Sunday, February 5, 2012

Mallam Salihu Sagir Takai: Wani Hanin Ga Allah Baiwa Ne!



Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, ubangijin talikai, Wanda ya dauki wannan al’umma ya fifita ta akan sauran al’ummatai, ya sanya ta jagora ga sauran mutane don ta shiryar da su ga hanyar cin nasara a rayuwarsu ta duniya da lahira. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen Manzanni, cikamakin Annabawa, wanda Allah ya fifita shi ya ba shi littafi mafi cika da kamala wanda ya ke shafe-zane ne ga sauran littatafai, Annabi Muhammadu da alayansa da sahabbansa dakuma wadan da sukabi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamko. Dukkan wanda Allah ya shiryar shi ne cikakken shiryayye, haka kuma duk wanda Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne.

Allah buwayi gagara misali, mai yadda ya so; mamallakin ranar sakamako, wanda mulkinsa bazai taba tauyewa ba ballantana ya kare, haka rahama da ni’imarsa batada iyaka ga bayinsa masu hakuri, Allah da kansa yace kuyi Bushara ga masu hakuri. Allah ya fada acikin littafinsa mai tsarki cewa mulki nasa ne, kuma yana bada shi ga wanda yaso akuma lokacin da yaso. Wannan haka sunnar Allah ta ke, sauda yawa Allah yakan baiwa wasu mulki amma halaka ne a garesu, haka kuma yakan baiwa wasu ya zama rahama a garesu, muna addu’ar Allah ya tabbatar mana da rahamarsa.

Hakika lokacin da aka gudanar da zaben gwamna a kano kusan mafiya yawanmu da muke goyon bayan Mallam Salihu Sagir Takai wannan zabe ya zo mana da bazata, domin bamu yi zaton haka ba, sai dai bamu gafala da mancewa da hukuncin Allah ba. Shakka babu dole hankali ya tashi dole zukata su kadu, a yayin da ka ke sa ran samun Nasara ta zo maka akasi; mun shiga cikin dimuwa da damuwa da tashin hankali da wannan zabe. Amma duk da abin da ya faru muka maida komai ya zuwa ga Allah, hakika munyi hakuri da juriya, muna rokon Allah ya bamu ladan hakuri kamar yadda ya yi alkawari.

Muna son Mallam Salihu Sagir Takai ne, saboda halayensa na kirki da suka bayyana zahiri a garemu da kuma kyautata masa zaton da mukeyi, dakuma irin yadda yake riko tare da kula da addini, hakika Mallam Takai mutumne mai cike da kamala da sanin ya kamata, ga yakana, ga fara’a, sannan kuma ga tsayawa kan gaskiya, ga ibada. Wadan nan dama wasu da dama suka sanyamu nuna soyayya ga takararsa da dan uwansa kamar yadda yake fada Dr. Bashir Shehu Galadanci, shima kamar dan uwansa Dr. Galadanci mutumne mai tsantseni da kokarin bingaskiya ga kuma nuna tsoron Allah a zahiri, dun wadan da suka sanshi tunda sun shaida haka, tun yana malamin makaranta a jami’a yana da kula da dukkan al’amura da suka shafi addini.

Hakika, wadan nan mutane guda biyu idan za’ayi bayanin halayensu na gari, za’a dade ana bayaninsu. A lokacin da suka rike mukaman kwamishinoni a gwamnatin Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, sun nuna kankan da kai da tsoron Allah akan abin da aka basu na amana. Wata kila wannan shi ne dalilin da ya sanya mai girma Sardauna ya zabo su, Allah masani, mu kam munyi aiki da abinda ya bayyana na zahiri a garemu, kuma mun kyautata zato a garesu da kaso mai yawa.

Kamar yadda kowannemu ya sani, bayan kammala zabe, hukumar zabe ta bayar da sanarwar cewa Rabiu Musa kwankwaso shi ne ya samu nasara a wannan zabe. Bayan wannan sanarwa ta watsu ga jama’a, abubuwa na tashin hankali suka biyo baya domin da masu goyon bayan wanda aka bayar da sanarwar shi yaci nasara sunfito kan titunan cikin birni sunata kokarin nuna murna da farinciki da wasu munanan alkaba’i, domin rahotanni sun zomana cewa ansami wasu da dama da suka ringa zagin shari’a cewa babu shari’a da kuma zagin masu gemu, sun manta da cewa sifface ta annabi, da aibantasu da muguwar sifa, ance mata suka ringa hawa kabu-kabu ana kewaya gari da suna ihu babu shari’a. Sai wannan ya bayu a garemu cewa lallai adawar da aka ringa yiwa Sardauna cewa baya tafiyar da shari’a zaluntarsa akayi domin su sun tabbatar ana aiwatar da aiki da shari’a dai-dai gwargwado. Ankafa hukumar Shari’a da Hizba, zakka, Hubusi da Adaidaita sahu, wanda duk sharia itace manufarsu, hakika mun shaida haka.

Bayan nan a sakamakon da ya zowa su Mallam Salihu Takai cewa wannan zabe akwai al’amura na rashin gaskiya acikinsa, wannan ta sanya jam’iyyar Mallam Takai ta shigar da karar kalubalantar wannan zabe, kamar yadda kowa yasan cewa bin hakki ba laifi bane idan har kana ganin anyimaka ba dai-dai ba. Anje kotun zabe (tibunal) tare da dukkan shaidun da ake da su amma wannan kotu tayi amfani da damarta ta kori wannan kara, ba tare da ta cemana Mallam Salihu Sagir Takai ba shi ya samu nasara a wannan zabe ba, wannan ce ta sanya aka daukaka kara zuwa kotun gaba ta Appeal wadda take a Kaduna, inda nanma kotun tayi amfani da damarta inda ta kori wannan kara ba tare da ta cemana Mallam Salihu Sagir Takai ba shi ne ya samu nasara a wannan zabe ba, wanda hakan ya kara mana kwarin guiwa akan wannan yanayi.

Daga nan kuma aka sake garzayawa zuwa kotun daga ke sai Allah ya isa, wato kotun koli(supreme). Wallahi bamu yanke tsammani daga samun nasara daga gurin Allah ba, yana iya bamu ta wannan hanya kuma yana iya canzawa da abinda yake shi ne mafi alkhairi, don haka muna addu’ar Allah ya tabbatar mana da alkhairi, kuma wadan nan mutane bazamu gusheba muna yi musu addu’ar Allah ya shige masu gaba acikin al’amuransu da yi masu jagora a rayuwarsu ta nan gaba.

Bahaushe yakance wani hanin ga Allah baiwa ne. A ganina a wannan lokaci da muke ciki da Allah bai sanya gwaninmu shi ne gwamnan Kano ba akwai hikima sosai wanda Allah shi yasan iyakarta. A sakamakon al’amuran da suka faru kuma suke faruwa, misali sanin kowa ne kusan duk kasarnan anyi zanga-zangar nuna adawa da cire tallafin man fetur (occupy Nigeria) da gwamnatin tarayya tayi a daukacin johohin kasarnan, kuma bayanai sun nuna cewa gwamnoni sune sukayi ruwa sukayi tsaki akan wannan batu, na tabbata da gwaninmu shi ne gwamna da farin jininsa da soyayyarsa sai ta ragu da yawa akan wannan batu, amma da yake Allah ya san abinda bamu sani ba ya yi abinda ya dace da mu, wannan cema ta sanya gwamnan da yake akai yanzu ko masallacin juma’a baya iya zuwa, wannan har ta kai anmayarda Masallacin gidan gwamnati zuwa masallacin juma’a, Allah mai iko!

Bayan haka kuma sanin kowa ne cewa akano ansami wani mummunan al’amari na tashin bama-bamai barkatai a cikin birni, wannan ya kai ga asarar rayuka masu dimbin yawa, kamar yadda muka sani alhakin kowace gwamnati ne ta samarwa al’ummarta cikakken tsaro na lafiyarsu da rayuwarsu da dukiyarsu dukda cewa Allah shi ne mai tsaremu amma wannan bai hana muyi riko da sababi ba, wannan gwamnati tayi sakaci matuka da gaske inda har aka samu wasu mutane miyagu sukazo suka hallaka al’ummar da basu jiba basu gani ba, domin su wadan nan mutane da ake kira ‘yan Boko Haram rahotannin sun nuna cewa har wasika sun aikewa da gwamnati akan barazanar tsaro amma babu wasu alamu da suka nuna andauki mataki, wannan ya tabbatar mana da cewa tilas wannan gwamnati ta dauki alhakin duk wanda ya rasa ransa ta sanadiyar wannan al’amari, domin hakkinta ne ta kula da sha’anin tsaron jama’a.

Na tabbata da gwaninmu shi ne yake gwamna, da ya shiga cikin wani tashin hankali da dimuwa na cewa mutanan da suka rasu a sanadiyar wancan abu dole ya bada bayani a gaban Allah ranar gobe kiyama, me yasa yana shugaba duk da irin kudin da ake kashewa ta fuskar tsaro abin da ya faru ya kasance, ya dan uwana zaka yarda dani cewa Allah ya tsallakar da gwaninmu daga gurfana a gabansa akan wannan al’amari, muna addu’ar dukkan wadan da suka mutu musulmi a sanadiyar wannan abu Allah ya jikansu ya gafartamusu, ya kuma kare jiharmu daga aukawa cikin irin wannan mummunan yanayi anan gaba.

Kuma wani tuntube da dungushi, wannan gwamnati tayi iyakar bincikenta ta kama mai girma sardaunan kano da laifin al’mundahana da dukiyar al’umma amma ta rasa wannan cema ta sanya mukaji jagoran gwamnatin yana cewa sun bar Shekarau da Allah, na tabbata da ace Mallam Salihu Sagir Takai ne yake gwamna yace Sardauna baiyi al’mundahana ba lokacin da yake gwamna babu mai yarda kowa cewa zaiyi saboda jam’iyyarsu daya shi ya sa aka rufa masa asiri duk irin rantsuwar da zai yi akan wannan batu jama’a bazasu yarda da shi ba.

Don haka muna kara jaddada goyon bayanmu ga Mallam Salihu Sagir Takai da kuma Dr. Bashi Galadanci cewa muna nan tare da su kuma wallahi har yanzu bamu yanke tsammani ba akan wannan al’amari, tunda haryanzu babu kotun da tace bakuci zabe ba, muna rokon Allah ya tabbatar mana da alheri, kuma ya tabbatar mana da duga-duganmu akan hanya madai-daiciya, ya cigaba da yi mana garkuwa da garkuwar nan tashi. Allah ya taimaki jihar Kano.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment