Wednesday, August 5, 2015

Me Ya Sa Ake Kiran Gwamna El-Rufai Da Me rusau?


ME YASA AKE KIRAN GWAMNA EL-RUFAI DA ME RUSAU?

Na tambayi kaina wannan tambayar akan dalilin da yasa ake yiwa Gwamna Malam Nasir El-Rufai da sunan 'Me Rusau', a Madadin a kira shi da Mai Ginawa? Rushewa ai ba ginawa bane, domin ginawa shi ne aiki, rusawa kuwa aika-aika ne! Ba mamaki nine ban fahimta ba. Watakila a lokacin da el-Rufai yayi Ministan Abuja ya rushe gidajen jama'a da yawa shi yasa ya samu wannan suna.

Amma ni a fahimtata el-Rufai ma'aikaci ne, kuma yazo domin ya hidimtawa al'umma a matsayinsa na Gwamna ba kuntatawa ba. Ba mamaki mutanen da aka ce za'a rushewa gidaje a Zaria sunyi ba bisa doka bane. Daman kuma hakkin hukuma ne tsare doka, yana da kyau a wasu lokuta a nunawa al'umma cewar ba fa kara zube kawai ake rayuwa ba, akwai doka, kuma akwai hukuma.

Bana ko shakkar cewar mutanan da aka basu notis na su tashi za'a rushe gidajensu, sunyi kasassabar sayan filayen gwamnati da yin gini a inda bai kamata ba. Amma abin tambayar shi ne, me yasa Gwamna ya zabi wannan lokaci na damuna dan ya rsuhe wadannan gine gine da ake cewar anyi ba a inda ya dace ba?

Hakkin Gwamnati ne ta tsare tare da kula da al'umma ta dukkan janibin rayuwarsu. Gwamnati ita yafi kamata ta nunawa al'umma jin k'ai da tausayawa sama da kowa, a irin wannan yanayi na damuna da ake samun ruwa mai yawa, wad'an da suke da gidajen tabo hankalinsu a tashe yake idan ruwa ya tsawaita, a wannan lokacin za'a ce wasu su tashi za'a rushe gidajensu, saboda dawo da hakkin hukuma? Haba Gwamna!

Inama a ce gwamnati ta yiwa wad'annan mutane rangwame zuwa lokacin girbi bayan damuna ta jima da wucewa sannan a yi batun wannan Rusau! Nayi ta mamakin yadda masu baiwa Gwamna Shawara basu bashi shawara akan ya maida hankali wajen inganta harkokin lafiya da noma da samar da taki a wannan lokacin na damuna ba. Amma sai suka bada shawarar Rushe inda ba shuka za ai ba.

Wadannan mutanan sunyi kuskuren sayan filin hukuma sukai gidaje. Amma a zance na gaskiya, ya akai hukumomin baya suna gani ana yin gini ba inda ya dace ba, amma suka kasa tsawatarwa? Ina hukumar tsara birane masu sawa gini jan fenti? Ina ma'aikatan kasa da safiyo? Duk suna ina aka sayarwa da al'umma inda bai kamata ba. Ana maganar wasu sunfi shekaru 20 da mallakar fulotai a wajen!

Ya kamata Gwamnan Kaduna ya tausayawa wadannan mutane, ko da kuwa da basu diyyar da bata kai k'imar gidajensu ba, dan sauk'ak'a musu radadin halin da suke ciki. Babban burinmu shine muga Gwamna Nassir el-Rufai yana ginawa ba rushewa ba, akwai abubuwa muhimmai da suke da bukatar hanzarin hukuma na gaggawa da suka fi wannan Rusau a wannan lokaci.

Suma kuma al'umma ya kamata kowa ya shiga taitayinsa, musamman masu san banza na sayan filaye a gurare masu tararrabi. Dillalai da suke kasuwancin irin wadannan haramtattun filaye ya kamata suma a dinga kamasu ana yi musu Shari'ah, domin da yawa su ke zuga mutane su sayi waje me hadari irin wannan. Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale
05-08-2015

No comments:

Post a Comment