa ko hangawa, kalbi marar ilimi abin rainawa, himma da kwazo garkuwar mashiyinku . . . hakika kamar yadda wannan mawaki ya gwarzanta ilimi ya cancanci wannan yabo, haka kuma ya nuna cewa mai llimi kamar wani kare ne abin a wulakanta domin dai kowa yasan kare wata dabbace da bata da wata kima tsakanin mutanan kwarai, haka kuma mai ilimi shi ne fitilar al’umma shi yake bayyanar da haske daga duhun jahilci.

Ilimi shi ne yake maida karami ya zama babba mai kima da daraja, haka kuma rashinsa yakan sanya kaskanci da wulakanci, ka kwatanta dukkan wata irin kasaita da karramawa da kasani da ilimi, ka kuma kamanta dukkan kaskanci da wulakanci da koma baya ga rashin ilimi. Hakika tazarar ilimi da jahilci tazara ce mai yawan gaske da kana iya kamanta ta da sama da kasa, domin ko da wasa biyun bazsu taba haduwaba. Na tuwa ranar da aka sanyani makarantar firamare, ina dokin shiga makaranta, bayan da muka shiga ofishin hedimasta, ya daga kansa ya nunamin wata kalanda da hoton wani gida na bukka yace dani yaro kaga wannan gidan, na daga kaina na kalleshi yace ilimi na iya bunkasashi ya kasaita, haka kuma duk girman gida ilimi na rusashi; hakika wannan magana tayi tasiri a iya tsawon rayuwata kuma sau da yawa nakan tuna wannan magana. Don kuwa wata rana muna hira da marigayi Arc. Musa Tanko Waziri yake shaidamin cewa shi ya taso mahaifinsa talaka ne, amma yanzu gashi ya mallaki gida da mota kuma ba gadone na mahaifinsa ba, yace to haka ilimi ke daukaka mutum daga rayuwa ta kaskanci zuwa rayuwa ta daukaka.

Idan kuma muka dawo batun ilimi a yankin Arewa abin a zubar da hawaye ne a ciza yatsa. Domin bincike da alkaluman kididdiga na kara nuna cewa kullum harkar ilimi tana kara samun koma baya a wannan yankin da akajima ana daukin ganin ya dore. Hakika yankin Arewa shi ne yankin da yafi kowane yanki yawan mutane a Najeriya, bayaga haka kuma ga fadin kasar noma da albarkar kasa, amma sai dai wannan yanki namu cike yake da tarin jahilai da marasa aikinyi, halin da wannan yanki yake ciki hakika wani irin mawuyacin hali ko yanayi ne da ya shallake hankali da tunani ganin cewar magabatanmu da sukayi kokarin yimana tsuwurwurin samun ingatacciyar rayuwa da samun nagartacce kuma ingataccen ilimi sun kafa harsashi mai kyau. Saninmu ne cewar da yawan magabatanmu na yanzu sunyi karatu kyauta a lokacin da kasafin kudin wannan kasa bai kai kaso daya cikin dari na kasafin kudi na yanzu ba, sunyi karatu kyauta aka basu aiki da motocin hawa da gidajen kwana su da iyalansu da kuma albashi mai inganci, amma har kawo yanzu sun kasa biyan wannan kasa bashin da ta basu na moriyar ilimi da suke ci a yanzu.

A shekarar da ta gabata ta 2011 hukumar kula da kidayar jama’a ta kasa National Population Commission karkashin jagorancin shugabanta Cif Samoila Danko Makama ta fitar da wata kididdiga da take nuna cewa a Najeriya yankin Arewa maso gabas shi ne yankin da yafi kowane yanki yawan mutane jahilai, inda yankin Arewa maso Yamma yake binsa a baya da kuma yankin Arewa ta tsakiya; sannan wannan kididdiga ta nuna cewa yankin kudu maso yamma shi ne yanki da yafi kowane yanki karancin mutanan da basu yaki jahilci ba, haka kuma wannan kididdiga ta nuna cewa jihar Ekiti kusan itace jihar da tafi kowace jiha adadi mafi karanci na wadanda basu je makarantar boko ba; a yayinda jihohin Jigawa da Zamfara da Yobe da Gombe da kuma Kebbi sukafi adadi mafi yawa na wadan da basu halarci makarantun Firamare da sakandare ba.

Haka kuma, wannan kididdiga ta nuna cewa mafiya yawan mutane a Jihar Legas suna kashe kusan kashi 63 na kudadensu wajen yin hidima ga karatun ‘ya ‘yansu, inda sukace mafi karancin kudin da iyaye kan kashewa ‘ya ‘yansu yakan kama daga 20,000 zuwa abin da ya yi sama a duk zangon karatu; sannan kuma ya nuna cewa a yankin Arewa mafiya yawan mutane masu dan abin hannu sukan kashe kusan kashi 17 na kudinsu domin karatun ‘ya ‘yansu abin da ya kama daga 5,000 zuwa abin da ya yi sama kadan akan karatun ‘ya ‘yansu, kuma yankin da yafi kula da harkar kartun yara kanana a Arewa shi ne yankin Arewa ta tsakiya. Muna tsaka da wannan komabaya ne kuma kwatsam sai ga wasu da suke da’awar shi kansa karatun Bokon Haramunne!

Hakika wannan rahoto abin duba ne kwarai da gaske. Ya rage na mutanan Arewa su gasgata wannan rahoto ko su karyatashi amma dai ko babu komai gaskiyar al’amura tana kara bayyana, domin a yayinda dalibai 2,300 suka samu damar rubuta jarabawar JAMB a shekaru biyu da suka gabata a Jihar Jigawa takwarorinsu na jihar Imo kusan 90,000 suka sami nasarar cin wannan jarabawar. Haka nan kuma a shekarar da ta gabata kamar yadda sabon gwamnan jihar Zamfara ya fada a wata hira da ya yi da jaridar Daliy Trust ya ce yara 60 ne kacal suka sami nasarar cin darasi biyar na shiga jami’a wato 5credit a jarabawarsu ta WAEC da NECO acikin kusan yara 30,000; sanna kuma a dai wannan shekara da ta gabata a cikin yara 18,000 da suka zauna wannan jarabawar ta NECO guda 18 ne kawai suka iya samun darasi guda biyar a jihar Gombe kaga kenan ana da kwantan yara 17,982 a wannan jihar da bazasu sami damar shiga jami’a ba. Sannan kuma idan zamu iya tunawa a shekarar 2003 matasa 45,000 suka samu nasarar kammala jami’a a jihar Imo a daidai lokacin da matasa 5,000 ne kacal suka sami nasarar kammala jami’a a jihar Kano, jihar da akace tafi kowace jiha yawan jama’a a Najeriya da kusan mutane sama da miliyan 10 a kididdiga ta baya-bayannan.

Shakka babu wannan alkaluma suna kara tabbatar da cewar yankin Arewa shi ne yafi kowane yanki adadi na wadanda basu yaki jahilci ba a Najeriya. Hakika wannan ba karamin kalubale bane ga daukacin gwamnatocin Arewa da sarakunan Arewa da manya masu fada aji a wannan yanki, domin wannan ba karamin abin tashin hankali bane ace irin wadan nan alkaluma ba wai raguwa suke ba kullum karuwa suke, nasan Allah ne kadai yasan adadin daliban da ake bari kwantai a kowace shekara a Arewa da basu sami damar shiga jami’a ko makarantar gaba da sakan dare ba. Nasan a jihar Kano akwai wata makaranta da gabaki daya dalibanta kaf babu dalibi ko daya wanda ya iya samun nasarar cin darasi biyar na 5credit. Duk wannan na faruwa ne a lokacin da gwamnatocin Arewar suke ikirarin kashe makudan kudade a harkar ilimi.

Duk da irin wannan komabaya da ake samu a harkar ilimi a Arewa, kuma ga wata matsala ta karancin dakunan daukar darussa da kuma cunkoso a wadanda ake da su, ka kai ziyara duk wata makaranta ta firamare ko ta sakandare da ke kusa da kai kaga yadda ake cunkusa yara sama da dari a aji daya. Sanna kuma ga matsalar karancin malamai domin zakaga malamin lissafi guda daya shi ne yake koyar da ‘yan aji 1 da aji 2 da 3 na babba ko karamar sakandare, sannan kuma ga rashin kwarewa da ta dabaibaye malaman musamman na firamare da karamar sakandare, domin a wani bincike da na gudanar na kai ziyara wata makaranta inda na sami wani malami dalibai sun kewayeshi yana ta yi musu feleke inda na bukaci yin magana da shi da turanci abin mamaki sai yayi tsuru-tsuru yana kame-kame ya nemi da mu koma gefe na fuskanci kwata-kwata baima san abinda yake ba, kuma wai a haka ake koyar da karatu, ka rasa wai me ake koya musu ne! Sannan kuma mun sani cewa yara manyan gobe wadanda sune ake fatan zasu rike kasarnan idan hali ya yi amma anbata musu lokaci da rayuwa, kaga yaro ya kammala sakandare bazai iya baka cikakkiyar jumla da turanci ba a haka ake son yaje yayi ko ‘yar difiloma ko wani karatun yazo a bashi koyarwa a firamare! kuma wadan nan yara acikinsu ne akesa ran Arewa ta fitar da likitoci da injiniyoyi da manyan malamai a fannoni daban daban da suka shafi al’umma.

Bayan haka kuma, jami’o’in da muke da su a Arewa bazasu iya daukar kaso 25 na daliban da suke kammala sakandare ba a kowacce shekara, a bara kawai a dalibai 45,000 ne suka nemi guraban karo karatu a jami’ar Bayero da ke kano amma dalibai 3,000 ko sama da haka ne jami’ar zata iya dauka, haka idan kaje jami’a Ahmadu Bello dake zariya da Usmanu Danfodiyo dake Sokoto da Maiduguri abin yake. Idan kuma ka dauki jihar Ogun a yankin kudu maso yamma tana da adadin jami’o’i da zasu iya bayarda takardar shaidar kammala digin farko kusan guda 8 daman kar ka tambayi jihar Legas da ta ke da jami’o’i barkatai da suke bayar da wannan shaida. Mu kalli yadda gwamnan jihar Rivers mista Rotimi Amechie inda ya dauki nauyin dalibai ‘yan asalin jiharsa kusan 45,000 zuwa karo karatu a fannoni daban-daban a kasashen turai da Amerika abinda ko gwamnatin tarayya bata taba yin irin wannan muhimmin kokari ba inda ya ware kudi wajen Naira Biliyan 14 domin wannan aiki.

Sannan kuma, idan muka kalli wadannan alkaluma babu wani shiri da gwamnatocinmu suke da shi mai karfi na koyar da matasanmu sana’o’in hannu domin su dogara da kansu, da kuma fuskantar rayuwarsu ta nan gaba, kullum ana kara samun ‘yan zaman banza da kashe wando da ‘yan maula da tumasanci da ‘yan jagaliya, ka kalli kowane irin babban titi ko mahada a yankin Arewa kaga tarin mabarata masu karfi da jini a jika wadanda zasu iyayin sana’o’i amma anaji ana kallo sun zama mabarata kuma ana kara kashe musu guiwa mai makon karfafasu, a gefe guda kuma gashi kullum rayuwa tana karayin tsada kudi suna karayin karanci a hannun mutane, wallahi idan ba hankali mukayi ba wataran kanaji kana kallo al’majirai zasuyi yi maka taron dangi su turmusheka su wafci kudi daga gareka, mu kalli irin yadda kana tsayawa akan danja/titi zakaga al’majirai sun baibaye maka mota kamar saci babu, shin yanzu bazamu kalli wannan a matsayin wani kalubale ko barazana ba?

Sau da yawa sai kaji mutanen Arewa suna cewa sana’o’in hannunma sunyi karanci a yankin Arewa. Wanda kuma idan kabi wannan magana sai kaga ba gaskiya bace, domin mu kalli irin dimbin inyamurai da yarabawa ‘yan kudu da suke yankin Arewa shin zaman banza sukeyi? Mu kalli irin yadda ‘yan Nijar da Kamaru da cadi suke tudadowa yankunanmu musamman idan aka ce maka rani ya yi shin zaman banza suke yi? Wani zai iya cewa ai suma ‘yan Arewa suna zuwa yankin kudu, sai mu tambaya shin idan ‘yan Arewa sunje kudu me sukeyi? Da yawan ‘yan Arewa dake kudu sunayin kaskantattun sana’o’ine misali shushana(me wankin takalimi) da makamantansu, kuma wani abinda zai baka mamaki da haushi shi ne sai kaga mutumin Arewa yana sana’ar sayar da zaren zura carbi a kudu ko kuma sayar da allura da zare, shin ka taba ganin inyamuri ko beyerabe yana sana’ar sayar da goro da taba a Arewa?

Ga rashin ilimi ga jahilci ga matsanancin talauci shin me ka ke jin zai faru? Mukallai yadda rikicin bayan zabe ya auku a yankin Arewa, domin wannan ba rikicin kabilanci bane ko na addini da Najeriya tayi kaurin suna akansa ba, duk wadan da sukayi wannan kone-kone da fashe-fashe ‘yan Arewa ne kuma dukiyar ‘yan Arewa suka kone! Shin wannan ba zai zama izina ga shugabanninmu ba? Bahaushe yace a lokacin da ka kure mage taje bango to ka sanifa kanka zata juyo, Lallai da tarin jahilai marasa aikinyi gara tarin masu ilimi marasa aikinyi domin shakka babu mai ilimi ba zai shiga hanayi da hargitsi irin wannan da zai kai ga hasarar dukiya ba, kuma alal a kalla mai ilimi yana da wani tunani na daban da ya sha bamban da jahili duk da shima yana da nasa tarin matsalolin na kaucewa dukkan wasu sana’o’in hannu.

Sannan kuma shi talaka bayan irin wannan mugun koma baya da yake aciki, babu wani yunkuri da yake yi na kwatar kansa daga wannan hali da ya yi kama da kangin bauta ko mulkin mallakar bakaken fata ‘yan uwansa, iyaye basayin wata hobbasa domin ganin ‘ya ‘yansu sun sami kyautatuwar rayuwa anan gaba, ankyale yaro shi ne malamin kansa shi ne zaiyiwa kansa tunani kuma ya yankewa kansa hukunci! Kaga iyaye na gadarwa da ‘ya ‘yansu talauci da gangan, bayan wanda hukuma ta jefasu ciki.

Ya kamata hukumominmu su tsaya su duba wannan koma baya da wannan yanki namu yake ciki da kuma nemo hanyoyin da za’abi wajen warware wadan nan matsaloli. Kuma yana daga cikin al’adarmu a wannan kasa shi ne duk wata matsala da take damun al’umma sai kaji hukumomi sunce a kafa kwamitin bincike bayan ga abu nan a zahiri babu bukatar kafa wani kwamiti, kaji anwarewa kwamiti dimbin kudi kuma a karshe ba’a aiki da rahoton kwamitin, yanzu kwamitoci nawa ne aka kafa tundaga 1999 zuwa yanzu wane kwamiti aka taba yin aiki da rahoton da ya kawo? Shin nawane aka kashe wajen aikin kwamitoci daga wannan lokaci zuwa yanzu zaka samu dimbin kudadene suka tafi a iska ba tare da biyan bukata ta ko sisi ba.

Hakika duk wanda ya bibiyi wadan nan alkaluma, sai ya yi tambayar shin su wane suke da alhakin duk wadan nan abubuwa da suka dabai-baye wannan yanki mai tarin albarkar kasar noma, musamman ta fuskar ilimi, ina gani wannan ba laifi bane da za’a dorawa hukuma ita kadai ba kusan bangarori hudu sunyi tarayya a ciki. Na farko su ne yaran domin da yawan yaranmu yanzu basason karatu domin suna kallon kawai wahalar da su ake yi, yara sun gwammace su bata lokaci mai yawa wajen kallon kwallo da tattaunawa a kan dakali da guraran hira marar amfani, da kuma bata lokaci mai tsada wajen tattaunawa ko musayar ra’ayi a zaurukan sada zumunta a 2go da sauransu.

Sannan bangare na biyu, su ne iyaye, hakika iyaye suna da gudunmawa mai yawan gaske da zasu baiwa ‘ya ‘yansu wajen samun ingatacciyar rayuwa. Da yawan iyaye a Arewa basu damu da abin da ya shafi karatun ‘ya ‘yansu ba, mu kalli abokan zamanmu Yarabawa zakaga beyerabiya tana gasa masara ko tallar gugguru da gyada kawai domin ta sami kudin da zata biyawa ‘ya ‘yanta kudin makaranta. Iyaye maza sun gwammace su canza sabuwar talabijin ko sabon babur da su biyawa ‘ya ‘yansu kudin makaranta, ita kuma uwa ta gwammace tayi zubin adashi ta dinka atamfar ankon bikin kawarta da ta taimakawa danta ko ‘yarta da kudin sayan litattafan karatu.

Bangare na uku kuma, sune al’umma, hakika al’umma suna da gudunmawa mai yawan gaske wajen ganin yaransu sunsami ingataccen ilimi, ta hanyar daukan nauyin yara marasa galihu da kuma shiryawa yara darussa na musamman da kuma fadakar da yaran illalar da ke tattare da jahilci da rashin aikin yi. Abin mamaki sai kaga kowa bai damu ba, yaransa kawai ya sani, akwai wani yaro da ya rasa dukkan iyayansa ya kasance babu wanda yake kula da rayuwarsa kasancewar a gidan haya ya taso sai wata tsohuwa take bashi abincin dare, wannan yaro maganar wannan mata kawai yakeji duk abinda tace ya bari ya bari, kaga da haka al’umma suke taimakawa rayuwar irin wadan nan yara da ansamu kyautatuwar lamura da samun ingantacciyar al’umma, sannan ya kamata mu fadaku mu sani ba komai ne hukuma zatayi mana ba, akwai abubuwanda dole sai mun hada dari da kwabo wajen taimakawa rayuwarmu da ta yaranmu.

Kashi na karshe kuma, su ne gwamnati ko hukuma, hakika duk gwamnatin da ta san metakeyi tasan dukkan abubuwan da ya damu al’ummarta kuma sun san hanyoyin da za’abi wajen magance dukkan matsalolin da suke barazana ne ga dorewar al’umma. Ko dai gwamnati a mataki na karamar hukuma ko jiha ko gwamnatin tarayya. Daga karshe ina mai addu’ar Allah ya shiryi shugabanninmu, kuma Allah ya basu ikon sauke nauyin da yake kansu na al’umma.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment