Thursday, March 1, 2012

Addinin Musulunci Ba Addinin ‘Yan Ta’adda ba ne!!!

Addinin musulunci shi ne addinin gaskiya wanda Allah ya aiko Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi wasallam dashi kuma ya kasance shi ne cikamakin annabawa, kuma addininsa ya kasance cikamakin addinai, don haka babu wani abu da manzon Allah yatafi yabari face ya yiwa musulmi bayaninsa, don haka ne ya cewa sahabbansa da sauran al’ummar musulmi idan kunyi sabani a tsakaninku sai ku koma ga al’qurani da Hadisi, wato sunnarsa. A sabida haka nema a khudubar bankwana da manzon Allah yayi aikin hajjinsa na karshe yace yau ne nake shaida muku cewa Allah yacika addininsa. Don haka babu wani kari ko ragi da zai zo acikinsa nan gaba.

Don haka addinin musulunci addini ne da yake damfare da rayuwar musulmi gaba daya, kuma musulmi na hakika shi ne wanda yake bibiyar me addini yace kafin ya aikata wani aiki, ba sai ya aikataba sannan ya nemi me addaini yace game da wannan abu daya aikata, don haka, rayuwar musulmi rayuwa ce da take tattare da hikima da amana da basira da sanin yakamata, musulmi shi ne aka sani da Hakuri da juriya da tausayi ga taimakawa marayu da nakasassu da mabukata, musulmi baya tayarda hankalin mutanen da basuji basu gani ba. Musulunci addini ne da bai takaicewa kowa komai ba kuma shi ne addinin daya baiwa kowane mai hakki hakkinsa don haka bai takewa wani ko wata hakki ba, kamar yadda wasu la’annanu suke ta kururuwar iblis cewa musulmi suna danne hakkin musamman na mata.

Misali a makon da ya gaba mukaji, wani dan majalisa daga jihar Kuros Riba(Cross River) ya mika wani kuduri gaban majalisar dokokin jihar inda yake neman majalisa tayi dokar da zata baiwa mata ‘yancin gadon iyayansu, abin mamaki banda wannan dan majalisa ya kawo wannan kuduri baka taba jin wannan batu ba, kaga yanzu da misali a wata kasar musulmi dake Arewa ne aka samu irin wannan da sai kaji kungiyoyin da aka kyankyashesu daga kasar Turai da Amerika suna ikirarin ana dannewa mata hakkinsu na cin gadon iyayansu. Haka suma kasashen turai duk da wannan tsugudidi da suke yiwa kasashen musulmi babu wanda ya kaisu danne hakkin mata, yanzu suna ta kumfar bakin cewa Saudiyya ta dannewa mata ‘yancin tuka mota, kuma suna ta kokari su zuga matasa mata musamman wadan da sukayi karatun boko da su fito suyi bore akan basu wannan ‘yancin.

Idan kuma muka dawo batun da ake alakanta musulmi da shi domin bakanta musu, da kuma bata sunan musulunci musamman a gurin wadan da suke kokarin fahimtarsa shi ne kalmar Ta’addanci. Kalmar Ta’addanci ba sabuwar kalma bace a gurin musulmi kuma dukkan musulmi na hakika yana alla wadi da aikata ta’addanci koda kuwa akan dabbobine ba mutane ba, kamar yadda yanzu aduniya ana tsaka da yaki da ta’addanci, kullum ana alakatanta Kalmar ta’addanci ga musulmi ko kuma musulunci, bayan anki yi mana fassarar hakikanin ma’anar wannan kalma, kuma menene mutum zai yi a kirashi da sunan dan ta’adda, ba adalici bane don musulmi ya aikata wani laifi ka alakanta wannan laifin da addininsa ba, don haka bazai zama halal ba don wani musulmi ya aikata wani laifi ya nemi kariya da addini, manzon Allah yace “da Fatima ‘yar Muhammad Allah ya yarda da ita, zatayi sata wallahi da na yanke mata hannu” don haka wannan yake nuna a musulunci babu sani babu sabo duk wanda yayi za’ayi masa gwargwadon abunda ya aikata.

Yanzu kusan duk wani abunda musulmi ya aikata sai akirashi da sunan dan tada zaune tsaye, ko mai tsattsauran ra’ayin kishin addini, dama wasu kalamai na batanci da ake ta kokarin aibata musulmi, ciki kuwa harda jaridun kudancin Najeriya; ko kuma da musulmi ya yi wani kuskure sai kaji anacewa yana neman aikata ta’addanci. kuma, turai da Amurka basuyiwa musulmi adalci ba domin kullum sukan kira musulmin daya aikata wani laifi dan ta’adda ko kuma wasu kungiyoyi na musulunci. Yanzu misali akwai kungiyar ‘yan ta’adda da ke Arewacin Ireland a kasar Birtaniya kowa yasan abin da sukeyi ta’addanci ne akan fararen hula, amma babu wata kafar watsa labarai ta kasashen turai ko gida Najeriya da suka taba kiransu da sunan ‘yan ta’adda. Sannan kuma, mu kalli kungiyar Tamil Tigas a kasar Sri Lanka babu wanda ya kira abinda da sukeyi da sunan ta’addanci duk da dimbin jama’ar da suka halaka; idan kuma muka dawo gida Najeriya mu kalli kungiyar da ake kira ta tsagerun yarabawa ta OPC karkashin jagorancin cif Ganiyu Adams, da kungiyar da suke fafutukar samar da kasar Biafara wadda Ojukku ya jagoranta duk sun kashe dumbin al’umma, amma wa mukaji ya taba kiransu da sunan ‘yan ta’adda!

Akwai manya manyan mutane wadan da ba musulmi ba sun aikata laifukan da idan akwai wani abu da ya zarta ta’addanci to da za’a iya kiransu da wannan suna amma bakaji ana kiransu da ‘yan Ta’adda ba, misali Adolph Hitler karkashin Nazi ya halaka dubban yahudawa amma ba’a taba alakanta wannan abu da yayi da sunan aikata ta’addanci ba, hasalima turawan Jamus ko son tada wannan magana basa son ayi, haka kuma missolouni ya kashe dubban mutane a Italiya ba’a taba kiran abin da yayi da sunan ta’addanci ba, haka kuma a shekarar da ta gabata aka samu wani matshi ya yi harbin kan mai uwa da wabi a kasar Nezalad ko Holand inda ya halllaka mutane sama da 30 amma duk wannan ba ta’addanci bane!

kawai musulmi da kungiyoyinu su ne ‘yan ta’adda misalai kungiyar Jama’a Islamiyya ta Abubakar Bashir dake kasar Indonusiya ankirata da kungiyar ‘yan ta’adda kuma shima jagoran kungiyar ance Dan ta’adda ne, ko masu matsanancin kishin addini, haka kuma ka dauki kungiyoyi irinsu Hamas da Jihadul Islami a Palastinu duk ankirasu da suna kungiyoyin ‘yan tada zaune tsaye dama kar ka tambayi kungiyoyi irinsu Taliban dake Afghanistan, da kuma kokarin da ake tayi na nuna cewa akwai kungiyar al-qa’ida a Arewacin Afirka.

Haka kuma ka dauki daidaikun mutane, musulmi ne amma duk ankirasu ‘yan Ta’adda misali Ayman Alzawahiri da su Baitullah Mehsud da Abu Mus’ab Alzarqawi da su Mullah Dadullah kai harda dama irinsu Abdulbasit Ali Almagarahi wanda ake zargi da kai harin Lokobi. Idan kuma muka dawo gida Najeriya akwai kungiyoyi da daman gaske awannan kasa ankira wasu ‘yan ta’adda wasu kuma ankauda kai daga garesu misali duk irin abinda MEND take aikatawa a yankin Neja Dalta ba’a taba ganin wannan abun a matsayin Ta’addanci ba, itama kungiyar tsagerun yarabawa wadda ake kira OPC ta aikata shegantaka da tsiya iri-iri amma ba’a taba kiranata da kungiyar ‘yan ta’adda ba sannan kuma mukallai mutane irinsu Zamani Lekot da Zamani kaza sun aikata kisan kiyashi ga musulmin zangon kataf amma duk wannan ba ta’addanci bane haka kuma mukalli irin yadda karfi da yaji aka kakaba kungiyar Boko Haram da musulunci da musulmi, duk da ayyukansu sun nuna sunyi hannun riga da musulunci, domin ko a hareharensu kusan gabaki daya musulmi suke kashewa.

Sannan kuma, gashi yanzu tana sake bayyana cewa kiristoci sune ‘yan Boko Haram, abinda ya faru a harim Bom din da aka kai COCIN church da ke birnin Jos, da kuma wasu matasa da aka kama da yunkurin dasa Bom a takwarar wannan coci a Bauchi duk wannan yana kara nuna cewa wannan makarkashiyace ake shiryawa Musulmi, abin mamaki sai gashi jaridun kudu da kiristoci duk sun ja bakinsu sun tsuke akan wannan batu, sai ma wani kokari da akeyi na nuna cewa Musulmi ne suka kai wannan Hari bayan, bayanai sun nuna cewa shi wanda ya kai wannan harin na Jos kirista ne. Abin haushi shi ne lokacin da aka kai harin Bom din madallah sai ga Sarakunan Arewa da Malaman addini da suhgabanni har rige-rige sukeyi zuwa Abuja domin su jajantawa kiristoci da kungiyar CAN, a ranar da abin ya faru sarkin Musulmi ya sabi takalmansa ya yi Abuja domin ya baiwa shugaban kasa hakuri akan wannan batu, amma sai ga shi duk hare-haren da ake kaiwa musulmi babu wani kirista da kake jin yana magana akai; duk wannan abin bazai bamu mamaki ba, domin Allah yace kada ku taba daukar mushirikai a matsayin masoya ko majibinta!

Rahotanni da dama sun nuna cewa, kiristoci ne suke batar da kama ta hanyar sanya doguwar riga da nada rawani, kamar yadda aka kama wani kirista a jihar Bayelsa yana shirin kona coci, haka itama wata mata da aka kama a Bauchi tana shirin sanyawa wata coci wuta duk domin a dorawa musulmi wannan laifi. Wani abin da zai baka mamaki shi ne irin yadda gwamnati ta doge akan sai anbankado tare da hukunta wadan da suka kai harin ranar kirsimatin shekarar da ta gabata a wata coci a garin Madalla, inda aka zargi wani Kabiru Sokoto kuma aka alakantashi da wannan kungiya ta Boko Haram; abin tambaya me ya sa ba’a binciko wadan da suka kaiwa musulmi hari a garin Jos ba, a ranar idi? Sannan me ya sanya ba’a hukunta wadan nan mutanan da aka kama da yunkurin kona coci ba? Kamar yadda da yawan Jaridun kudu suke ta kururuwar me ya sanya ba’a yanke hukuncin kisa ga dan Najeriyar nan da ake zargi da yunkurin tayar da Bom a cikin jirgi a kasar Amerika ba.

Sanna kuma, yanzu kusan ana ta kokarin a nuna cewa duk dan Arewa ko musulmi kamar dan kungiyar Boko Haramne, wanda mu kanmu musulmi munyi allawadai da wannan kungiya ta Boko Haram da ayyukanta, kuma mun tabbatar da cewa ba musulmi bane na hakika. Alhamdulillahi munyi imani da Allah, acikin al-qur’ani, acikin surata 29 aya ta 2 Allah mai girma da daukaka yana cewa “tsammaninku kawai don kunyi imani, haka kawai sasakai ku shiga aljanna batare da irin misalin bala’i da tashin hankali da tsanini da wadan da suka gabaci wadan da suka gaceku basu sameku ba” ya Allah munji kuma munyi da’a. Muna kallon dukkan wadan nan abubuwa da suke faruwa a matsayin wata jarabawa da Allah ya ke yiwa Musulmin wannan kasar, kuma muna rokon Allah ya bamu ikon samun kyakkyawan sakamako. Hakika munyi hakuri, kuma muna kanyin hakuri, amma wannan bazai hana mu tashi tsaye wajen bincike tare da kokarin kare kanmu da dukiyoyinmu daga wadan nan miyagu azzalumanba. A kwanakin baya munjiyo shugaban kungiyar CAN Pasto Ayo Oritsejafor yana kira ga kiristocin wannan kasa da kowannensu ya tashi tsaye domin kare kansa daga dukkan wata barazana ta musulmi ko kungiyar Boko Haram.

Sai ka rasa su waye jagororin Muslumi a wannan kasa, duk irin wadan nan abubuwan da suke faruwa kowa ya kame bakinsa ya yi shiru tundaga malamai da sarakuna da ‘yan siyasa, kowa tsoron magana yake musamman akan abinda ya shafi wannan kungiya ta Boko Haram alhali kuma munsan suna kara bata sunan musulmi ne, wannan kuma bai hana magautanmu amfani da wannan dama suyi ta kururwa da wanna batu ba, da nuna cewar kusan dukkanmu ‘yan wannan kungiya ne. Har yanzu ankasa samun wadan da zasu tashi tsaye suyi kira ga gwamnatin Jihar Pilato da ta biya Musulmi diyyar irin dukkan abin da akayi musu a wannan jihar, kowa ya ja baki ya tsuke, amma ko ya akaji wani abu ya fashe a coci sai ace gwamnati ta biya diyya!

ko shakka babu musulmi ana iya samunsa da kuskure tunda ba ma’asumi bane zai iya aikata ba daidaiba kuma kamata yayi idan musulmi ya aikata wani laifi kada ajingina wannan laifi zuwa ga addininsa, kamar yadda idan kirista yayi laifi musulmi ba zai jingina wannan laifi zuwa ga kiristanci ba, tabbas musulmi na hakika ba dan ta’adda bane kuma addinin musulunci baya koyar da ta’addanci kuma shine ma addinin daya fara allawadi da aikata ta’addanci. domin mace ta shiga wuta saboda mage haka kuma musulmi ya shiga aljanna saboda kare.

Daga karshe ina amfani domin jajantawa al’ummar Arewacin kasar nan bisa wadan nan abubuwa da suke faruwa musamman tashin bama bamai a Borno da Yobe da kano da Gombe dukkan musulmin da suka rasa rayukansu Allah ya jikansu ya gafartamusu, kuma wadanda sukayi hasarar dukiya sanadiyar wannan al’amari Allah ya mayarmusu ninkin abin da suka rasa, kuma wadan da suke aikata wannan ta’addaci muna rokon Allah ya tona musu asiri ya wargaza nufinsu. Allah ya tabbatar da mu akan hanya ta gaskiya, ya bamu lafiya da zama lafiya a kasarmu.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment