Sunday, September 13, 2015

SA'UDIYYA: Kasa Mai Tsarki


SA'UDIYYA: KASA MAI TSARKI 

Da farko ina amfani da wannan damar wajen Jajantawa Khadimul Haramain Ash-Sherifain Sarki Salman Bin Abdulaziz da dukkan al'ummar Musulmi bisa wannan ibtila'i da ya faru a Masallacin Allah mai alfarma da ke Makkah a Juma'ar da ta gabata. Ba shakka komai da ke faruwa muqaddari ne daga Allah,  kamar yadda wannan rubzowar da gini ko karfen gini yayi, sanadiyar iska mai karfin gaske tare da ruwan sama mai yawan gaske. Allah Ta'ala Ya jika  wadan da sukai shahada, sun rasu a waje mafi tsarki da daraja a ban-kasa, sannan Allah ya karbi rayuwarsu a daya daga cikin ranaku masu martaba ranar Juma'a a daidai lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi yace sa'ar karshe ta Juma'a lokaci ne mai falala da ake amsa addu'ah, a kuma cikin yanayi na ruwan sama, suna wadan da gini ya fadowa, wanda alama ce ta mutuwar shahada, Allah ya jikan su ya gafarta musu. Allah ya kare aukuwar hakan anan gaba.

Kamar yadda kowa ya sani dakin Allah Mai Alfarma waje ne da ake ibada awanni Ashirin da hudu a kowacce rana, dan haka al'umma daga ko ina a duniya, sukan dunguma su shagala cikin Ibada a wannan waje mai tsarki. Haka kuma, sanin kowa ne cewar fiye da shekaru Goma da suka gabata wannan waje (Harami)  bai taba zama ba'a yin wani aiki da ya shafi gyaran wannan Masallaci a ciki ba, ko dai fadada shi abinda ya shafi kara girman Haraba dan samun sukunin masu Ibada cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da sauran dangin nau'o in siyana. Irin wannan hidimtawa wannan waje da Sarakunan Sa'udiyya sukai abin a yaba musu ne kuma a jinjina musu, kullum kashe kudi ake a wajen nan kamar babu gobe, wadannan mutane basu taba yin bara ko rokon a taimaka musu zasu gyatta wannan waje da ya shafi dukkan Musulmin duniya ba. Wannan kadai abin a cira musu tuta ne, Allah ya saka musu da alheri, ya yalwata arzikinsu, ya basu ikon hidimtawa Musulunci. Wannan duk wani bayani ne da sai wadan da suka saba zuwa zasu fahimci yadda ake kashe wa wannan waje zunzurutun dukiya.

Tare da haka kasar Sa'udiyya bata gaza ba wajen taimakawa al'umma musamman wadan da bala'i ya shafa nan da can. Sunyi kokari matuka wajen sanya farin ciki a zukatan al'ummatai da yawa. Zai zama katon zalinci da rashin tsoron Allah da mugun nufi, wasu 'yan gaza gani, su ce wannan abinda ya faru wai laifin Sa'udiyya ne, wasu kuma suyi kwaskwarima su ce ai kamfanin dake aikin ya kamata a tuhumeshi, wasu kuma suce, me yasa ma ake aikin alhali Alhazai sun fara hallara a Makkah domin ibadar aikin hajj na wannan Shekarar,  wasu ma cewa suke ai dole Sa'udiyya su biya diyyar rayukan da suka salwanta.  Da sauran soki burutsu da yawa da galibi masu barbarar tunani daga Iran suke yi.

Masu wadancan korafi da kalubale, sun mance cewar wannan abu ya auku ne, a lokacin da ruwan sama mai karfin gaske ya sauko tare da iska mai karfi ya haddasa. Wannan abu duk da ana aiki, ba shakka kamfanin dake aikin yayi kokari wajen gudanar da aiki tsawon lokaci ba'a taba samun ta'adi mai yawa irin wannan ba, wanda kai tsaye ba zaka ce laifin ma'aikata bane, domin ba a tsaye kawai kayan aikin suka rubzo ba, ba kuma tsaka da gini ake wasu manyan tubala suka rikito ba. Duk da haka, da kansa Gwamnan Makkah bayan ya zagaya yaga irin adadin da wannan barna tayi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike nan take, domin samun ingantattun bayanai dan sanin ko akwai sakaci ko kuwa daga Allah ne. Ba shakka, Gwamnan Makkah ya katse hanzarin 'yan yaga riga masu zakwadi da ganin baikensu,  wanda dama kullum neman gazawarsu ake dan a samu abin fade. Muna kuma da yakini ba zasu kasa biyan diyyar rayukan da aka rasa ba.

Haka kuma, wasu dan tsananin kifewa, sai karaji suke wai ai Sa'udiyya daman ba kasa ce me tsarki ba, Makkah da Madina ne kawai birane masu tsarki a cikinta! To idan kace Sa'udiyya ba kasa bace me tsarki tsammaninka ka rage darajarta a idan wadan da kasar take da kima a wajensu? Shekaru nawa muka taso muka ji ana cewa Sarki Mai Martabar, Sultan Mai Alfarma, Gwamna Mai Girma da sauransu? Shin akwai wani abin damuwa da jin zafi dan an kira Sarki da Mai Martaba shin me yasa baka taba kalubalantar dan me yasa ake kiran Sarkin Musulmi da Mai Alfarma ba,  sannan a kira Sarki da Mai Martaba yayin da ake kiran Gwamna da Maigirma? Shin akwai wani abu da zai ragu daga darajar Sarki dan ba'a kirashi Mai Martaba ba? To wannan fa shi ne tunanin wasu, wai dan me yasa za'a kira Sa'udiyya da kasa mai tsarki. Albashirin masu wannan tunani ko ransu ya so ko Kada ya so, har duniya ta tashi Najeriya da sauran Garbi Ifriqiyya zamu ci gaba da Kiran Sa'udiyya da sunan kasa mai Tsarki idan ya so sai a koma da baya ace karya ne ba kasa bace me tsarki.

Daga karshe, ina tukewa da cewar ko anki ko anso kwalba ita ce uwar turare. Allah ya taimaki Khadimul Haramain Ash-Sherifain Sarki Salman Bin Abdulaziz bisa wannan hidima da suke yiwa Masallatan Allah masu Alfarma na Makkah da Madina. Allah ka daukaka Musulunci da Musulmi, Allah ka kaskantar da Kafurci da Shianci da masu daurewa Shiah gindi da masu mara musu baya da 'yan kanzaginsu, Allah ka kunyata magauta da daukakar Sunnah da Masu taimakawa yaduwar Sunnah.

Yasir Ramadan Gwale 
12-09-2015

No comments:

Post a Comment