Friday, August 7, 2015

Satar Kud'in Gwamnatin Kano A Bainar Jama'a!!!


SATAR KU'DIN GWAMNATIN KANO A BAINAR JAMA'A!!!

Jaridar Premium Times​ ta Juma'a 7 ga watan Auguta, ta ruwaito cewar, Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR​, ya amince da fitar da kudi wuri na gugar wuri har naira Miliyan dari da Tamanin (N180m) domin yin kwaskwarima a sabon ofishin mataimakin Gwamnan da gwamnatin kwankwaso da ta gaba ta gina shi akan kudi Naira Miliyan 303 watanni hudu da suka shude.

Wannan fa sabon office ne da aka gina aka kawata shi da dukkan kayan alatu watanni biyu kafin saukar Gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso​ wadda Ganduje shi ne mataimaki, kuma shi ne ya shiga wannan sabon office da aka gina, watansa biyu kacal a office din Gwamnatin ta shude. Dan Allah wannan wace irin satar dukiyar al'umma ce haka a bainar Jama'ah ko kunya babu?

Shin wannan ba abin kunya bane a wajen Gwamna ace ya amince da fitar da wadannan zunzurutun kudi dan yin kwaskwarima ga ofishin da ya bari watanni biyu da suka gabata. A daidai lokacin da ake cewa ana tsuke bakin aljihu sabida gwamnatoci ba su da  kudi, a daidai wannan lokacin ne gwamna zai yi wannan muguwar facaka da almubazzaranci da dukiyar al'umma!

Rahotanni suka ce hatta albashi Gwamnoni sun kasa biya, sai da gwamnatin tarayya ta taimaka musu da kudade sabida matsalar kudi da suka shiga, babu kudi a asusunsun gwamnatocin jihohi! A wannan yanayin ne Gwamnan Kano zai taka wannan mugun ta'adi da dukiyar al'Umar da suka zabe shi dan samun saukin lamura. Haba Gwamna, Wannan fa sata ce.

Duk da haka kuma, wai Gwamna ya bayar da umarnin korar ma'aikata 2000, wanda idan laifi akai na daukansu har da shi tunda gwamnatin da yake ciki ce ta dauke su aiki... Ya kamata Gwamna yaji tsoron Allah ya dawowa da al'umma dukiyarsu sannan a dawo da ma'aikatan da aka kona babu gaira babu dalili.

Lallai Gwamna ya sani, mu al'ummar Kano a yanzu matsalar samar da tsabtataccen ruwan sha da magunguna a asibiti da samarwa da manoma taki a farashimai rahusa, da inganta Ilimin Furamare da sakandare da karasa ayyukan Gwamnatocin da suka gabata suka bari sune abubuwan da suka dame mu, ba facaka da almubazzaranci  da kudin gwamnati da sunan aikin baban giwa ba.

Da yawan unguwanni an farke musu tituna,  da zummar yin aikin titi amma an barsu haka ruwan damuna yana musu ambaliya, wannan su ne irin misalin ayyukan da suka damu al'umma suke bukatar Gwamna ya fitar da kudi dan karasawa ba wannan satar da sunan aikin Gwamnati ba.

Yasir Ramadan Gwale​
07-08-2015

No comments:

Post a Comment