Wednesday, February 8, 2012

Siyasar Kano Tsakanin Shekarau da Kwankwaso!!!



Siyasar kano sai kano, wannan take ko shakka babu ya yi daidai da siyasar kano. Hakika idan ana maganar siyasa a Najeriya akayi maganar Kano to ko shakka babu anzo muntaha wato magaryar tukewa, ba zai zama abin mamaki ba idan akace mutumin kano ya kware wajen iya siyasa, domin sanin kowa ne cewa jihar kano itace mahaifar Uban ‘yan siyasa marigayi Mallam Aminu Kano. Hakika Mallam Aminu Kano ya raini mutane da dama a siyasa, mutane masu akida ta cigaba da kuma kishin al’umma.

Yanzu siyasar kano ta dauki wani sabon salo, domin yanzu idan ana maganar siyasa a kano to babu kamar Mallam Ibrahim Shekarau da Engnr. Rabiu Musa Kwankwaso, don yanzu sun zama alkibla a siyasar kano kasancewar yadda sukayi tasiri matuka a siyasar, ta hanyar dumbin magoya bayansu, da kuma fada aji a tsakanin magoya bayansu, bari muyi bayaninsu daya bayan daya.

Mallam Ibrahim Shekarau: kusan shi ne mutum na farko da ya kafa tarihi a siyasar kano, domin ana cewa ba’a maimaita mulki a jihar kano sau biyu a jere, kamar yadda da daman ‘yan siyasa suke fada cikinsu harda marigayi tsohon gwamnan Kano Muhammad Abubakar Rimi. Cikin wani lokaci mai cike da sabatta juyatta Mallam Shekarau ya zama gwamnan kano a karo na biyu, inda ya karya maganar nan da aka dade ana yinta tsakanin al’ummar Kano. Mallam Ibrahim shekarau ya yi tasiri ainun a zukatan ‘ya ‘yan jam’iyyarsa ta ANPP da kuma da yawa daga cikin matasa da dattawa da kuma mutane masu kishin addini, kai ba su kadai ba ma kusan kowanne bangare na al’ummar kano zaka samu masoya na hakika na Mallam Ibrahim Shekarau.

Sanin kowa ne mallam mutumne wanda yake kokarin sanya addini acikin dukkan al’amuransa na siyasa, wannan ta sanya da yawan wadan da suke hammay da mallam suke ganinsa a matsayin mai ci-da addini, wanda wannan kalma kusan duk wanda ya fadeta ko dai bai san addinin ba ko kuma kawai yana fadar kalmar ba tare da yasan hakikanin ma’anarta ba; atakaice ma’anar ci-da addini a Musulunci “shi ne mutum ya san wani abu na addini wanda al’umma suke matukar bukatarsa amma yace bazai sanar da su ba sai anbiyashi wani adadi na kudi ko dukiya” wannan abinda aka bashi idan yaci to shi ne al’akalu biddini wannan atakaice ita ce ma’anar ci-da addini a musulunce, idan kuwa haka ne to inaganin duk wanda ya alakanta Mallam Ibrahim Shekarau da cewa yana ci-da addini shakka babu ya zalunceshi, kuma ya jahilci addini.

Baza kayi maganar siyasar Mallam Shekarau bakayi batun hakuri da yake dashi ba. Kusan yana daga cikin abin mamaki dangane da Mallam shi ne hakurinsa ya bayyana karara, domin a cikin wani yanayi da yana iya daukar dukkan matakin da yaga dama ga duk wanda ya taba mutuntakarsa, misali an sami wani shakiyyin dan siyasa ya buga hoton malamin da iyalinsa da wasu kalamai na batanci aka kuma kama wannan dan siyasa amma duk da yana da ikon daukar mataki yace ya yafe, sannan mutumne da ake shiga radiyo a fadi magana akansa babu linzami, duk da haka ya yi hakuri, wannan na daya daga abinda ya karawa mallam soyayya a zukatan jama’a da dama.

Mallam Ibrahim Shekarau, kusan a dukkan jawabansa akan jiyoshi yana farawa da karanta suratul fatiha da kuma yin addu’a bayan kammala dukkan wasu jawabai da ya yi, haka kuma mallam mutumne da ya shiga lungu da sako na jihar kano ya zabo mutane masu addini domin sanyasu a mukamai daban-daban da suka shafi al’umma, da dama wasu sunyi kokarin kiyaye nauyin da aka dora musu, wasu kuma sun yaudari malamin domin ayyukansu ya nuna basuda alaka da addini a aikace, sai dai kawai a sifa.

Sannan bayan da mallam yazo karshen zangonsa ya mara baya ga takarar Mallam Salihu Sagir Takai wanda ya yi shugaban karamar hukumar Takai, kuma ya yi kwamishinan Ruwa da kuma kananan hukumomi a jihar kano, sun fuskanci adawa mai tsanani sosai daga ‘yan hamayya, anjefesu da kalamai na bace ainun, haka kuma sun fuskanci adawa mai yawa daga cikin jam’iyyarsu ta ANPP musamman wadan da suke goyon bayan Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo suna ganin kamar juya baya ne ga biyayyar da akecewa Gwarzon na nunawa Mallam Shekarau din.

Bari kuma mu kalli ban garen Engnr. Rabiu Musa kwankwaso. Hakika siyasar kwankwaso tanada abin mamaki kwarai da gaske a jihar kano. Domin siyasarsa ta nuna cewa shi mutum ne mai juriya da karfin hali sosai. Kwankwaso mutum ne da yake da goyon bayan matasa da yawa daga cikin al’ummar kano da kuma ‘yan bangarensa na kwankwasiyya a cikin jam’iyyarsu PDP.

Hakika duk yadda ka kai da adawa da kwankwaso dole ka yarda cewa yanada matukar kishin jihar kano, sai dai mutumne da yake amfani da kausasan bayanai a mafi yawancin magan-ganunsa haka kuma kwankwaso mutumne mai yawan barkwanci, domin da wuya ka saurari kalamansa batareda ya sanyaka dariya ba.

Haka kuma bayanai sun nuna cewa kwankwaso mutumne mai son abubuwa da gaggawa, sabanin mallam shekarau da yake son abi al’amura sannu-sannu, haka kuma kwankwaso mutumne mai matukar son girma kamar yadda wadan da suka sanshi suke cewa domin mutumne da kokadan baya yarda da raini.

Shakka babu kwankwaso ma ya kafa tarihi a siyasar kano domin bayan da bayanai suka nuna cewa ya rabu da al’ummar kano dutse hannun riga a zangon mulkinsa karo na biyu, inda har rahotanni suka nuna cewa ya koma Kaduna da zama shi da iyalansa, daga baya a hankali farin jininsa ya fara dawowa, inda ya komo kano kuma ya yita zagayen kananan hukumomi domin motsa magoya bayansa. Sai dai bayan da ya dawo ya zo da wani slo daban na jan hankalin matasa wannan kuwa shi ne wani take da ake yi masa na kwankwasiyya amana hakika wannan ba karamin abu bane da zaiyi saurin janye hankalin matasa ba, domin ko da shugaban kasa yazo kano sai da yayi wannan take kuma jama’a suka amsa, wanda wannan ta nuna cewa kwankwason ya yi tasiri ainun.

Kwankwaso ya sake dawowa gwamnan kano a karo na biyu bayan tsaiko da ya samu daga gurin Mallam Ibrahim Shekarau na shekaru takwas, wannan kuma ya nuna jajircewar kwankwason da kuma nuna kwazonsa a siyasa duk da bayanai sun nuna cewa uwar jam’iyyarsa ta kasa ta so ta tadeshi a zaben gwamnan da ya gabata, amma da yake abin da Allah ya kaddara shi ne yake faruwa, basu ci nasarar shataleshi ba.

Wannan ta nuna kwarewa matuka a siyasa ta wadan nan mutane guda biyu Mallam Ibrahim Shekarau da Rabiu Musa Kwankwaso, idan har gwamna kwankwason yaci nasarar kammala zangonsa na biyu to sun zama kusan kafada-da-kafada da Shekarau a siyasance, kuma za’a dade ana tunawa da su a siyasar kano.

A bayyane ta ke cewa farin jinin mallam Shekarau na kara samun tagomashi bayan barinsa gidan gwamnati; haka shima kwankwason sai bayan ya gama munga irin yadda yake a tsakanin al’umma zamu tabbatar da kaiwarsa makura. Haka kuma a zaben 2015 kowane bangare zai tsayar da gwaninsa domin gadon kujerar gwamnan kano tsakanin Kwankwason da Shekarau, da alamun cewa daga bangaren Shekarau bazata sauya zani ba wato Mallam Salihu Sagir Takai shi ne zai zamo dan takara a 2015, yayinda a nasa bangaren shi ma ake ganin kamar zaiyi nune, alamu dai sun fara nuna cewa kwankwaso na son gadarda Rabiu Suleman Bichi a bayansa wanda a yanzu shi ne sakataren gwamnatin Kano, kafin zamansa kusan ana masa kallon na kusa da kwankwason sosai domin shi ne ma ya rike shugaban darikar kwankwasiyya a jam’iyyar PDP.

Duk wannan lokaci ne zai tabbatar mana da kwarewar siyasar Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan kano da kuma Engnr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a siyasar kano a zaben 2015 mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment