Wednesday, June 3, 2015

Boko Haram Da Goodluck Jonathan


BOKO HARAM DA GOODLUCK JONATHAN
Da sannu gaskiya zata bayyana. Ada idan muka ce Jonathan ba shi ne Boko Haram ba wasu gani suke wannan magana tamkar Ridda ce, ai bayadda za'a ce Jonathan ba shi ne ke kashe mu ba, a tunaninsu ai tsabagen kiyayya ce ta sanya Jonathan ke kashe mutanan Arewa.
Mutane da yawa sun shiga rudu akan hakikanin al'amarin Boko haram, aka kasa yiwa Jonathan adalci akan Boko haram. Mutane, ciki har da masu ilimi da suke tara jama'a su yi musu huduba, zaka ji suna rantsuwa da Allah cewar Jonathan ne ke kashe mutane da sunan Boko Haram, kawai sabida sunga wannan ce haƱya mafi sauki ta neman suna da tara jama'a.
Mutane da dama sun dinga yad'a wata magana wadda ta samo asali daga Gumsu Sani Abacha, tana cewar, tsohon Shugaban kasa Marigayi Abacha yana cewar "duk wani rikici da gwamnati ta kasa shawo kansa cikin awa ashirin da hudu to akwai hannunta a ciki" wannan magana ta yadu kamar wutar daji, kuma ta zauna a zukatan mutane da yawa.
Daga acikin abin da zai fi bada mamaki shi ne yadda har mutanan da suke a yankin da wannan fitina ke faruwa zaka ji suna zargin Jonathan da cewa da hannunsa wadannan abubuwa ke wakana. Wasu har anan facebook suka dinga karairayi da kaucewa gaskiya, da d'ora laifi ga Jonathan amma kuma yanzu sun fara lashe aman da suka yi akan zargin da sukaiwa Jonathan na zalinci.
Kamar yadda muka sha fadi a baya, wannan batu samo bakin warware shi yana da alaka da sai mutane sun gamsu akwai Boko haram kuma kuma 'ya 'yan Musulmi ne da suke ikirarin addini sannan su gamsu cewa ba Jonathan bane, sannan hakikanin gaskiya zata bayyans a shawo kan abun. tare da abokan gwagwarmaya irinsu Yamai Muhammad Buhari da Sule Abbati mun sha nanata wannan kira sau da yawa a baya, abinda mutane suka ki yadda su fahimta da gangan.
Dukkanmu munyi tarayya wajen cewar matakan da ake dauka a tunani irin namu ba su ya dace a dauka dan magance rikicin ba, sannan shugaban kasa na lokacin Mista Jonathan duk munyi tarayya akan cewar yana da sakaci wajen daukar matakan da suka dace. Amma wasu da dama suna ganin babu yadda za'a ce Jonathan bai da hannu a wannan rikici, Musulmi shi ne mafi kololuwar mutumin da ya kamata yayi adalci a ban kasa ko da kuwa akan waye, sai dai da dama sun gagara yin haka akan Jonathan.
A yanzu a wannan karon, da aka samu sauyin Gwamnati Boko Haram suka kaddamar da kai sabbin hare hare, Gwamnan Borno Kashimu shatima yake kiran ai musu ahuwa duk kuwa da irin mummunan ta'adi da barnar da suka tafka. Ammam dai duk da haka, lokaci na kara tafiya gaskiyar wannan lamari zata cigaba da bayyana.
Ba mamaki, daga masu wancan ikirari na baya suce ai Boko Horam ta kare yanzu kuma ISIS ne suke kaddamar da sabbin hare hare dan tabbatar da zargin da sukaiwa Jonathan a baya. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya, Allah ka bayyanawa al'umma gaskiya akan wannan ta'addanci, Ya Allah duk mai hannu a ciki ka tona masa asiri kowa ya ganshi.
03-06-2015

No comments:

Post a Comment