Friday, August 7, 2015

Sabon Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano


SABON OFISHIN MATAIMAKIN GWAMNAN KANO DA YAKE JIRAN LAMUSHE MILIYAN 180

Wannan ne fa sabon ofishin Mataimakin Gwamnan Kano da Gwamnatin Kwankwaso da Ganduje ta gina watanni hudu da suka wuce akan kudi Naira Miliyan dari uku da uku (N303m) wanda yanzu sabon Gwamna kuma tsohon mataimakin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace zai lakume zu zunzurutun kudi Naira Miliyan Dari da tamanin (N180m). Kai Jama'a!  Gwamna Gandujen Kwankwasiyya watansa biyu ka call a wannan sabon ofishi ya fice ya baiwa sabon mataimakinsa,  abin tambayar shin a iya zaman Gwamna na wata biyu a wannan ofishi har yayi masa illar da zai ci wannan zunzurutun kudi?


Kwanaki biyu ko uku da suka wuce an taka ruwan sama a Kano inda yayi sanadiyar rushewar gida je da yawa a Kwanar Jaba a karamar hukumar Nasarawa. Talakawa na cikin mawuyacin hali na matsi amma Gwamnatin da suka tsuguna suka haifa tana musu almubazzaranci da dukiya babu gaira babu dalili. A sabida karancin kudin Gwamnati fa aka ce Gwamna ya sanya an rufe makarantu kafin kaiwa karshen zangon karatu na uku sabida Gwamnati ba zata iya ciyar da daliban da ke karatu a makarantun kwana ba da na Firamare da ake ciyar wa sau daya. 

Gwamnatin da ta kasa biyan bukatar 'ya 'yan talakawa  da suke karatu a wani irin mawuyacin yanayi mai ban tausayi, amma ita ce ke almubazzaranci da kudin al'umma da sunan kwaskwarima ga ganin da wani garin ko taka shi ba ai ba. Ya kamata Gwamna ya sani, kud'in Gwamnati na al'ummar Kano ne, an zabe shi dan ya alkintawa al'umma dukiya ba dan yin almubazzaranci da dukiyar ba.

Yasir Ramadan Gwale
07-08-2015

No comments:

Post a Comment