Thursday, August 27, 2015

Malamai Masu Ci Da Addini


MALAMAI MASU CI DA ADDINI 

Wannan hoto ne na Matthew Hassan  daya daga cikin manyan Malamai masu fada aji a addinin kirista. Yayin da ya kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa Shekaranjiya. Yanzu mu dauka cewa Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ne ya kaiwa Goodluck Jonathan ziyara a lokacin da yake Shugaban kasa, me muke zaton mutane zasu ce? Na tabbata da babu irin zagi da cin mutunci da ba za ai masa ba a dalilin wannan ziyara, sabida muna da karancin tarbiyya da ladabi ga Malamanmu na addini.

Har yanzu banga wani kirista da ya fito yana zagin Kuka ba akan wannan ziyara da sunan cewar yana ci da addini ko yana yiwa kiristoci dodorido. Amma mu da yake mun ragewa kanmu matsayi da daraja, mu kan dauka Malamai ba su da wani ruwa da tsaki a harkar mu'amana da Gwamnati da masu Mulki. Lokacin da aka hasko hoton wasu Malamai na Musulmi sun karya kumallo da Azumi tare da Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan babu irin zagi da cin mutunci da ba ai musu ba a dalilin wannan ziyara.

Idan Shugaban kasa ya zama Musulmi kowa fatan sa a yi Gwamnati da mutanan kirki kamar yadda muke gani yanzu a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma a zamanin mulkinsa  (Goodluck Jonathan) fatan mutane da yawa da burinsu ba haka bane, kullum fata ake Jonathan yayi Gwamnati da mutanan Banza, barayi miyagu yadda za ai ta tsine musu, idan mutanan kirki masu amana suka shiga sai suma su zama abin zargi da tozartawa. 

Tilas mu sani cewar Gwamnatin Najeriya ta dukkan al'ummar Najeriya ce Musulmi da kirista. A kan wane dalili zamu tozarta mu aibata Malamanmu kawai dan sun gana da shugabanni, Musulmi ne ko wadan da ba Musulmi ba, alhali ga Malaman Kiristoci suna ta bibiyar Shugabanni Musulmi babu wanda muka ji yana zaginsu ko yana tozarta su daga cikin kiristoci. Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata.

Yasir Ramadan Gwale 
28-08-2015

No comments:

Post a Comment