Thursday, September 3, 2015

RE: Malamai Masu Ci Da Addini


RE: Malamai Masu Ci Da Addini 

Abbas Yushau Ya Rubuta game da rubutun da nayi dazu kan ziyarar Kuka ga Buhari:

Yasir Ramadan Gwale wannan Magana taka haka take, Marigayi Sheikh Abubakar Gumi Allah ya jikansa sanda yana da rai yayi muamala da Shugabannin Najeriya  musulminsu da Kiristocinsu, takai idan yayi tafiya akan hanyarsa ta zuwa gida ya kan tsaya a legas su tattauna da Shugaba Manjo Janar Muhammadu Buhari, Shugaba Ibrahim Babangida da Sauransu, Kai akwai lokacin da Shugaban Kasa na soja kuma dan Kabilar Igbo, Manjo Janar Johnson Thomas Umunakwe Aguiyi Ironsi ya kirawo Marigayi Sheikh Abubakar Gumi Fadar Dodan Barack yacewa Malam yaje kasashen larabawa yayi musu bayani cewa juyin mulkin da aka yi na watan Janairun 1966 an yi shi ne da kyakkyawar manufa, nan take Shekh Gumi yacewa Janar Ironsi ba zai je ba saboda duk wadannan kasashe sun zaga da sardauna, saboda haka domin mutuntakarsa ba zai koma yace an kashe su Sardauna da kyakkyawar manufa ba, haka yace shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo ma yana girmama shi inda yace ba musulmi bane amma kuma ba kiristan azziki bane da dai sauransu, Kuma wannan mu'amala da sheikh Gumi yayi bai hana shi gaya musu Gaskiya ba, kuma bai tara abin Duniya ba.

28-08-2015

No comments:

Post a Comment