Wednesday, March 7, 2012

Matsalar Dan Arewa!!!

Matsalar Dan Arewa!!!

Naka yanzu sai naka, ‘yan Arewa ga naku . . .! Wannan wani baiti ne na wata waka da akayiwa wani dan siyasa da ya fito neman takara daga Arewa. Hakika wannan baiti yana nuna abubuwa da yawa; kusan a bayyane ta ke cewar duk lokacin da kaji ana maganar Arewa to ko shakka babu ana batun wata matsala da ta faru ne, da wahala kaji ankira sunan Arewa ana maganar samar da wata sabuwar jami’a ko wani muhimmin abu na cigaba, da yawan manya ‘yan Arewa basu cika tunawa da wannan yanki namu ba sai idan sun shiga cikin wani mawuyacin hali, sannan zakaji suna maganar Arewa, Ko kuma idan suna cikin wani hali na bukata sai kaji suna cewa to jama’a ga namu kada mu kishi domin naka naka ne; tabbas maganar haka take cewa “naka fa sai naka”, amma abin tambaya anan lokacin da namun ya samu dama me ya yi mana da ya nuna cewa shi dinfa namu ne? Akwai ‘yan Arewa da yawa da suka samu dama da zasu kawowa Arewa cigaba mai yawan gaske a lokacin da suka sami dama amma da yawa haka damar ta bare basu amfana mana komai ba, sai bakin ciki da takaici.

Yanzu idan zamuyi magana ta gaskiya, mukalli duk irin matsalolin da yankin Arewa ke ciki, me shugabanninmu sukayi na fitar damu daga cikin mawuyacin halin da muke ciki? Sanin kowa ne cewa yankinmu shi ne yankin da yafi kowane yanki komabaya ta kowanne fanni a kasarnan, gashi kuma Arewa shi ne yankin da ya fitar da galibiln ‘yan siyasar da sukayi tasiri a al’amuran siyasar kasarnan. Yanzu idan zamu dauka daga shekarar 1999 zuwa yanzu da mulki ya ke a hannun farar hula, wace irin matsala ce da ta ke damun Arewa shugabanninmu suka sanyata agaba akaga bayanta? Amsar itace babu, sai dai kawai dogon turanci da iya lankwasa harshe da karya hula agaban goshi da nuna ‘yan bokwanci da bajekolin manyan riguna da dirka-dirkan motoci a lokacin taruka. Yanzu mu dauki matsalar wutar lantarki da rashin aikin yi, kusan babu matsalar da tafi gallabar yankin Arewa kamar wannan matsala, ‘yan Arewa sune suka kawo Olushegun Obasanjo a 1999 suka tallata shi domin a zabe shi, amma me sukayi na ganin cewa Obasanjon ya kawo karshen matsalar wutar lantarki da magance zaman banza a Arewa? Kullum kuma kara fadawa cikin matsala mukeyi daga wannan zuwa waccan. Bayaga rashin aikin yi da ya addabi matasanmu da rashin ingancin ilimi da kiwon lafiya da matsalar tsaro da rikicin manoma da makiyaya, da kuma mafi muni a iya tsawon tarihin Arewa shi ne al’amarin Boko Haram, don ko sha’anin rikicin mai tatsine da ya faru a kano da maiduguri a shekarun 1978-80 bai kai kaso daya cikin goma na abin da ke faruwa a yanzu ba.

Idan muka duba matslar ilimi kusan mune mukafi kowa yawan jahilai (illiteracy) a kasarnan, jahilai ina nufin ta bangaren ilimin boko tunda yake da shi ne gwamnati ke la’akari wajen aiwatar da dukkan ayyuka na hukuma, domin baza a dauke ka aiki kowane iri ba sai kana da takardun makaranta; yaranmu sune wadan da basa iya cin jarabawa, malaman makarantunmu sune suke fama da rashin kwarewa da rashin ingataccen yanayin koyo da koyarwa; kusan shugabannin da suke ikirarin yanzu sune shugabannin Arewa idan ka bincika zaka samu sunyi karatune kyauta ba da kudin iyayansu ba kai hasalima galibi ‘ya ‘yan talakawa ne, amma da al’amura suka dawo hannunsu duk suka maida hannun agogo baya. Domin a lokacin da kasar nan batada kudi kamar yanzu aka dauki dawainiyarsu ta karatu da bukatunsu, a gefe guda kuma ana ta kokarin samar da kamfanoni da masana’antu domin samar da guraban aikin yi ga wadan da suka gama makaranta, irin manyan kamfanonin da muke da su irinsu Arewa Textile da manyan masakun Kano da Kaduna da UTC da PZ da Liventise da kamfanin mulmula karafa na ajakuata da kamfanonin siminti da muke da su da manyan kantunan kamfani irinsu John Holt duk wadan nan sun zama tarihi gine ginen kawai suka rage duk da suma suna fuskantar barazanar yanayi, sannan ragowar wadan da suka rage irinsu kamfanin buga jaridu na Arewa wato NNN da Gaskiya Tafi Kwabo suna cikin mummunan yanayi na Rai kwa-kwai mutu kwa-kwai duk wannan yana faruwa ne a lokacin da samun kudin da kasarnan ya ninka ninkin ba ninkim kaji ana maganar kudi malala gashin tinkiya, a lokacin da kasafin kudin kowace jiha a Arewa bai gaza Naira Miliyan dari ba (M100).

Yanzu ina amfanin kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ta ACF da kungiyar Gwamnonin Arewa da duk kungiyoyin da muke da su masu ikirarin Arewa? Sai kayi mamaki shin wai duk irin kungiyoyin da muke da su da sunan Arewa waccece ta gaskiya domin bayaga ga ACF akwai kananan kungiyoyi da daman gaske tundaga na dalibai da na ‘yan boko da na Matasa da na ‘yan kasuwa da tsofaffin sojoji da sababbi duk wacece ta ke yi da gaske akan wannan yanki? Abin da zai baka mamaki mu kalli takwarorinmu ‘yan kudancin kasarnan, idan muka dauki Yarabawa mutum daya ya iya hada kan dukkan yarabawan kasarnan suka zabi jam’iyya daya a zabubbukan da suka gabata sai kace shin wannan wane irin mutumne kuma jama’arsa wasu irin mutane ne? Bola Ahmed Tinubu ya tsaya kai da fata akan al’ummar yarabawa ya shiga lungu da sako domin ya tabbatar sun zabi jam’iyyar ACN kuma sukai hakan, kuma idan ka duba bashida mukami na komai a cikin jam’iyyar, kaga wannan shi ne kyakkyawan jagoranci; ina ‘yan Arewa da muke ikirarin mungaji siyasa daga mutane irinsu Mallam Aminu kano da Sa’adu Zungur da sauransu shin wannan ba zai zamar mana abin isharaba; haka kuma, idan ka dauki al’ummar gabas ta inyamirai suna karkashin jagorancin mutum daya, yanzu a ‘yan kwanakinnan da Ojukku ya mutu duk wani inyamiri dake kasarnan sai da ya rufe kantinsa domin nuna alhinin wannan mutum da suka kira jagoransu kai inyamirai har a kasar Amerika basu bude kantunansu ba lokacin da ake jana’izarsa duk domin nuna girmamawa gareshi. Yaznu idan ka dawo nan gida Arewa shin waye zai iya magana da murya daya a saurareshi? Shin akwai wanda zai iya cewa a zabi mutum guda kuma ayi hakan? Shin akwai wani da zai mutu mu nuna alhinai kamar yadda inyamurai suka nunawa Ojukku? Waye zai iya bada umarni kowa yabi, shi kenan mun zama mu bamu da kan-gado!

