Sunday, June 21, 2015

Tsokaci Kan Azumi #Ramadan 2015


TSOKACI KAN AZUMI #RAMADAN 2015

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, Yace duk wanda ya ciyar da mai Azumi yana da kwatankwacin ladansa. Da yawan al'umma da sun fahimci wannan magana ta Manzon Allah SallLlahu Alaihi Wasallam, da kowa ya kasance mai kokarin ciyarwa, ba wanda ake ciyarwa ba. Haka kuma, Manzon Allah tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi yana cewa, ku fanshi kanku daga wuta ko da kuwa da tsagin dabino ne.

Babu shakka wadannan maganganu guda biyu suna nuna mana tsananin kwadaitarwa da ciyarwa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yayi mana umarni da su. Sai dai kadan ne daga cikin al'ummarmu suka fahimci wadannan maganganu biyu masu matukar muhimman. Allah ka bamu ikn ciyarwa da dan abinda muka mallaka.

Yasir Ramadan Gwale
21-06-2015

No comments:

Post a Comment