Sannan uwa uba kuma akazo akayi amfani da addini aka raba kan Arewa. Sanin kowa ne cewa a yankin Arewa babu wata magana ta kabilanci sai ta addini domin kiristan Arewa yana matukar kin Musulmin Arewa haka musulmi ma, duk ilimin da muke da shi ya tashi a maho tunda bamu iya amfani da shi ba wajen dai-daita tsakaninmu, akazo aka haifar da kiyayya da gaba babu gaira babu dalili kullum mune akejiyowa a shafukan jaridu da kafafen yada labarai muna kashe junanmu muna barnata dukiyar ‘yan uwanmu da suka jima suna tsuwurwurinta. Yanzu irin dimbin rayukan daka rasa da dukiyar da akayi hasara madudu ta sanadiyar rikicin jihar Pilatu da Kaduna Allah ne kadai yasan adadinsu, haryanzu an rasa wanda zaiyi magana a saurarashi dangane da wannan batu, sai dai kawai ayi taron nuna isa da shan shayi a tashi . Haka kuma, akazo ta karfi da yaji aka haifar da wata kungiya da suke ta bata sunan Arewa da musulunci inda suke ta dasawa tare da tayar da Boma-bamai babu kakkautawa ta ko ina a Arewa anrasa yadda za a iya shawo kan wannan al’amari.

Matsalar dan Arewa kamar yadda na lura ita ce, kowannenmu so yake ace shi ne shugaba, shi yake bayar da umarni ana karba, ina ganin wannan ce ta haifar da kungiyoyi masu yawa da basa iya amfanawa da wannan yanki da komai ba, kuma, ga zatona wannan bazai rasa nasaba da kasawar kungiyar dattawan Arewa ta ACF da kungiyar Gwamnonin Arewa ba. A shekarar da ta gabata ta 2011 manyan ‘yan Arewa da suka tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP wato Alh Atiku Abubakar da Gen. Ibrahim Badamasi Babangida da Alh Aliyu Gusau da Bukola Saraki wani kwamiti karkashin jagorancin Mallam Adamu Ciroma ya yi kokarin hada kansu domin fitar da mutum guda wanda zai tsayawa jam’iyyar takara daga yankin Arewa wanda sukaci nasarar fitar da Atiku Abubakar, ko shakka babu wannan babban abin a yaba ne domin abin da bamu taba zato bane ya faru, har ga Allah da yawanmu bamuyi zaton za’a zabi mutun guda sauran su hakura ba, wanda wannan shi ne babban abin da muka rasa tun da farko, da ace tun farko haka muke akwai jagoranci karkashin mutum guda da tuni bama cikin halin da muke ciki. Don haka da alama zamu dade cikin halin da muke ciki na fatara da komabaya da jahilci matukar bamu dinke mun ajjiye dukkan bambance bambance ba mun tafi karkashin jagoranci guda daya ba. Domin wadan nan kungiyoyi da muke dasu babu abinda za su yi face kara raba kan Arewa. Yanzu mu duba yadda kullum ‘yan yankin da ake kira tsakiyar Arewa ko middle belt suke ta kokarin nuna kamar su ba ‘yan Arewa ba ne; yanzu Arewa daga guda daya ta zama uku wato Arewa maso yamma, Arewa maso Gabas da kuma tsakiya ko idan son samu ne yaci gashin kansa, to haka zamu ci gaba da rarrabuwa matukar bamu hade munyiwa Arewa aiki bai daya ba.

Bazamu gushe ba muna tunawa da wadan da suka nuna kishinmu da gaske ba irinsu Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da su Mallam Aminu Kano da Sa’adu Zungur da kuma irinsu Sunday Awoniyi duk sun nuna kishin Arewa da gaske, babu bambancin kabila ko na addini. Allah ya kawo mana zaman lafiya a yankin Arewa, kuma Allah ya sa shugabanninmu su fadaku su maida hankali wajen cigaban wannan yanki namu. Allah ya taimaki kasarmu Najeriya gaba daya.

Yasir Ramadan Gwale

Yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment